CHAPTER 93

2.1K 150 70
                                    

RECAP

Minal tace na Sami idea! Yazeed yace na me fa? Tace tunda dai bisa alamu aljanune suke bibiyarta dole zasu hanata bacci da daddare da rana kuma sai mudinga yi Mata kurwa tunda kaji dai abinda mahaifiyar ta tace kaga sun yarda akwai kurwa kenan. Kaga kawai kowa kallon tabbabiya zai dinga Mata daga nan zamu San abinyi.

CONTINUATION

A makaranta kuwa zayya suna shigowa aka fara kallon sabon motan Dan ba'a sanshi ba saboda ba da wannan motan yazo ba a karan shi na farko. Ansiya musu sabin mota saboda sunyi aure. Kan kace me labari ya karade ai an kawo sabuwar daliba. Motan na tsayawa kowa yayi kur da ido amma me ? Zayya ce da sahir suka fito hannu sakale da na juna dukda ko mintsininta yakeyi.

Ta aika masa harara alamun zata Rama har hostel ya rakata sukayi sallama ashe yeonsil da halsey suna hangosu ta window Dan a second floor suke tana shigowa sanda gabanta ya fadi ganin mutane  biyu sun kafeta da ido da sauri suka zauna da ita a bakin gado sukace dama a wajen mr handsome kikayi spending weekend dinki bayan kin sanr da mu cewa auren mamanki zakije?  Tace da farko dai addinin mu ya hanamu kwana a gidan saurayi na biyu kuma labarin dogone zama suka gyara sukace mun shirya ko zai kaimu Isha'I. Dungure kansu tayi tace ajin fa sukace ki mana alkwari zaku bamu tace an gama sannan suka shirya suka wuce.

Bayan sun dawo daga aji ta labarta musu yadda akayi tass har inda aka daura auren shewa sukayi sukace mude ki bamu tsarabar my dauko ma kowa nata tayi daidai lokacin cingam ya fado yeonsil ta dauka dama ita uwar bari ce babu ruwanta ko me yazo fada kawai take tace la me nake gani anan ? Zayya tayi saurin warcewa tare da  cewa bani chewing gum Dina.

Tafawa sukayi halsey tace kai amma kin Rena mana AI baki cika alkwari ba tunda baki bamu labarin bangaren nan ba. Shine dan renin hankali muna gani condom baro baro kice mana cingam? Dan yamutsa fuska tayi tace con..dom? Halsey tace kwarai. Zaunarta sukayi tare da bata bayani filla filla. Kamar zakanya haka ta Mike ta danna masa Kira ringing 2 ya dauka cikin tsokana yace wifey kinyi missing Dina ne naga... kamin ya karasa tace idan na kara jin kalma daya daga gareka lahira zatayi bako. Wato da gangan kace na taho da wannan abar makaranta ko? Yanzu idan da principal ta gani me zance? Bari ma ka gani yanzu zanzo in sameka saina.....

Yeonsil ne tayi saurin karban wayan ta kashe suka sata a tsakiya. Dungure kanta yeonsil tayi tace kinada hankali kuwa ? Halsey ma ta dungure ta tace mijinki kike ma ihu? Yeonsil ta dungurota tace kuma Dan iskanci harda  cewa zaki kasheshi? A tare suka dungure keyarta sukace daga yau abinda mukace kiyi shi zakiyi.

A gida kuwa ayush ta samu ta fito harda kunna kallo amma me abinda ya fara baiyana shine horror movie. Cikin tashin hankali ta saki remote tare da kashe socket din. Ta koma daki da gudu bata fito ba sai bayan magariba da yunwa ya sakota a gaba. Da sanda take takawa babu kowa a parlourn kuma akwai duhu a hankali ta kunna wuta.

Wani Abu taga ya gifta acikin kitchen din gabanta na dukan tara tara sansada ta shiga amma bataga kowa ba. Shayi ta fara hadawa kawai wuta yadauke kofar kitchen din ya rufu da karfi ihu ta tsala ta taho da sauri taja kofar amma a rufe kuka ta farayi sai taji ana dariyar mugunta a bayanta juyawa tayi kafarta na karkarwa batasan tana fitari ba cikin bari tace waye?

Muryarce tace Mata gani nan a sama tana kalla kuwa ta zube kasa sumammiya. Abinda bata sani ba kuwa shine basirar sahla ce tayi aiki domin ta iya Zane hakan yasa tayi zanen kurwa ta abinda ake cewa 3D.

 Abinda bata sani ba kuwa shine basirar sahla ce tayi aiki domin ta iya Zane hakan yasa tayi zanen kurwa ta abinda ake cewa 3D

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Koda ta bude idonta a daki ta sameta babu kowa saide ba'a canja Mata kayan jikinta ba har ta fara zarni. Mikewa tayi jiri na Dan dibarta taji ance sannu a kujerar dake dakinta. Tana juyowa sanda kirjinta ya buga wata ce zaune da farin kaya irin na nurse a jikinta kwayan idonta kore manya manya da gani kasan da matsala murmushi ta sakewa ayush tace sannu da tashi madam nice me kula dake har zuwa lokacin da zaki warke.  Yake ayush tayi matar tace kina bukatar wani Abu ne ayush tace eh fitsari zanyi. Kamata tayi ta taimaka Mata itadai ganin ikon Allah take domin bata taba ganin me irin halittar ba. Gabanta na faduwa ta shiga bandakin ta fara tsulawa kawai taga wuta ya mutu zabura tayi ta Mike tace nurse ke kika kashe wutan ne? Shiru sake magana tayi amma ba'a amsa ba hakan yasa da gudu ta fito ba tare da ta mayar da suturar ta ba tana haki tace mummy! Mummy!

A birkice mummy ta shigo tana fadin lafiya? Cikin tsinkewan numfashi tace ina.... ina take ? Mummy  tace wa? Ayush tace nurse din. Mummy tace nurse kuma? AI babu wata nurse a gidannan. Cikin Dibir bir cewa tace mummy kice Allah. Tace zan miki karya ne aishatu? Tace mummy na banu wallahi aljanu da kurwa nake gani.

Dariya mummy tayi tace kiji min ke da wani zance wai aljanu da kurwa. Kode minyard ce ta fara tabaki kinga ni barni naje nayi bacci kema ki kwanta ta fadi haka tana juyawa rikota ayush tayi shikin kuka tace mummy na karki barni Dan Allah na shigesu mummy tace ke ayush banson sakrci ya kike Abu kamar yarinya ne ? Ni ki wuce ki kwanta gobe ma tattauna ayush tace inada sheda akwai kurwar a kicin muje ki ganta nasan wannan ma buya tayi idan babu zan barki ki kwanta.

Kitchen sukaje babu komai su yazeed har sun goge. Mummy tace kingani babu komai haba yar kirki. Kawai ke kike ganin cewa akwai wani Abu amma babu komai je ki kwanta kinji cikin sanyin jiki tace toh amma a dakinki zan kwana mummy.

Dakin mummy suka shiga hankalinta ya Dan fara kwanciya hakan yasa ta yanke shawarar shiga bandaki tayi wanka bayan mummy ta tabbatar Mata babu komai a ciki. Da dar dar tayi wankan amma bataga komai ba har ta fara tunanin toh ko da gaske babu komai kawai rudewa tayi? Gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta cikin kwana biyu kamar ana tsotse Mata jini. Duk tayi wani kwarshal da ita fuskar nurse dinne ya fado Mata a zuciya take fitsari ya tsargo Mata. Har ta gabatar tayi flushing amma maimakon ruwa sai taga jini. Juyawa tayi bayan ta rufe ido ta daura hannunta a kirji tace ayush karki damu ba gaskiya bane. A hankali ta bude idonta sai taga jariri anyi masa yankan wulakanci jini yana bulbulowa kamar daga famfo da gudu ta fice Dan yanzu ba ta ciwon jikinta take ba yanzu ta ranta take. Mummy tace ke lafiya kika fito kamar kinga mutuwa? Ayush tace idan kika fadin hakan ma yayi daidai domin naga mutuwar. Mummy wallahi ba tunani na bane yanzu nan naga........

Labarta Mata tayi mummy taja tsaki tace ke ni kin fara fice mini akai inba iskanci ba yaushe katuwa irinki zata dinga wani gudun kurwa da aljanu? Na fara  bacci na zaki wani fito da gudu ki tsinka mini gaba muje naga ni. Ayush ta shige bargo tana rawar sanyi tace bani kara shiga wallahi. Gobe dakin yaya yazeed zani Dan shi yana addu'a.  Mummy tace ni kuma kafura ko? Toh nima na iya addu'ar ai babu abinda zai bani tsoro ayush de batace komai ba illa kara kankame bargo da tayi.

Mummy cikin dure duren ashar ta shiga ban dakin tana fadin wani shegen ne  yake tsoratar min da yata? Aikin banza da wifi ashe ma matsorata ne kunsan dai ni ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya. Har zata fita taga brush din ayush dake jefe cikin sink. Girgiza kai tayi tana kaji shashashar yarinya. Bude famfon  sink  tayi ta wanke tace gashinan ruwa me kyau zata wani ce na jini ne. Kamin ta rufe bakinta ruwan ya koma jini. Murmushi tayi tace ka duba nima har tasa na fara gane gane. Rufe fanfon tayi dukda ko taga jini ne amma gani take kamar tunaninta be dago kanta da zatayi ta cikin madubi ta kalli wannan nurse din saide halittarta ta munana sosai anan murmushi tayi ma mummy tare da daga Mata hannu alamun hello sannan tace SANNUNKI!

Bude baki mummy tayi zatayi magana amma shiru kakeji ji kake jigib tayi ruf da ciki a gaban aljana tana. Waiyo! Waiyo ! Aisha! Aisha ki kawo Agaji ki taimaka.
Ayush ne ta leko kanta ta cikin bargo tace mummy ba komai fa karki damu shirme na ne. Mummy tace kiyi wa Allah kizo wallahi wannan shine fitsari na na 5 kenan kiramini yazeed yayi min addu'ar nan. Ayush tace AI kema kin iya  kiyi kawai kamin ta rufe bakinta wani saurayin aljanu kyakkyawa har yafi yazeed nesa ba kusa ba amma kwayar idonsa Jajawur ne ya zauna a gefenta tare da daura hannunsa a bakinta yana Mata murmushi yace matata kiyi shiru kinji? Kirjinta na bugu ta gyada kai.

A bandaki kuwa mummy fadi "lakad ja'akum innaka innaka humaiya" wai ita ta dage addua take harda daga murya.........

TO BE CONTINUED IN CHAPTER 94.......

SISTERS  YA KUKE YA RAMADAN ? YA IBADA ALLAH YA BAMU LADANSA.

ME KUKE TUNANI GAME DA CHAPTER DINNAN ? SHIN HUKUNCIN DA NAYI WA SU AYUSH YA DACE DASU ?

KARKU MANTA KUYI VOTING DA COMMENTING TARE DA SHARING.

LOVE YOU ALL 💋

miss untichlobanty 💕

8th may, 2020.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now