CHAPTER 53

3K 268 32
                                    

Juyowa yayi domin ya kalli minal dake gefensa wacce ringing din wayarsa ta biyu ta tasa aiko suka hada ido tayi Saurin rufewa Kamar mai Baccin gaske.
Yazeed yayi murmushi cikin rashin kuzari saboda har yanzu bata gama sauka Ba tunda Ba saba sha yayi ba yace na kamaki kazame kallo na kikeyi.

Blushing ta fara bada San ranta Ba kumatunta yayi jaa Kamar tumatiri kamin ta tashi ta zauna tana mai rife ido da Hannu.

Tace ina kwana ? yace lafiya amma Daga yau Ba ina kwana nakeson kice min Ba. Tace Toh me zance? Motsowa yayi ya janyota jikinshi sannan cikin kunnenta yace good morning zaki ce min sai kimin sumba.

Girgiza kai tayi tace ni kunya nakeji. Yana smirking Yace humm! Amma Idan zan iya tunawa dakyau jiya rigarki ma kika cire a gabana kuma da kiketa rife ido a haka muka kwana.

Sai alokacin minal ta tuno aiko ta zabura ta fara kokarin Jan bargo yace rabu da bargo babu laifinsa.
Turo baki tayi tace ai Dan bana hayyaci nane.

Serious face yazeed yasa ya hade gira alamun tunani sannan yace zamu tattauna akan wannan ma amma yanzu karfe nawa ne? Minal ta zaro ido tace bamuyi sallah ba!!

Aiko ta tashi da gudu ta nufi toilet.
Wankan tsarki tayi dukda babu abunda sukayi amma dai a Kore kokonto.
Fitowa tayi yace ko dauko kayanki muyi sallah Anan sannan ymshima ya Shiga.
Dauko doguwan Riga irin na shan iska tayi sannan tasaka ta zauna a bakin gado tana jiranshi yayinda ta Lula tunanin me yasa aka basu Kayan maye?kuma Waye ? Sannan taga yaya aka zuba musu?

Tana cikin tunanin na batasan sanda yazeed ya fito Ba saiji tayi ya hura mata iska a fuska yace kazame me kike tunani? Tace zan fada ma muyi sallah tukunna.

Kabbara sukayi sannan yazeed ya fara rero karatu da zakin murya ga taushi ga tausasa zuciyan mai sauraro. Minal mamaki ya cikata sosai jin zakin murya yazeed,jikinta yayi sanyi sosai saboda yadda karatun ya tsuma ta.

Bayan sun idar sunyi addu'a sun shafa yazeed ya janyota yace my kazame ya akayi ne?turo baki tayi tace nifa banason kazamennan Dan dariya yayi yace zanyi tunani.

Tace ya yazeed wa kake ganin ya saka mana abin maye a abinci ko kunun mu?Sosa goshinsa yayi yana kara samawa minal mazauni a cinyarsa yace nuna abinda naketa nazari kenan. Minal tace ni gani nake so ake a hada tarzoma tsakanin mu kuma ko Waye meyin abunnan yasan abinda ke wakana a gidannan saboda kasan da bakacin abincina......

Pecking goshinta yayi yace kuskuren da na tabayi kuma kenan Ba. Murmushi tayi sannan taci gaba da Cewa Toh kaga kenan ni aka zubawa tunda ansan kai bakaci ko kasha Ba. Kenan Idan na bugu sai ka dauka ni yar shayshaye ce kuma Allah ne ya tons asiri na kaga kenan Daga lokacin kome akace ma akaina zaka yarda.

Zama ya gyara yana kara zurfafa tunanin akan abinda take fadan domin tana making sense. Taci gaba da Cewa kuma kenan zaka iya sakina at any moment saboda wannan.

Toshe mata baki yayi yace shhh bazan taba sakinki Ba! Inaso kiyimin alkawari ko me aka fada miki akaina bazaki rabu dani Ba kuma zaki tun tubeni kuma bazaki rabu dani Ba Komai zafi Komai wahala.

Tace Nayi yace nima na miki alkawari bazan tana zarginki Ba kuma bazan rabu dake Ba.
Rungumeta yayi ajikinsa sannan yace ya Allah ka karemu Daga Sharrin dukkan mai sharri.

Minal ne ta mike yace ina zaki?tace ina zuwa. Parlour taje aiko kalli wayar a Inda yazeed ya buya jiya. Murmushi tayi tunowa da irin haukar da suka dinga yi.

Wayan ta dauka ta dannan on button aiko yana kan contacts Inda yazeed yayi saving numbern shi Ba fita Ba.

Kokarin karanta sunane da yayi saving yayi tunda ta iya karatun Hausa na turancin ma Ba laifi zata rubuta zata karanta saide abinda ba'a rasa Ba matsala shine batasan ma'anan abinda take karantawa ko rubutawa Ba.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now