CHAPTER 52

2.7K 259 10
                                    

Suna shiga daki yazeed ya fara kokarin cire riga amma ya kasa minal tace kai me hakan yace aunty sanyi nakeji ki ciremin rigana sai kimin tausan.

Minal ta fashe da dariya tace amma ka bugu dayawa kai bakasan Cewa damina akeyi yanzu Ba? Shima dariya yayi yace woooo kin fado war was yanzu lokacin zafine toh, tace Ba zafi bane yace zafine tace Ba zafi bane yace ZAFINE tace na hakura zafine amma dai ka bugu tunda Cewa kayi sanyi kakeji.

Yace kin yarda kema kin bugu tace na yarda. Rigan ta taimaka masa suka cire. Sannan ta daura hannunta a kirjinsa tace kai yaronnan aradu jikinka Nada kyau gwaliyo ya mata yace banga naki baaaa.

Tace ai nawa yafi naka kyau yace karyane tace kai auntyn ka ne take karya?kunne ya kama tare da turo baki yace sorry aunty amma dai kinsan na Fiki kyau ko? Turo baki tayi Kamar zatayi kuka tace Allah Baka fini baaaa.

Yace nafiki manaaa ki yarda kukan shagwaba ta fara sannan tace Allah Baa fini Ba tsaya fa ka gani kokarin cire Riga ta farayi amma ta kasa Neman zip din riganta tayi amma ta rasa. Tace kai so ka dubawa auntynka zip din ta.

Yace ina zanzo kuma bayan kina rike da dayan hannuna tace mantawa Nayi dubamin tana sakinshi ya tafi luu tayi Saurin rikoshi tare da zaunar dashi. Juya masa bayanta tayi ya Duba can yace naga zip din amma banga kan Ba tace ka Duba na gaji da tsuguno can yace Allah ki kama telan dayayi mini dinkinnan ki hadasa da Yan San;sama a kasa yasa miki zip dinfa.

Tace aiko saina kasheshi yace good aunty na!yauwa ga kan nan bude zip din yayi ta cire sannan ta juyo tace ya kagani ? na fika kyau yace wannan wayone fa ni ai babu brazier a jikina.

Motsowa kusa da fuskanshi tayi cikin ra'da tace kai Dan iska ne kakeson ka kalleni babu Komai abin tausayi yazeed yayi ya girgiza kai tace good yanzu abinda za'ayi ka rakani in dauko Riga shara shara kaga sai in saka sai kaga jikina amma mutane haka zasuce ai inada Riga kaga Mun musu wayo ko?ta fada tana murmushi ita a dole ta kawo idea.

Tadawa su kayi sannan suka nufi dakinta suna ta shirme amma yazeed yanzu zai iya tafiya saide Ba control.
Koda suka shiga dakin minal din, Yazeed Idanunsa a rufe yace ina kika ajiye rigunan toh ? Kicin kicin tayi da ido tace bude idonka! Turo baki yayi yace aunty bacci tace baka isaba bude idonka. Cikin muryan kuka yace Kiyi hakuri to na bude.

Tace good amma fa a akwatina suke babu rigunan a wardrobe dina saboda bana sawa tunda Ba mai gani ko nasaka. Yazeed yace aunty to Daga yau ki fara sawa zannan gani pleaaase! Shafa kanshi tayi kaman Yaro tace angama.

Karamin store din dakinta ta bude ta janyo akwatin sannan ta bude suka kwaso duka transparent rigunan Baccin nata suka jera sannan ta dauki wani baby pink.

Bayan ta miyar da akwatin ta fito tace zan saka rigan.
Hannu yasa ya rife fuskansa kokarin cire bra dinta ta fara dakyar dai ta cire Dan sanda tayi minti 3.

Yazeed ne ya fara kokarin lekota ta tsakanin yatsansa tace wallahi kana lekoni zancewa mamanki kai Dan iska neh. Da Sauri yace na fasa karki fada please.

Saka wancan rigan tayi sannan ta dauke wanda ta cire takaishi laundry koda ta dowo yazeed ya fara gyangyadi da hannunsa a fuskarsa.

Tace tashi mu tafi in maka tausan. Komawa dakinshi su kayi  ya cire wandonsa Daga shi sai short nicker ya dale tsakiyar gadon. Turo baki tayi tace to NASA rigan Baka kallah Ba. Kallon yayi sai alokacin yaga yadda tayi kyau bai San lokacin da tazo ta zauna kusa dashi Ba hannun da tasa zata rife masa baki shi ya ciroshi Daga Inda ya shiga.
Tace rife bakinka kar sauro ya shiga. Yace Gaskiya ne Aunty Ba karya kinyi kyau. Washe baki tayi tace dagaske tana Dan Daga murya yace har cikin zuciyata kuwa. Peck ta masa a kumatu sannan tace amma Gaskiya ka mtsa Dan wajennan yamin kadan yace wa yace miki Anan zaki kwana dariya ta kyalkyale dashi kamin tace ai Anyi an gamayace zamuga ni bazaki kwana Anan ba. Tace to mu kulla, suka kulla yatsa sannan ta fara masa tausan Kamar yadda takeyi wa baba amma harda mugunta aciki.

Tashi yazeed yayi ya zauna a take kamin yace haba yan mata irin wannan dannan ai ko makiyinki albarka ai saiki karyamin baya. Tausa kwata kwata babu armashi.

Hararan shi tayi tace Toh sannu mai armashi sai ka koyamin tausa mai armashi ai ni Idan Nayi wa baba tausarnan har kyautan kudi ko goro yake bani wani sa'in shine zaka wanine Ba armashi? Yace to ai baba kikace ni kuma Ba tsoho ba ne.

Kicin kicin tayi da fuska tace kana nufin baba na tsoho ne?girgiza kai yayi yace wasa nake fa Kiyi hakuri,Tace yafi maka. Kwantar da ita yayi sannan ya fara mata tausan ajiyan zuciya ta sauke tace kai wallahi dadi yace to wannan itace tausan me armashi tashi kimin tace Dan imin na minti biyar sai in ma.

Tausan yayi mata har na minti biyar ko kasa da haka tunda ba Duba agogo yake ba,itako dadi takeyi zatayi winning Dan haka ta fara Baccin karya. Jin saukar numfashi yasa yace toh tashi saura ni yaji shiru. Yace aunty yana Dan jijjigata shiru.

Sake jijjigata yayi yace aunty ki tashi mana kimin. Bude bakinta tayi da kyar tace bacciii....
Turo baki yayi yace wannan fa ojorone fa. Tace zanmaka double gobe daganan ta bingire gaba daya kuma babu lokaci Baccin gasken ya tafi da ita.

Kwanciya yazeed yayi akan ruwan cikinta shima ya bingire haka dai suka dinga auna style din bacci kala kala musamman ma minal Dan babu lungun da batakaiwa ziyara ba akan gadon tsaban birgima.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Da safe around 8 zakiyya ta hau ta dire Cewa sai ta kira yazeed yayinda mamanta tace ta bari a sallameta  mana tace lala.

Wayanta aka bata aiko ta laftowa yazeed kira......

🌹.......

Yazeed kwance minal akan kirjinsa ko sallahn asuba basuyi ba saboda kwayar dake kansu.

Wayarsa ce ta fara ringing aiko ya tashi atake saboda yadan tsorata amma sai yaji wani Abu mai nawi ya danneshi kallon kirjinsa yayi yaga minal tana bacci hankalinta kwance Dan batamasan wani Abu waishi waya ya buga ba.

Dama kunsanta da nauyin bacci a haka ma ya aka kare?

Ahankali ya dagata ya kwanta da ita akan pillow yana murmushi kamin ya tashi ya dauko wandonsa dake wulle akasa ya Ciro wayan sai alokacin ya lura da yanayin da yake sannan duk abinda ya faru na haukarsu ya dawo masa kamin ya Lula duniyar tunani wayansa ya kara ringing hakan yasa ya dauka.aiko kuka ne ya fara ma dodon kunnansa marhaban.

Yace subhanallahi zakiyya menene ya fadi haka yana zama akan gadonsa gefen minal.
Tace baby boutique dina? Yace me yafaru da boutique din tace ya kone gaba daya Wai babu abinda aka cire sabon ma an kwashe kayan ciki sannan aka rusa.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yazeed ya iya fada kamin yace Kiyi hakuri Allah yasa haka shine mafi alkhairi bari idan kin dawo zamuyi magana sai a gyara ko? tace Toh baby saina dawo.
Yace I miss you tace me too sannan ta kashe wayarta ba ko godiya.

Wallahi banyi niyan typing ba amma danaga comment din wata Wai batayin bacci dakyau kwana biyu saboda jiran update shi yasa na fara rubutu karfe goman dare.

Oya Kiyi voting,commenting and sharing. Ahhh!wallahi na gaji ga bacci nakeji.

Saida safenku ga wadanda basuyi bacci ba.

Wanda su kayi bacci kuma good morning!😜

Karamarsu babbarau ce

Miss untichlobanty💕

9th December, 2019

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now