CHAPTER 7

3.1K 233 2
                                    

Wani wawan mari amina ta sakewa hannatu har sanda taga tauraro
Sameera ce ta hayaiyako zata daki amina,wani lafiyaiyan mari
Amina ta aika mata atake ta dauke wuta ta suma zaliha ce tace ni amina zo mutafi kamin kisa da naushi Kiyi kisa taja hannunta suka tafi ayayinda akabar bilkisu sakoko a tsaye batada tudun dafawa gashi yau zasu wanki wani alhaji yace su ukun za'a hada lokaci daya (Allah shi kyauta)

Atake taji wani bakin ciki ya rufeta taji ta kara tsanan amina.....

Amina kuwa dasuka je islamiyya sunyi latti gashi malam isa ke taran latti ya iya bulala Kamar Allah ne ya aiko shi

Shikadai ne yake iya dealing da amina kuma tana tsoransa sosai amma tsabar bakin ciki da haushin daya rufe mata ido bata lura dashi Ba
Sai saukar bulala da taji batasan sanda ta karbi bulalan ta karya Ba hade da banka masa harara ayayinda ta murkuda cute pinky lips dinta tace Allah ya isa ta wuce

Malam isa sai da yasha jinin jikinsa domin yasan yadda take tsoranshi(saboda ya iya bulala itakuma duk abinda zai taba lafiyar jikinta bataso)
amma yau harda karya bulala wadda take tsoro Kamar maciji gashi fiskanta yayi jaaa(red)alamun Bacin rai kuma dama shima dai yana shakkunta karfin hali ne kawai irin nasa amma ya girgiza yau Dan haka satinnan dole ya Dan tsagaitawa amina idan Ba hakaba shima zai karbi rabonsa ko ta kullo masa jagwal.
Haka suka Shiga aji Amina tasha mur,zaliha nata aikin ban hakuri hakadai har aka tashi suka dawo gida tana kumbure kumbure.

Bayan sallan magriba inna ta gama abinci ta kwalawa Amina kira bata amsa Ba ta kara kwala mata kira still shiru abinda bata tabayi Ba kenan akirata taki amsawa shiga dakin inna tayi thinking that something is wrong with her daughter to her surprise Amina was sitting down on her mattress

Ke yar nan dama kina jina kikai shiru to abincin ki zaki dauka she didn't reply inna rather all she did was sip water from her tiny blue cup

Inna tace yar nan Ba lafiya Dan a yadda nasanki ko bata maki rai akayi baki wasa da tuwo amma yau ko motsi bakiyi
Ta fadi hakanne ayayinda take taba goshin Amina Dan inna ji take Amina batada Lpy domin ita bata wasa da tuwo

Jin ko magana batayiba yasa inna ta fita ta samu baba ta labarta masa abinda ta gani baba ne yace rabu da ita zamu hadu atakaice de ranan Amina bataci abinci ba.

Washe gari koda Amina ta tashi tayi shara da wanke wanke ta gama koko,
Sai wajen karfe goma ta tuna da Cewa zata raka zahra anguwa tashi tayi tasa hijabi taje dakin inna tace inna ni zan tafi gidansu zahra tace zan rakata anguwa

wani kallo inna ta watsa mata kamin tace shine gaisuwan ki ?

Amina tace mantawa Nayi ina kwana
Inna tace rike abinki
Sannan a haka zaki rakata anguwan kai Innalillahi aminatu yaushe zaki canza yau kwana uku kenan bakiyi wanka kuma a haka kike tunanin zaki samu miji ki Duba kullum in zahra zatazo gidannan kwas da ita amma ke a birkice

Since bakin zaninta tayi ta miko mata Dari biyu ki siyo sabulu da tirare dan d'uri da sabulun gashi kinji

Bubbuga kafa Amina ta fara haba inna zan bata mata lokaci fa
inna tace to wallahi inbakiyi abinda na fada Ba babu Inda zaki mutum sai shegen kazanta Allah ma daya taimaka bakida karnin kashi ai da mun mutu

Turo baki tayi tana guna guni har ta siyo ta dawo
Inna tace maza Shiga wanka ki wanke kanki sai kizo in miki kitso saura kiyimin gardama ma babu inda zaki
Subul subul tayi Kamar yadda inna ta umarceta ta shiga ban dakin shiru shiru babu ita babu labarinta inna tace wai me kike yine har yanzu kinsan dai jiranki nakeyi ko?

Fitowa tayi gefen kanta duk kunfa inna tace ke haka ake wankar duk dadewannan nanki baki daurayu Ba? Bata ko kula innar Ba ta shigewarta daki ta goge kan sosai ya zama saura damshi sannan ta zauna aka mata kitson ta dauko kayanta mai Dan haske ta saka sannan ta Dan shafa man baki sai tayi dass da ita.

Tana fitowa inna tace ko kefa amma ace mutum bayason wanka minal tace inna kwana biyu ne fa inna tace kaji banziya ko kunya bakiji har kina daga murya gararin makota suji

Tace to Nide na tafi tana fitowa Zaure ta hadu da baba tace baba ina kwana yace Lpy a'a aminatu ce haka ko bake bafa amma ace mutum kullum...............

Tace to baba ya isa mana tunda Nayi wankan ba he ka since min zani a kasuwa ba. Yace yauwa yar gari kinga in kina Dan kwalliyan nanne zaki samu miji ko Ba haka ba? murmushi tayi ya miko mata naira Dari biyu yace na sanki da awara ok gurasa watakilla shi zakije siyowa ko innan ki ce ta aike ki?
tace a'a gidan su zaliha zani zan rakata anguwa Dan auntyn ta ya karye kuma zamu tayata gyaran gida dashi ke basu Dade da kaura wannan gidan Ba
Baba yace Toh sai kin dawo amma karkiyi dare tace Toh kamin ta fita tanayi masa godiyan kudin daya bata

Tana fita tace Kamar baba yasan banda kudi wlh

Abangaren YAZEED kuwa yau ana shiri da mitimiyar domin bataje office Ba,
Ya Shirya musu evening outing zaliha anci ado makeup kamar ya zubo daga fiskanta attachment dinnan ba'a magana sai harhada rai take wai ita adole batason raini(nace uhm shi baice zaki rainashiba sai ke?)

Taku daidai take har ta iso gaban wani Mercedes Benz

sai yauki take alokacin YAZEED ya Dade yana jiranta domin yace shi da kanshi zai tuka su kuma bayason escort na soldiers ko daya

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

sai yauki take alokacin YAZEED ya Dade yana jiranta domin yace shi da kanshi zai tuka su kuma bayason escort na soldiers ko daya.

How is the novel?is it good?any suggestions?

Ramadan Mubarak and happy sallah in advance

2nd June 2019

Show some love

Mzz untichlobanty💕

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now