12

4.8K 301 28
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*

ZAN CIGABA DA YIN POSTING RABO AJALI IN SHA ALLAH, AMMA MATUK'AR AKA CIGABA DA SIYAR MIN DA NOVELS CIKI ABU HUD'U TABBAS ZANYI D'AYA, KO NA MAYAR DA NOVELS D'INA NA KUD'I, KO NA YI APPLICATION NA MAYAR DA NOVELS D'INA CIKI, DUK MAISO YAJE PLAY STORE YAYI DOWNLOADING KO NA MAYAR KAN YOUTUBE DUK MAISO YAJE CAN YA SAURARA, KO NA DAINA RUBUTUN KWATA-KWATA GABA D'AYA DAN BAI YIWA KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, NI INA NAN INA SHAN WAHALA WANI NA CAN NA AMFANI DA WAHALA TA, BASIRA TA BA

'''DEDICATED TO'''
*MAMU GEE*

1⃣2⃣

Jin hannunshi saman mutum yasa shi tsammanin Najwah ce ya k'ara matse ta tsam a jikinshi,
ya shigar da ita cikin k'irjinshi yana shafa ta, had'i da k'ok'arin had'e bakinsu yana fitar da numfashi gami da nishi,
cikin bacci Neelah taji bak'on yanayi yana bak'ontar duk ilahirin jikinta,
sama-sama taji kamar ana tura mata abu cikin bakinta, a d'an shagwab'e ta turo harshenta,
had'i da k'ok'arin zamewa gam ya rik'eta fuskarshi d'auke da murmushi,
muryarshi can k'asan mak'oshi yace " ina zaki.....!?

Bai bari ta bashi amsa ba ya tura harshenshi cikin bakinta,
tare da soma sucking lips d'inta, jin abinda bata b'ata ji ba a iya tsayin rayuwar ta,
yasa ta saurin bud'e ido duk da nauyin bacci irin na Neelah,
a tsorace ta soma k'ok'arin kwace jikinta da bakinta daga gare shi amma ta kasa,
hakan yasata sakin gigitacciyar k'ara,
wacce tayi sanadiyyar dawowar Neehal cikin hayyacinshi,
wata irin muguwar hantsilawa had'i da katantanwa Neehal yayi a tsakiyar d'akin,
cikin matsanancin tashin hankali da firgici Neehal ya mik'e tsaye,
duk ilahirin jikinshi ya d'auki kerrrrma gami da tsuma, cikin d'imuwa ya nunata da yatsanshi,
yana jifanta da wani irin matsiyancin kallo batare daya iya furta koda kalma d'aya ba,
ya d'auki tsayin lokaci a haka yana k'ok'arin tuna ainahin abinda ya faru,
"no..! no...!! no...!!! yace yana dafe k'eyarshi lokacin daya tuno da abinda ya farun,
" impossible! ya fad'a dai-dai lokacin da idanshi suka sauka akan Neelah,
dake rab'e gefe tana furzar da yawo had'i da goge bakinta,
hakan daya gani ne ya k'ara tabbatarwa Neehal tabbacin kissing d'inta yayi,
tashin hankali wanda ba'a saka maka rana, cikin zallar tashin hankali Neehal yayi waje,
ya durk'ushe a k'asa cikin k'asa yana kakarin amai،  tare da zura yatsanshi cikin mak'ogwaronshi,
cikin k'ank'anin lokaci Neehal ya fita daga hayyacinshi,
gaba d'aya ya rud'e, idonshi yayi mugun yin ja kamar gauta,
gumi ya jik'a mishi jiki sharkaf, amma yak'i daina kakarin aman,
gashi aman yak'i zuwa, babbar burin Neehal bai wuce yayi aman ba,
amma kwata-kwata babu ko alamar aman, yakai 1hr nan tsugunne yana k'ok'arin yin amai amma a banza,
Neelah na tsaye tana kallan duk abinda yake cike da mamaki,
dole ya yasa shi, tashi ya shiga ban d'aki, ya soma wanke bakinshi,
yakai 30 minutes yana wanke baki, sai da ya k'arar da toothpaste guda d'aya,
kana soma wanka cike da kyama, yake wanke jikinshi saboda k'ankyamin jikinshi daya tab'a nata,
sai da ya  d'auki tsayin lokaci yana wanke jikinshi kana ya fito ya shiga d'akin.

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now