CHAPTER 86

2.2K 151 60
                                    

RECAP

Cikin kakkaurar murya kuma kamar ya gaji da yin maganan yace idan akwai jagwalgwalon da kuke Kira kwalliya a fuskarki toh ki fita ko jarabawar baza'a miki ba idan ko babu to kalli gefenki na dama. Babu musu ta aikata hakan kujerace akai akwai laptop da kuma files guda 10. Yace kalli agogo karfe nawa ne? Tace 11:50 yace mun rasa soft copy na wadannan files da kike gani Dan haka so nake kamin karfe 12:45 ki sake typing duka sannan banason kuskure ko daya idan kuma bazaki iya ba toh KEMA GA HANYA!

CONTINUATION

Kallon files din tayi sannan tayi nazarin lokacin da aka bata indai aikin kwanciyan hankali zatayi toh kana bukatar awa biyu amma a kasa da awa daya akeson ta gama. Zama kawai tayi ba tare da tace mai kala ba, mamaki be ya kamashi da yaji karar keyboard. Ko shi da yakeda saurin aiki yana bukatar awa daya amma mace tayi tunanin zata gama a kasa da minti 55 ? Taurin Kaine kawai na Dan Adam.

Ganin saura mata minti hudu yasa shi yin murmushi faduwa dole. Itako garin sauri ta fice daga wajen Allah ya taimaka tanayi tana saving kokarin komawa tayi dukda ta cire rai saboda akwai file daya a gabanta amma me? Sai taga ga files dinnan gaba daya da me kuskure da Wanda yazeed din ya gyara wato wahalar banza yake basu daga karshe goge aikin zaiyi? Lallai ma mutuminnan. Ai in yasan wata baisan wata ba kaji tsohon nan fa ! Kofar file din tayi sai ta saka kuskure guda 1 daya saboda kar ya gane agogo ta kalla saura Mata second Goma sha biyu ta dannan control-save tace na gama. Yazeed dake Abu cikin wayarsa Dan ya sakankace faduwa zatayi ya kalli lokaci saura second 8. Abu biyu ne suka dira masa a lokaci daya mamaki da kuma kishi, yace karaso ki zauna. Hakan akayi amma me? Yana juyowa suka hada ido take annurin fuskarta ya dauke yayinda a nitse kamar yau ya fara ganinta yace miss mai nasara can you tell me why you want to be my personal assistant? (Ko shin zaki iya fadamin dalilin da yasa kikeso ki zama personal assistant dina?) Tabe baki tayi tace personal assistant na president ba naka ba tunda bansan kai bane president din, amma yanzu da na sani..... mikewa tayi tace kaga tafiya ta gobe zan kawo takardan barin aiki.  Har takai bakin kofa yace dakata ms (miss) mainasara! Da alama sanda kika saka hannu a takardan aiki  baki karanta ba? Ka'idar mu shine dole mutum yayi aiki damu a kalla na shekara 1 idan ba wani laifi yayi aka koreshi ba. Kinga bisa wannan dole kiyi aiki anan batun mukami kuwa nine me komai anan Dan haka no zan zabi Wanda naga dama ya zama kaza ko kaza. Daga gone office dinki ya dawo nan, banason latti! zaki iya tafiya.

Washe gari lokacin free period sai surutu ake a ajin su zayya kaya kaya yayinda ta turo baki tayi jugum kamar ka dangwaleta tayi kuka.
Halsey da yeonsil ne suka zo sukace zayya wai ba yau bane 1 year anniversary dinku keda saurayinki? Ba yau zaizo ba? Ajiyan zuciya ta sauke tace jiya muka rabu sukace mene? Meyasa?

Kuzarinta ne ya dawo Mata a take tace kai kubar wannan zancen kunsan mota Lexus? Yeonsil tace nidai ban taba shiga cikinta ba amma na taba ji. Zayya tace kina ganin nawa za'a kashe domin a gyara Dan karamin kurjewa a jikinta? Ta fadi hakan tana gwada kankantar da hannun ta?

Murmushi me kyau halsey tayi tace ke gajiya me kika aikata? Cikin San yarda magana tana wasa da yatsarta tace bani bace kawata ce. Halsey tace a kudin kasarku akalla dubu dari! Zayya tace haa ? Yeonsil tace zaifi sauki ka biya jikinka.

NA YEONSIL

NA YEONSIL

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now