CHAPTER 42

2.8K 190 16
                                    

Ana cikin jiran ango sai hayani ake ana gaggaisawa da Yan uwa da abokan arziki. Da kaga fuskokin jama'an kasan Cewa cikin farin ciki suke.

Wani matashin saurayi ne ya kutsa mutanen daurin auren sannan ya iso daidai da'iran wakilai da manyan mutane.
Sallama ya musu aka amsa sannan ya tsuguna ya Sanar dasu hatsarin su Sulaiman din.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un suka dinga maimaitawa yazeed ne ya kalli  lukman idonsa Adan zare yayinda shima lukman din yazeed din yake kalla.

Lallai Sulaiman ya kasance Dan clique dinsu lokacin da suke secondary wato su uku abokaine saide shi Baya burin zama soja sabanin lukman da yazeed.

Idanun su ne yayi ja musamman yazeed daya tuno yadda minal din keson aminiyarta zaliha. Yaya zasuyi in sukaji wannan labari matsala bibbiyu ga mutuwar Sulaiman ga rashin daurin auren.

Ganin Kamar wajen ya kara hautsinewa yasa suka daina kallon-kallon da suke.

Baban zaliha ne hawan jininsa ya tashi domin yasan yadda diyartasa ke mutuwan son Sulaiman din tabbas yasan akwai kaddara kuma ya zama dole yin tawakkali amma yaya diyartasa zata dauki wannan lamari? Abu daya ne mafita shine in ta samu Wanda zai kula da ita ya kwantar mata da hankali, to amma taya hakan zai kasance ? Da Kamar wuya tunda Ba bawa wani dama zata yi Ba.

Wannan tunanin yasa hawan jininsa tashi lokaci daya.
Bakinsa na rawa yace Dan Allah Idan akwai Wanda yasan in ya aureta zai iya mantar da ita Sulaiman dinta dukda ko bazata mantashiba amma dai hankalinta zai kwanta ya taimaka ya aureta.

Hawaye ne ya silalo a idanunsa yayinda samari suka dagashi suka sakashi acikin mota akayi asubiti dashi.

Yazeed ne ya kalli lukman kallon aboki ka taimaka ka aureta girgiza kansa ya alamun bazai iya Ba sannan yace yazeed kasan Cewa ayush nakeso kuma how sure are you Cewa yarinyar zata aminta dani?

YAZEED yace na sani lukman amma ka Duba halin da mahaifin yarinyarnan ya Shiga Ina ga ita yarinyar kuma?
Shin kana ganin kaf na wajen akwai Wanda ya cancanci ya aureta? Kana ganin akwai Wanda zai iya kwantar mata da hankali? sannan ya Daga mata kafa ta dawo cikin nutsuwarta kamin ya bukaci hakkinsa?

Girgiza kai lukman din yayi ya budi baki zaiyi magana yazeed yayi saurin Cewa Idan maryam( kanwar lukman din) ne acikin wannan yanayin fa?

Ajiyan zuciya ya sauke yace yazeed ni yanzu Idan ma na aureta ina zan ajiyeta ? Yazeed yace karka damu da wannan ka amince kawai lukman yace amma yazeed kana ganin nayiwa ayush adalci kuwa?
Yazeed yace India har tanasonka zata fahimta kuma ai ita dinma zaka aureta sannan Idan itace awannan yanayi ai bazataso aki auranta Ba.

Lukman yace amma..... Yazeed yace Dan Allah. Ajiyan zuciya lukman din ya kuma saukewa sannan yace shikenan na yarda.

Murmushi yazeed yadan masa sannan ya dafa kafadarsa alamun bada kwarin guiwa sannan.

Tashi lukman yayi ya tsaya sannan yace ni zan aureta.
Kallonsa jami'a sukayi, babu bata lokaci aka aminta dashi musamman da akaga Cewa shidin abokin yazeed, kuma shi yazeed din ya kasance suriki na gari.
Kuma ai masu iya magana na Cewa inkanason kasan halin mutum to ka tambayi su Waye abokansa.

Hakan yasa babu bata lokaci aka daura aure sannan akayi sanarwar jana'izan Sulaiman.
Nan hankali Yan cikin gidan ya kuma tashi aiko nan wasu sukasa kuka yayinda wasu sukayi shewa Suna fadin "ahaiye cass, yo dama anga mai Hannu da shuni an like masa anaso ashiga Dan aci bagas toh ta Allah Ba taku Ba zaliha dai anzama Amaryar lukmanu 😀😀😀😀 auren shige aka mata" wata mata tace yo danma mutanen suna da mutunci naji ance anbada sadaki naira tamanin kome? Kinsan gidan ya kacame banji dakyau Ba.
Wata tace naira tamanin ko sanda rake yafi haka shewa suka kuma sawa dai dai lokacin waliyin zalihan malam ado (Wanda akayiwa yarsa fyade #chapter 2)yayi sallama.

Iya dake sharar kwalla tama kasa magana saboda halin da diyarta ta Shiga domin tunda ta farfado ta kafe waje daya da ido Ba tayiwa kowa magana Ba sannan bata yi kuka ba, ta amsa sallamar sannan ta nufi hanyar kofa tana mai saka hijabinta.

Gaisawa sukayi sannan ya mata ta'aziyya,addu'a sukayi ma Sulaiman din sannan ya miko mata 80k cas Kamar yadda aka bashi sannan ya Samar mata yadda akayi lukman ya auri zalihan.

Godiya tayi masa sannan ta basa 10k nan fa ya rufe ido yace Sam bazai karbi kudin ba. Haka iya ta hakura ta tafi tana kara masa godiya.

Koda ta shigo ciki daki ta nufa ta boye kudin tunda kannenta guda 3 ne kawai a dakin sai innar minal. Matsowa kusa da zaliha data sandake da minal daketa aikin kuka iyan tayi sannan ta lallashi minal nan hankalin minal din yadan kwanta tunda lukman din da aka aurawa zaliha lukman abokin yazeed ne ba wani ba kuma yanada mutunci.

Nanfa suka fara kokarin saka zaliha tayi kuka amma shiru sanda innan minal ta matso kusa ta yi mata nasiha sannan tace ta rike mijin ta da amana ta danne zuciya tunda Sulaiman din ya tafi Anan tayi breaking ta hawaye suka fara zuba tahau shure shure Kamar mai tabin kwakwalwa. Ihu take tana Cewa wallahi ba mutu ba ni Sulaiman dina bai mutu ba,Nasan bazai barni ba ku sakeni,ni kusake ni.

Kanwar iya mai Suna iya murja ce ta fita sannan tace wa jama'a sun gode da halarta da sukayi.

Wannan matarnan ce tace yo ai bansan baban zaliha munafiki,Mara mutunci bane sai yanzu, Ashe batada hankali shine zai aurawa Dan mutane.

Tasss!taji an dauketa da tafi.

🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹

Agidansu Sulaiman kuwa ana sanardasu wannan labari mahaifiyarsu ta yanki jiki ta fadi hospital akayi da ita Ashe coma ta Shiga.

Laila Kanwar Sulaiman rasa Inda zatasa ranta tayi. Kanin babansu Alhaji Ibrahim shi yasanar dasu wannan labari.
Lallashin laila da sauran family yake domin sunyi rashin da saiga goje(from chapter 10) ya shigo yana fito kallonsa kowa ya tsayayi

Shoki ya kwaso ya sauke sannan ya watsa zanku. Babansa ne ya daukesa da mari sannan yace kaide bansan me zanyi dakai ba da'ace a Asibiti aka haifeka da nace an canja Mani Kai, Allah ya Shirya amma ace mutum Dan uwansa ya rasu ko ajikinsa ?

Soka earpiece dinsa da yayi a kunne sannan ya kalli baban NASA yace kai tsohonnan ka kiyayen Idan ba haka ba kauna zaka raka wacan shegen Sulaiman din. Aikin banza duk kunbi kun cikawa mutane gida da kukan Munafurci.

Ke laila ki mana ko kallon Inda yake bata yi ba yace ba dake nake ba? Ta sharesa falla mata mari yayi yace ke Dan ub*nki Dan kinga anasonki shine zakiyi wa mutane hauka?

Kuka ta fashe dashi tace Allah ya isa wallahi Allah bazai barka ba. Wani mari ya dauketa dashi sannan ya take mata kafa yayi ball da ita yace kucaka kawai.

Fitonsa ya cigaba dayi har ya fice yana fadin Daga gadon asubiti uwar taku ma ta wuce.

Hey lovelies masu Neman update gashinan na muku.

Waiting for your votes and comments. See yah

19 November, 2019

Oups ! Cette image n'est pas conforme à nos directives de contenu. Afin de continuer la publication, veuillez la retirer ou télécharger une autre image.

19 November, 2019.

KURUCIYAR MINALOù les histoires vivent. Découvrez maintenant