CHAPTER 82

2.1K 154 43
                                    

RECAP

Jijjigata suka fara yi suna kuka suna kiran sunanta wani ya haskosu da tocila tare da cewa kai! Su waye a wajen ne? Matsowa kusa yayi ganin kamar yara ne. Haska Fuskar minal yayi cikin rawar baki yace YAR UWA? KECE?

CONTINUATION

Gumi ne ya fara tsatstsafo masa cikin tashin hankali ya sake furta yar uwa? Ashe rai kanga rai? Daukarta yayi tare da cewa yaran su biyosa. Zayyana tace ka San mu ne? Ina zaka kai mana ummin mu? Bai kulata ba har suka iso gidansu dakin mahaifiyar sa ya kaita.

Ummu sabir tana cin goronta taga ya fado da mace da yara tace kai dannan, me zan gani haka? Yace ummu nasan bazakiso ba amma ki daure ki danne zuciya kinga matata ma tabar gidannan ne sandiyyar ki. Kwata kwata bana iya zama da mace saboda ke ki daure kibar wannan baiwar Allah ta zauna ko na lokaci kadan ne tsaki taja tace kar ka fice da wadannan Ababa a daki kaima sai in tsine ma. Hawaye ne suka cika masa idanu jiki a sanyaye ya juya ya fita tareda kaisu dakin matarsa. Kwantar da minal yayi sannan ya yaiyafa Mata ruwa. A hankali tace ruwa, ruwa.

Ruwa ya dauko ya ba ma zayyana yace ta bata sannan ya fita ko zai samo abinci. Garzayawa yayi ya koma gidan da yake gadi ya sanar dasu abinda ya faru, nan suka bashi abinci da wasu surutu sukace yakai ma minal din.

Koda ya dawo minal har ta Dan ware nan ya basu tare da ficewa sallar asuba.
Bayan ya dawo minal tayi masa godiya harda hawaye kamin yace niko kamar na sanka. Murmushi yayi yace Dan uwa ne fa. Shiru tayi ta gama nazari bata gano wani Dan uwa ba. Nan sabir ya labarta Mata yadda akayi  aiko ta dinga yi masa godiya.

Dakin mahaifiyar sa ya leka ya sanar da ita zai koma bakin aikinsa. Dauke kai tayi tare da fadin da fatan tare zaku tafi? Yace haba baba kiyi hakuri mana zasu bar gidannan amma yanzu ki daga musu kafa. Naji kawai tace hakan yasa shi sauke ajiyan zuciya harda godiya sannan ya fice.

A hanyarsa ko tunanin halin mahaifiyar sa yake ita indai harka ba ta kudi bane to baza'ayi da ita ba. Tunda ya rasa aikinsa ya kasa gane kanta. Haka ya isa gurin aiki hankalinsa ba a kwance ba.

Samu yayi gidan anata shirye shirye ya tambayi me bayin flower me ke faruwa ne ? Me bayin flower yace bakasan cewa yau diyar Alhaji na biyu zata dawo ba? Sabir yace ikon Allah gaskiya naji dadi. Mai bayin flower yace cab lallai an barka a baya kace kaji dadi? Wannan yarinyar bata ganin kowa da gashi a tsakiyar ka. Sabir yace kaga malam, ni banason gulma. Sannan ya koma bakin aikinsa.

A gida kuwa sabir yana fita mamar sa ta fito ta samu sahla da zayyana a bakin rijiya runa dibar ruwa. Warce gugar tayi tace Dan...... wa ya Baku izinin shan ruwa a gidannan? Zayyana tace ishi mukeji. Tace kinci ..... sahla cikin muryarta na abin tausayi tace kiyi hakuri. Idonta sun ciko da hawaye .

Minal ce ta fito tana kokarin bada hakuri kawai ummu sabir ta adungure kan sahla kan kace tak ta fada rijiyar. Wani irin kara ta saki ta fara ihun neman taimako mutane ne suka shigo aka cirota kamar gawa kokarin ceto ta samarin sukeyi amma minal gani take kamar kasheta zasuyi hakan yasa ta karbi yarta ta wuce suka fice a gidan Allah wadai mutane sukayi da irin halin ummu sabir sannan suka fice.

Tana tafe batasan inda take wulla kafarta ba Dan ji take kamar tana dauke da gawar yarta ne duba da yanayin sahlan. Zayyana ne taja hannunta ta zaunar da a bakin wani gini tace ummi ku zauna anan bara in kawo mana ruwa.

Tafiya ta fara bata masan inda zata Sami famfo ko rijiya Dan sun fara shiga cikin Abuja, pure water kuwa sai ka siya.

🌹🍀

Yazeed ne zaune a office yana shan tea sai ya tuno cewa yanada meeting kuma personal assistant dinshi bai tunatar dashi ba cikin bacin rai ya Mike tare da danna kararrawar neman sa Wanda yayi sanadiyyar faduwar wayansbi ya fashe. Shiru yaji har minti biyu suka wuce hakan yasa ya Dan sassauto tare da tunanin ko baya kusa ne. CCTV footage na office dinsa ya duba amma me? Bacci take harda yawun bacci. Wani tafasa ya farayi baisan sanda ya jefi gini da wayarsa ba. Babu wasting time  personal assistant yasan inda dare yayi masa. Yayinda yazeed ya fice domin Nemo wani waya dukda ko zai iya sawa a kawo masa amma duniyar yanzu sai ayi connecting wayan yanda za'a iya samun muhimman abubuwa.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now