CHAPTER 8

3K 237 12
                                    

Tana shigowa ya kunna mota domin yaji haushin bata masa time da tayi domin he values time so much. Tafiya suke a hankali babu Wanda ya kula kowa

......

Abangaren minal kuwa ta isa gidan su zally ta sameta tana kwalliya an rike mirror da bakin eye pencil sai zana girannan ake baki wuluk abin abin dariya

'Daka mata duka tayi a cinya
Kinga abinda kika jawomin ko? kullum in zakije anguwa saboda iyayi sai kinyi kwalliya kinsa inna ta Mani kitson dole ta sani kwalliya.

Sai alokacin zally ta kalle ta tace kawai kice kinyi kwalliya kinaso ki nuna mini  shine zaki fake da guzuma ki harbi karsana!
To wallahi bashi dukannan.

Minal tace wannan ke ta shafa sannan ta zauna tace kinsan yau Dana hadu da baba a Zaure na dauka duka na zaiyi saboda tabarar danayi musu a gidan

Ga mamaki na bemin maganar Ba kuma harda bani kudi
zally tace iye lallai kwalliya ta biya kudin sabulu,wato haduwar taki har akan baba tayi tasiri, yo ina batun su babba?hararanta minal tayi taci gaba da cewa amma matsalata dake ko kwalliyan baki iya Ba kinsan mu yan boko kuma wayayyu anaso adinga yin make up mai kyau amma kin wani shafa powder da man baki

Minal tace iye sannu wayaiya yar boko.
Zaliha tace ke nifa zan cigaba da karatu domin suleiman yanason inyi karatu har kudin WAEC ya biya min a wata makarantar private kuma yace zai Nayi mini lesson in munyi aure.

Minal tace lallai ma yarinyar nan wato haka zamuyi dake? tafiya makarantar gaba zakiyi ki barni? Zaliha tace a ah zama zanyi in jiraki harsai kin zama farfesiya. kallon zaliha minal takeyi yayinda zalihar taci gaba da kwalliyarta.

Can zaliha tace ni yanzu banida burin daya wuce in Tara kudin Indan siya man kara haske Dan ba'ki na yayi yawa wallahi. Minal tace man me?! Sauri zaliha tayi ta rufe mata baki tace toh sannu sarkin karadi so kike iya taji ko?

Tureta minal tayi tace to in tajin ma ai haka akeso ni ban taba Sanin bakida hankali bama sai yau,ke bakisan Cewa butulci wa Allah bane ace yayi ki baka kice Wai bakinki yayi yawa ? Kin FISA sanin daidai ne? Kuma ai koba Komai mayukan blitin dinnan yana 'bata fata bara kiji kuma iya da lahani sosai saima kinji ciwo in yaki warkewa zakiyi bayani.

Karkiga ke baka ce wallahi wani zai iya mutuwa akan bakar mace kuma wallahi sai kiga fara ko a kafa aka daura masa sai ya kunceta.
Kima godewa Allah kinada kyau farare nawa ne munana?mtswww!

Ajiyan zuciya zaliha ta sauke kamin tace kuma fa maganar ki Gaskiya ne waje daya kika kwafsa Ba man blitin akace Ba bleaching ake Cewa. minal tace Koma menene Nide tashi mu tafi.

Zaliha tace Gaskiya kizo na Dan miki kwalliya minal tace Wanda Nayi ma ya isa. Zaliha tace shiyasa bazaki taba samun saurayi Ba ki Duba ki gani kafin a tsaida lokacin aurena samari na dayawa amma ke wa ya taba miki kallon birgewa ma?

Shiru minal tayi kamin tace kuma fa hakane wato shine sirrin baki taba fadamin Bako,Allah ya isa Zaliha tace ai shiyasa kullum inna ke miki fada akan wanka baki gane Ba. Ba sai kin nuna tsiraici ba amma de aga fuskarki da kyan gani.

Minal tace to me mike jira zana mini ado Yan mata zama tayi zaliha ta shafa mata Jan powder aka zana giran nan akayi mata Layin baki da green Yadda Kasan yar tashe

Fitowa sukayi zasu tafi sukayiwa iya sallama tanata kodasu Wai yan matanta zasu haska titi

Koda suka fita zaliha ta ballawa Amina harara tace yar uwa matsalata dake baza'a taba iya gyaraki Ba kaf duniya Ba Wanda zai iya in aka gyara nan sai asamo wani matsalan wannan wani irin tafiyane?Minal tace me matsalar tafiyannawa ?

Zally tace kinga yanda ake tafiya yanga ta soma Kamar talo talo (lol karfa kuce ina kushe characters dina zasu Waye, just for entertainment ne 😂😂)

Minal ma ta fara kwaikwayanta abin har gwara na Zally domin minal ita nata Kamar agwagwa😂.

Ana cikin haka aka fara ruwa Kamar da bakin kwarya. Yan matan ka suka nemi wurin buya domin kada ruwa ya musu duka, amma sanda aka sami matsala domin ya ca'be musu ado

Abangaren yazeed kuwa parking yayi domin ruwan ya tsagaita ganin zakky baby ta 'bata masa lokaci gashi ko kulashi batayi Ba balle yasa ran zata bashi hakuri abin sai ya bata masa rai

Yace
Zakky what's all of this ?

Tace
Meaning?

Yace
first you wasted my time,also came out walking like a snail and you can't even apologize?

Tace
What wrong have I done that I will apologise? Is it wrong to walk majestically?
Look that's fashion

She said that Prolonging the fashion

Yace
Fashion my foot,the hell with it

Alokacin ruwan ya tsaya kunna motan yayi
Ayayinda zakky ke Cewa

Look idan ka fito dani just to disgrace me ne am not in the mood please hurry up ma ni am starving gushhh

Wani wawan acceleration ya kwasa ya kure speed din motan shi dama ba mutane akan titin

Alokacin dadai su zaliha sun fito daga Inda suka labe domin su tsallaka titi takalmin minal ya Tsinke tsallakawa zaliha tayi koda ta juya ta hango minal bata tsallako Ba tace Ki tsallako kamin abawa motocin Hannu .

Minal tace ke aradu sai na gyara takalmi na.
Zaliha tace wallahi ko ki tsallako ko in tafi in tafiyata minal tace da nace ki jiranine?
Tsugunawa tayi ta cire takalmin ta fara kokarin gyarawa yayinda zaliha tayi tafiyatta tana mai jin haushin minal din.

Neman kara minal ta farayi bata zamu Ba aiko tana Daga kanta taga wani a tsakiyar titi Dan haka Ba tare da nazari Ba ta hay kan titin domin burinta kawai ta gara takalmin ta.

Alokacin kuwa aka bada Hannu kuma daidai lokacin fada ya kaure tsakanin zakiyya da yazeed CeCe kuce suke tayi yana hankalinsa kenan daga titi yana Cewa zakky don't try me this evening

Minal kuwa ta dauko karanta tana kokarin gyara takalmin tare da tafiya a hankali akan titin domin itama ta tsallaka taga mota a guje yana iyowa kanta
Duk kayan cikinta sanda suka kada.

Daidai lokacin yazeed ya lura da ita kokarin kaucewa yayi ya fada cikin wani Dan rami Wanda ruwa ya taru kuma ya daki motan wani

Tun daga sama har kasa yawatsawa minal ruwa ta sule ta fadi kasa yayinda mai dayan motan ya fito......................

Hhhhh finally!

This is my sallah gift to u guys hope you like this chapter

NOTE:
All pictures of characters shown here are not related to the story.

Kindly share,like,vote and comment thank you

Much love and eid Mubarak once again

4th June 2019

Miss untichlobanty💕

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now