CHAPTER 94

2K 183 25
                                    

RECAP

Ayush tace AI kema kin iya  kiyi kawai kamin ta rufe bakinta wani saurayin aljanu kyakkyawa har yafi yazeed nesa ba kusa ba amma kwayar idonsa Jajawur ne ya zauna a gefenta tare da daura hannunsa a bakinta yana Mata murmushi yace matata kiyi shiru kinji? Kirjinta na bugu ta gyada kai.

A bandaki kuwa mummy fadi "lakad ja'akum innaka innaka humaiya" wai ita ta dage addua take harda daga murya.........

CONTINUATION

Haka kawai ayush taji ta kasa yin komai jikinta duk ya mutu ta kurawa wannan aljanin ido. Bayan wasu dakiku yayi murmushi yace mahaifiyar ki ta fita raki daga ganin yaya ta duk tabi ta rikice murya na rawa tace waye kai? Murmushi ya Mata yace ni mijin ki ne. Zaro ido tayi tace AI inada miji kuma kai aljani ne tayaya zaka aure ni? Riko hannunta yayi yace zo mu tafi gidan mu masoyiya ta.

Kamar shashasha (dama shashashar ce) ta sauko daga gadon yace rufe idonki rufewa tayi. Taji kamar suna cikin iska bayan sakanni yace bude. Tana budewa ta ganta a wani kungurmin daji ta Dan tsorata amma ganin ya rike hannunta yasa ta Dan saki ranta tafiya suka fara babu jimawa ta hango wani dankareren gida kai kace ba duniya bace.

Murmushi tayi a ranta tace Allah me riko nikam abubuwa sunmin daidai ga miji kyakkyawa ga kuma dankareren gida. Murmushi me sauti aljanin yayi Dan yanajin duk tunanin nan nata.

Suna shiga cikin gidan kofar ta rufe gam sanda gabanta ya fadi juyawa tayi tare da kokarin bude kofar taji kyam Kyam ta juyo zata ma aljanin magana amma sai gata a kasa sumammiya saboda halittar sa ta asali da ta gani jibgege ne. Harshensa kamar na micijiya idonsa kore shar ga kaho, ga jela kai bazai kwatantu ba.

.........

Zayya kuwa tsakar dare ta gudo ta nufi gidan sahir dama tana da mukullinta dan haka babu wani danna kararrawa ta danna kai ta shigewar ta.
Sahir yana bacci yaji ruwan sanyi sai jinsa kake a kasa fat! Ya fado. Mikewa yayi ganin zayya ce yace baby har kinyi missing Dina ne? Tace Allah ya kiyaye dama hukuncin abinda kayi min nazo ma kaga tafiya ta. Tayi ficewar ta kwafa yayi yace yarinyar nan sai na yi Mata seti tukunna. 

A gidan Alhaji mansur kuwa zaman lafiya ake sosai mom da mama kamar yan uwa dukda ko kowacce tana da kishin ta amma sun girmi wannan AI su dai a barsu da kokarin birge Alhaji mansur ko da inna zasu koma tsokanar sa take wai daga yin aure har yayi kumatu ko kwana uku beyi ba.

A gidan yazeed kuwa minal ce tsaye gaban madubi tana taje gashinta.  Yazeed ya fito daga wanka yazo ya tsaya a bayanta tare da karban cumb din. Murmushi tayi tace kana jiyo mutanen ka fa. Murmushi yayi yana cuku cuku da gashin yace na jisu saka rigarki mu kunna kallon mu. Tace kai bazaka sa ba? Murmushi kawai ya Mata yace zamuyi wasa ne anjima kadan. Girgiza kai tayi tana mamakin rashin kunya irin na mijinta. Tirare ta shafa sannan suka kunna kallo su.

Bayan mintuna sukaji knocking pause suka sa kuma suna daidai inda aljani ya fito ma ayush amma su basa ganin komai. Bude kofar minal tayi bayan yazeed yasa jallabiya. Summy (yar lesbian) ce minal tayi murmushi tace ki shigo. Shigowa tayi ta zauna a kujera kanta a kasa tace kuyi hakuri kun ganni war haka wani Abu na gani shine nace dole in fada muku shin nine ko kuma kun gani

DAN ALLAH KU MAIDA HANKALI NAN WAJEN KAR KU RIKICE .........

tace a CCTV footage Dina ina cikin kallon abinda ke wakana har na ga ayush tana magana ita kadai bayan ta sauko daga gadon kawai sai hotan ya dauke bayan sakan 3 ya kawo amma bata daki. Na duba kaf gidannan ban hanata ba kuma har bayin da mahaifiyar ta take na leka banga kowa ba.  (bazata iya ganin aljanin a camera ba)
Yazeed ne ya duba nasu suma Abu daya ne ya faru hakan ya daure musu kai sosai minal tace karki damu kije ki Kwanta idan ma guduwa tayi San kudin ta zai dawo da ita.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now