CHAPTER 45

2.7K 214 25
                                    

Sulalewa tayi Take yazeed ya bita Ya tsuguna fuskanta cikin tafukan hannunsa yace ke rosy cheeks! Rosy cheeks ! Menene? Kunfan dake kara bulbulowa a bakinta ke kata Daga masa hankali.
Cikin shakewa da kafewar murya minal tace ma..d..dara. Ganin kamar bakinta yayi motsi yasa yazeed ya saurara da tamboyin da yake mata Dan ya rikice.

Ahankali ta sake Cewa mad...darrr..aaa kamin wani kunfa ya kuma fito wa Daga bakinta.

YAZEED yace madara? Ta rufe idonta ta bude a hankali alamun eh. Da Sauri ya kwatar da ita ya mike ya dauko madara ya bude ko kallon Inda kofi suke beyi Ba ya kafa mata.
Tana fara sha ya sauke ajiyan zuciya Wanda yayi dadai da murdawan da cikinsa shima yayi.
Basarwa yayi amma murdin da cikin ta kara yi yasa yayi sauri zau ajiye gorar madaran daya kawowa minal.

Minal kam ta lura da yanayin yadda yake yatsine fuska Dan haka a take tayi saurin sa hannunta ta hade gorar da hannunsa takai bakinsa daya fara zubda kumfa.
Sanda ta tabbata ya shanye kamin ta kwantar dashi a wajen jiki babu kwari ta nufi fridge ta dauko ruwa da wani madaran sai kitchen towel.

Bakinta ta goge sannan ta goge masa nasa bude ruwan tayi zata kafa abaki taji muryansa kasa kasa yace ki dau kofi. Ba musu ta dauka ta zuba tasha sannan ta zauna ta daura kanshi a cinyanta sannan ta bashi ruwa.

madaran ta kara bude musu ta zuba cup din zata sha yayi saurin mikewa Daga cinyarta Dan karfinsa ya fara dawo masa.

Pouting yayi Kamar yadda take masa kullum yace rosy cheeks ni zan fara sha. Dariya ta kyalkyale dashi saboda yadda yayi maganan Kamar wani Yaro.
Bashi tayi yasha sannan itama ta kafa kai tana sha, ji tayi ya fashe da dariya dan haka ta dago da idonta tana masa kallon dariyar me kake yi ?

Yace rosy cheeks literary we just kissed tace uhm? Yace munyi Sumba nida ke saboda daidai Inda na kafa bakina nan kika sa naki. Zaro ido tayi Take madaran ya kwareta sannu yayi mata ya shafa bayanta sannan ya bata ruwa.
Hararansa tayi idonta ya ciko da kwalla muryarta na rawa tace Nide wallahi bamuyi Sumba Ba danni ba..... Sai kuma tayi shiru.

Yazeed sarai yasan me zata ce dan haka yace uhmm? Tace babu sannan ta dauke cups din ta wanke ta nufi dakinta yayinda yazeed ya kira doctor tunda dare beyiba sosai 9:10pm nema.

Koda doctor yazo yazeed yayi masa bayani Dr din yace poison ne.
Yazeed yace ya sani. Dr din yace menene last Abu da sukaci kamin attack din yace cappuccino ne amma kuma abinda ya bani mamaki kullum ina sha ban taba samun attack dinba.

Doctorn yace lets check the expiring date then. Dubawa sukayi amma akwai har shekara 1 da wata 3 before yayi expire. Doctorn zan kaishi lab in bayar domin test dan something is fishy.
OK kawai yazeed yace  ya raka Doctorn har bakin main door sannan ya rufe.
Dakinshi ya nufa ya kunna CCTV sannan ya tafi kitchen direct.
Forwarding Inda su tala sukayi su girki yayi making sure indonshi akan Ronan cappuccino powdern.

Chan bayan sun fita yaga Jennifer ta shigo tana sanda da waige aiko bata tsaya ko ina Ba ta dauko cappuccino powdern tayi mixing da powdered poison sannan ta zaro wayanta tayi kira kafawa a kunnenta tayi kamin chan tace angama aikinindai yasha to zai mutu murus...... gyada kai tayi kamin tace yes ma amma ma problem din baza'a budemin gate Ba sai da izininsa.

Shiru ta kuma yi da alamu tana sauraron dayan bangaren kamin tace yes ma karki damu zan labe da motansu ya shigo ni sai infita...........thank you ma.
Take ya dauki wayansa ya ranbadawa lukman text Cewa a nemo masa Jennifer ko a ina take a muce ko a raye.

Aikinsa ya fara a apple laptop dinsa amma hankalinsa Sam baya kan aikin da yakeyi hankalinsa ya ta'allaka ne akan wakeson kasheshi tunda acikin cappuccino akasa guban kuma shi daya ke shan cappuccino a gidan.

Bayan Kamar 30 minute wayanshi ya fara ringing dauka yayi ta dayan bangaren lukman  yace sir mun samota a kawo motor park da alamu so take tabi motar asuba. Yazeed yace great! aikinka yayi kyau, Ina alfahari dakai.
Lukman yace thank you yanzu haka ma tana hannuna we tricked her to come with us.
Yazeed yace tayaya kuka yi ne?

Lukman yace my man Ba Kai daya bane charming fah kawai nuna mata Nayi ina bukatarta a gado Ba musu ta biyoni tana shigowa mota taga bani daya bane ta fara zagina tana kuka Wai na cuceta na yaudareta zanjawo a kasheta.

Dariya yazeed ya sheke dashi jin yadda lukman din ke kwatanta yadda tayi maganan yace shegiya ai kadan ta gani.

Minal ko bayan ta Koma dakinta wanka ta sakeyi ta canja rigarta sannan tasa hular baccinta ta nufi dakin yazeed domin yi masa tausa Kamar yadda ya umarta.

Koda tazo kofar dakinshi bude kofar tayi a hankali domin so take ta bashi tsoro Kamar dai yadda yara keyi.

Abinda kunnenta ya jiyo mata shiyasa ta tsaya cak tabbas Ba karya bane yazeed ne ke waya yana magana Kamar haka:

"Great aikinka yayi kyau ina alfahari dakai" wani aiki ne yayi kyau?

Wai tayaya kukayi ne?sukayi me?karde abinda nake tunani ne?kai noo yazeed bazai tana kokarin kasheni ba. Wata zuciya ne tace mata kin manta ya tsaneki? To amma in so yake ya kasheni me yasa ya CeCe ni? Kuma ai shima yasha.

"Shekewa yayi da dariya yace kadan ma tagani" tabbas damirin sunan mace yake aiki dashi towai me yake magana akai?

Ganin bazata sami answer dinta Ba yasa tazo gabansa tace ya yazeed dama so kake ka kasheni?

A zabure yazeed ya dago yana kallonta ido cikin ido..............

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Zakiyya zaune gefen wata farar budurwa fat sai sharar kwalla take,Ba laifi tafi zakiyya kyau amma da kaga farinta kasan Ba na Allah da annabi bane.

I am sorry sis! Shine abinda taketa maimaitawa tana shafa bayan yarinyar wacca bazata wuce shekara 21 Ba.

Budurwacce ta kuma share kwalla tace Wai yanzu haka lukman dina yana tareda wata ko?

Girgiza kai zakiyya tayi tace baya tareda ita tunda kince baya sonta nima yazeed dina yayi auren amma ko kallon arziki baya mata ranananda na taho har jibganta yayi. Kidena kuka kinji sister AYUSH?

Let me kuku run for my life before ayi min duka dan yau Nasan zanbar fans Suna tsimayi na

Expect me soon!

Anyway result dinmu ya fito kuma it was masha Allah no problem.
Thanks for your du'as love yah😘

@mzz_untichlobanty 💕

26 November, 2019.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now