34

6.1K 385 57
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

3️⃣4️⃣

Ya dad'e kwance yana fitar da numfashi dakyar kafin ya mik'e yana jan k'afa, while yana dafe da k'irjinshi,
Allah ya taimake shi bayyi tafiya mai nisa ba ya samu napep, dakyar ya fad'awa me napep d'in inda zai kaishi,
sanin bashi da kud'i yasa shi cewa napep d'in ya jira shi a bakin get,
yana dafe da k'irjinshi ya shiga get d'in gidan yana kwalawa Neelah kira,
a kid'ime Neelah, Naufal da Umairah suka fito,  jikinshi na rawa ya zube gaban Neelah,
had'i da fasa mata kuka,  ya kasa furta koda kalma d'aya,  a hankali tari da hakkin da yake yi suka soma tsananta,
kallo d'aya zakayi mishi kasan yana cikin mawuyacin hali,  ya jigata sosai, ko numfashi dakyar yake iyayi,
yana dafe da k'irjinshi ya bud'e baki dakyar cikin muryarshi da bata fita sosai yace " nasan nayi miki kuskure but I'm sorry, kiyi hak'uri,
ki yafe min, ki tuna muma masu laifi ne a wajen Ubangijinmu,  muna yi mishi laifi yayafe mana,
Allah mai yafiya ne, yana kuma san mutane masu yafiya, Ubangiji me tausayin bayinsa ne, haka yana san mutane masu tausayi,
ki dubi girman Allah Neelah kiyi hak'uri ki yafe min wallahi Allah na tuba na canja hali, 
na kuma gane kuskure na,  please, ya k'arasa maganar jini fitowa daga hanci da bakinshi,
idanta kanshi tana k'ok'arin danne abubuwa da dama cikin ranta,  tace " baka canja ba, inda ka canja bazaka rink'a tunanin kanka,
da nemawa kanka mafita kai kad'ai ba, ko sau d'aya ka tab'a tunanin ni ina sanka ko bana sanka?

"Ka tab'a tunanin halin da Nauman zai shiga?

"Ina da tabbacin matuk'ar aka raba mu daga ni har shi sai mun shiga fiye da halin daka shiga,
amma saboda tsabar san kanka dayayi maka yawa ta kanka kawai kake yi,
kanshi ya shiga girgizawa yana cewa " nasan kina so na Neelah, ko shakka bana yi akan irin son da kike yi man,
hakan ne yasa ban..... dakatar dashi tayi ta hanyar d'aga mishi hannu tana kallan kwayar idanshi ta nuna kanta,
had'i da cewa " wa! ni nake sanka?

Da sauri ya d'aga kanshi tare da cewa " eh!  I knew you really love me,
murmushin gefen baki tayi tace " ashe abinda kake tsammani kenan?

Bata bari yayi magana ba ta cigaba da cewa " to idan ma abinda kake tunani cikin ranka kenan,
gwara tun wuri ka janye danni babu wannan shirmin cikin raina, ko an fad'a maka bani da hankali ne da ina ganin kashi da rana zan taka?

"Bayan na san waye kai, nasan halaye da d'abi'unka, sannan zan so ka,
" wallahi nasan kina so na Neelah,  dan tun kafin kisan komai a duniya kika san so na,
tun kafin kisan wacece ke kika kamu da soyayya ta,  tun kafin kisan meye duniya, rayuwa da mutuwa, hankali da nutsuwa kika san son Neehal,
baki san komai ba sai so na, baki san kowanne d'a namiji ba sai ni,  da dakon soyayyata kike kwana kike tashi, duk wannan tsayin lokacin,
fashewa tayi da matsanancin kuka had'i da durk'ushewa k'asa,  ta shiga girgiza kanta tana cewa " a'a k'arya kake ban sanka, bazan kuma tab'a sanka ba,
a hankali ya durk'usa a gabanta ya sanya hannunshi ya tallafo fuskarta,
hawaye na gangarowa daga idonshi yace " idan bakya sona meyesa a wancan lokacin kike kishi na?

"Idan baki so na meye a baya kike kallan fuskata idan ina bacci?

"Meyesa baki ganin laifi na?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now