CHAPTER 87

1.9K 141 48
                                    

RECAP 

Cikin tsohon dakin ajiya ta shiga ta window akwai inda ya fashe dama ta nan take fita kuma akwai tsani (ladder) dan haka ta fice.

CONTINUATION

Bayan ya kashe wayarsa ya kalli bakinsa Abdulhameed Wanda bashida buri saide yayi waka yace Abdul huy ya ka tsareni da ido ne? Abdul yace lamarinka sai kai yanzu kuma wata chika ka samu ? Yace shege mutumi na ka sanni dayawa. Wallahi wata yar secondary ce, Abdul yace kai daga samun freedom sai barna ? Kasan dai a turai baka isa ba.

Dariya suka fashe dashi Abdul yace bara inyi gaba ko? Sahir yace yeah zan biyoka nima sannan suka rabu.
Ringing bell din tayi ta security TV dinsa ya fada Mata password din. Tana bude kofar wani gajeran wando ne ya fara Mata sallama. Da ta kalli parlourn ba'a cewa komai gaba daya sai a slow. Ciki ciki tace hello, murmushin mugunta ya Mata yace hi tare da sake Mike kafa akan kujera yace nasan kin fahimci me nakeso kiyi ko? Tunburo fuska tayi kamin yace ni zan fita yanzu idan kin gama kawai kija kofar zai rufu shi da kanshi saura kimin kauyanci tace ance maka mu talakawa ne? Yavmce to ko kawai na Kira iyayenki ne. Jifarshi tayi da jakar makarantar ta tace dallah jeka.

Yana fita ta warware gyalen ta tare da daure sa akai. Aiki take tana wake wakenta tare da rawar hauka Dan ba iyawa tayi ba sanda ta gyara komai tas tayi ciye ciye da barnace barnace har su gym room dinshi ta shiga tayi tabe tabe. Magazines din Abdul ta samu na yan Mata model. Nan ta fara kwaikwayar yadda sukeyi tana murkude murkude ta ture ture. Allah sarki batasan akwai CCTV camera ba.

............

Bayan kwana biyu, yazeed ne ya shigo, sai gaisuwa ake wullo masa har ya shige office dinsa Dan tsayawa yayi ganin cewa minal bata fara zuwa aiki ba tun jiya tunda kujeranta babu kowa.

Cikin zafin rai ya zauna a kujeran sa ya Kira Jamal yace ya batun personal assistant Dina ne? Jamal yace bros kayi hakuri mana AI Hutun jinya ta dauka,yazeed yace tun kafin ta fara aiki kuma kuka bata? Toh banason irin haka. Jamal yace baza'a sake ba amma me ke damunka? Ajiyan zuciya ya sauke yace kaide bari. Jamal yace Matsalar safina ce ko? Kawai ka sausage Mata mana tunda kai bazaka kusanceta ba. Yazeed yace AI matsalar daga ita ne tunda ta nuna kanta afili na sanar Mata wannan baya gabana ganin ta damu tun auren mu bai shekara ba nace gaea mu rabu tace Sam dole na zauna da ita. Toh ya kakeson nayi? Hmm ganinan zuwa office dinka ma tattauna.

Bayan kamar minti 10 Jamal da minal suka shigo suka samu yana waya bayan ya gama. Cikin fara'a cikin harshen turanci Jamal yace yallabai,wannan itace ms mainasara,PA dinka.

Murmushin manya yazeed yayi cikin harshen larabci yace naji dadin sake haduwa dake murmushi tayi tace nima haka Jamal ne ya kalleta yace yanaji turanci da kuma hausa so kidinga yi masa magana dawa dannan shi kuma ya amsa yadda yaso.

Yazeed ne cikin harshen turanci yace naji ance an miki tiyatar appendix ko? Murmushi tayi yace shin gefen cikinki na daman ya warke gyada kai tayi tace yayi kyau haka akeson ji amma appendix a gefen dama yake.

Yawun rashin gaskiya ta hadiya,amma ta maske. Yace excuse me ko? Inada appointment yanzu, so sai na ganku a reception din anjima. Yana fita minal ta sauke ajiyan zuciya. Jamal yace ms mainasara kun taba haduwa ne bayan na interview? Tace a ah kawai a elevator ne mukace gaisa. Jamal de bai yadda ba amma ya share.  Tace to wai me yasa aka zabe ni? Yace ya zanyi in sani bayan shida kansa ya zabeki.

Kallonta yayi daga sama har kasa yace Partyn yau a haka zakije? Kide tuna yaune.  Sannan ya fice tace yan kamfaninnan a rikice suke dazu yace reception yanzu kuma party. Allah kyauta.

Bayan ta koma gida ta bude walk in wardrobe dinta tayi ta dirje ta dauko farin abaya anyi masa kwalliya da golden hakan yasa ta dauki Jaka,takalmi da komai golden.
Zaune take gefen yazeed tunda PA dinshi ce. Yace ms mai nasara akwai wani party da zaki ne bayan wannan ? Tace mene? Oh eh wallahi yau birthday kawata ne. Aranta ko tace ni wai wani iskanci ne yasa bazai wa mutane hausa ba saide turanci da larabci? Tunaninta ne ya datse sanadiyyar maganar sa yace kinyi kyau kuwa a cikin kayan nayi mamaki.
Tace thank you. Yace zai tafi daidai kuwa da mission dinki na yau. Tace mission kuma? Yace emm, kinga wadan can mutane masu farin neck tie. Kallonsu tayi tace wadan can biyun ko? Yace kwarai larabawa ne amma sunajin turanci Dan haka karki nuna kin iya larabci. Abokan gasar mu ne akan hayr deal kuma sultan wato mai hayr (company) yazo wajennan so nake ki jiyo akan meeting dinsu. Tace kana nufin inyi leken asiri zanyi? Ya zanyi ince ban iya larabcin ba? Yace amma AI ranan nan kinyi pretending ko? Tace ranan nan ai..... wata baturiya ce tace yazeed dama kazo? Daf da kunnen minal yazo yace zaki iya kamin ya wuce wajen baturiyar.

Tafiya wajen mazan can ta fara yi amma hankalin ta yana kan yazeed tana gungunin yadda ta sata aiki. Karo taci da wani ta zuba masa juice din dake kofin hannunta balarabe ta gani  a gabanta hakan yasa ta fada bashi hakuri ta yaransa sai a lokacin ta lura sune Wanda zatayi aiki a kansu. Tambayarta sukayi da fatan bataji ciwo ba tace ah ah. Wucewa sukayi yayinda ta dauko wayanta ta rambatsawa yazeed Kira. Dauka yayi ba tare da yace Mata komai ba tace na kwafsa? Yace mene ? Tace nayi magana da larabci ya zanyi? Yace ke wannan ta shafa mi dace document din ma idan ta kama. Sanna ta kashe wayarsa tace kan bala'I sannan tayi kwafa.

Wajen larabawan taje suna hira sai dayansu yace ko waye wancan yake magana da jeedmar president? Dayan ne yace AI babu Wanda yasan shine president din anan idan bamu ba. Dadin ta ma mu zamuyi gasa ne da balarabe irin mu ba wani banza Dan Nigeria ba. Dariya tayi tace amma wani hanzari ba gudu ba naji ance janar ya fiku shiga wai gaskiya ne na biyun ne yace inji wa? Ai mun masa wani tarko. Ba farkon ne ya nasa alamun yayi shiru tayi dariya tace karku damu ba aiko ni akayi ba  balle ba bada labari na farkon yace kin tabbata? Tace kwarai. Nan suka saki baki suka juye Mata komai ita ko ta shanye tas sannan ta tura masa ta message.

A hanyarsu na dawowa yace ms mai nasara kinyi kokari. Banyi tsammanin zaki iya samo Abu mai muhimmanci irin wannan ba. Tace wannan kuma Cibus dinsu ne. Yace cibus? Me wannan kuma tace kuskuren su ne wannan.

Yace gaskiya ne a kasuwanci faduwar wani ribar wani. Kinada wata baiwa na yaudara da Allah ya baki. Tace mene yace hmm yabo ce daga gareni. Tace waima.....

Wayanta ne yayi ringing ta fara nemansa tana dauka ya datse tace hello? Hello? Yazeed yace saurayinki? Tace babu ruwan ka wannan personal ne.

Kiransa(saurayin ta) tayi amma a kashe sake Kira take a karo na uku. Yazeed yace idan har ya kiraki sai kuma ya kashe, kika kira baya dauka toh akwai abinda yake boyewa.

Tace akan wani hujja kuma kake fadin haka? Yace na fiki sanin namiji idan kuma baki yarda ba ki sake gwadawa. Daidai lokacin motar da aka basu ta tsaya a company din. Cikin turo baki tare da dauke kai tace zaka iya sauka, bama bukatar shawara a wajen Wanda yakeda da tarun yan Mata amma babu soyaiya na gaskiya ko daya.

Sauka sukayi dukansu biyu yana fadin soyaiya ta gaskiya? Shin menene wannan soyaiya da kike batu akai? Purse din dake hannunta ta Dan buga a kirjinsa tana mai fadin tau sannan ta hure kamar da bindiga tayi harbi tace kaji kamar an harbi zuciyar ka da harsashin bindiga kasan wannan yanayin? Yace harsashe ko ? an taba harbina da bindigar gaske.

Jinjina kai tayi tace ba shakka naga alama AI karara. Toh bari kaji soyaiya ta gaskiya wato true love shine zuciyoyin mutum biyu su hade su zam daya, kuyi farin ciki tare ku taimaki juna yayin da aka shiga matsala wani Abu makamancin wannan.

Yace babu wani Abu kamar wannan. Tace akwai! Yace toh yana ina? Kirjinta ta dafa tace nan. Yace okay toh amma ms amina me yasa ko wani lokaci na kallesu babu alamun farin ciki tattare dake? Jumm tayi da fuska ya Mata yar karamar murmushi yace muje muci abinci sai ki wuce.  Yake ta masa cikin gatse tace na gode amma saurayi na zaizo zance gashi har isha'i ta kusa, Sannan ta harareshi ta wuce.

Murmushi yayi kawai ya girgiza kai Dan dariya ma ta bashi gida ya koma ayush ta taro shi gaisawa sukayi tace brother ni har yanzu baka fadamin dalilin da yasa baka tafi dani Partyn nan ba, wai ma da wa kaje? Yace da PA na naje. Cikin shagwaba Tace ina kishi fa. Yauwa brother dama cewa nayi mai ze hana zakiyya ta dawo cikin gidannan da zama maimakon dakin baya. Yace wacece zakiyya kuma? Tace kaide da mantuwa kake. Zakiyya yar gidan umma hani mana yace ba matsala Ai sai  ta dawo nan. Haka ayush tasa umma hani ta dawo da zakiyya cikin gida duk lokacin smda umma hani ke son tace zakiyya ba yarta bane sai ta kasa. Duk lokacin da zata fadi gaskiya kuwa sa farfadiya ta dauke ta.

Bayan minal ta dawo bata cire kayan jikinta ba tana jiran amude sairayinta amma shiru har bacci ya dauke ta saide taki yarda da cewa shima anarta yaci kamar sauran samarin ta.

Washe gari tana shigowa floor dinsu taci karo dasu yazeed secretary dinshi ne yace ms mina da alamu hiran jiya yayi dadi tunda birthday din saurayin ki ne. Kwal....datseshi tayi ta hanyar cewa rike zancenka, ko ganin fuskarsa banyi ba. Sannan tabi bayan yazeed tana mai murkutsa baki.

DA FATAN DAI YANA MUKU DADI DUKDA CEWA YA KUSA KAREWA?

DON'T FORGET TO VOTE,FOLLOW,SHARE AND COMMENT

ONE LOVE💋💋

Miss Untichlobanty 💕

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now