CHAPTER 54

2.7K 241 18
                                    

Koda ya Abubakar ya dawo daukan Laila yayi direct sai gidan aunty fauziyya sannan yace kar ta Fadawa kowa abinda ya faru Dan bayaso su fuskanci matsala Idan yace zai aureta sannan abin zai iya shafan yaransu sannan next week zai kaita asibiti domin a tabbatar babu shigan ciki.

Itakam kuka take tayi Dan abin ya fara daura mata kai Dan har yanzu bata dena bleeding ba ga irin azaba da takeji amma dai tayi deciding zata Fadawa aunty fauziyyan matsalanta tunda ita daya ne tasan abinda ya faru da ita.

Koda suka iso sallama ya Abubakar yayi. Aunty fauziyya ta fito da Sauri domin dams su take jira ta riko Laila tana mata sannu da kai kawai take amsawa. Fiki ta Shiga da ita yayinda akabar ya Abubakar a parlour.

Direct toilet ta nufa da ita sannan tace ta fara core kayanta tana zuwa bata ta sallami ya Abubakar.
Parlour ta sameshi sannan ta tambayeshi Karin bayani tunda bayani kadan ya mata a waya.
Nan ya fada mata duk abinda ya sani da abinda Laila ta fada masa. Lokacin da ya gama bayani mamaki ya cikata tana kasa magana can ta sauke ajiyan zuviya tace Allah ya rabamu da azzaluman Yan uwa da dangi ya Abubakar yace Ameen. Aunty ni zan wuce tace tsaya kasha ruwa mana yace a ah babu Komai ai ina godiya amma aunty ki tabbatar babu Wanda yaji Dan Allah tace karma damu Insha Allah babu Wanda zai sani yace na gode Allah ya saka Idan kuna bukatan wani Abu sai Ku kirani tace Toh ba matsala sannan ta rakashi koda ta dawo ta sani Laila yanda ta barta babu wani kayanta da tacire.

Aunty fauziyya ta riko kafadan ta tace hakuri zakiyi acikin gama ya gama Koma gode Allah kin zamu mai sonki tsakani da Allah Idan ba haka ba ai Anan zaki fuskanci tashin hankali.
Acikin sheshekan kuka tace ni babu abinda ke damuna illa yadda jinin yaji ya tsaya kuma marata azaba takemin.
Shiru aunty fauziyya tayi tana nazari kamin can ta girgiza kai domin kawar da tunanin da take Dan ba Abu mai yuwuwa bane.

Ruwan zafi ta hada mata sannan tace ta Shiga ciki kuma ta tsaya akanta Dan tasan Yan Mayan yanzu ba sason ruwan zafi(Cesar tsofi)
Fire kayanta tayi amma tabar vest sannan ta Shiga ga mamakin aunty fauziyya batayi ihu ko nuna wani alamu na Cewa taji ciwo ba Kamar yadda take zubda mini. Don't ita a tunanin ta idai har taji ciwo da yake zubda wannan jinin to ko tafiya bazata iyayi ba. Kai akwai alamar tambaya Anan wurin.

Matsowa tayi kusa da ita ta zauna sannan tace Laila tana mai riko hannunta dago da rinnanun idanunta tayi ta kalleta. Auntyn taci gaba da Cewa zan miki wani tambaya bawai Dan inaso in banbaro miki tsohon ciwo ba sai Dan in gano wani abu. Gyada kai tayi alamun tanaji.

Tace kin tabbata Cewa wani abu ya Shiga tsakaninku?gyada kai tayi har lokacin hawaye basu bar sintiri a fuskanta ba tace Kiyi min bayanin yadda Komai ya faru Dan kinsan Abubakar bazai iya min bayani a faiyace ba.

Nan Laila ta fada mata yadda goje ya mata karya har ya kaita dakinsa da irin kokuwar da sukayi har izuwa sanda ta suma sannan ko da ta farfado ga yananyin data tsinci kanta.
Jinjina kai aunty fauziyya tayi sannan tace wato kina nufin bakiji sanda ya Shiga jikinki ba har kika suma kawai dai kinji maranki ya murda? Ta gyada kai.

Sake kallonta aunty fauziyya tayi tace yaushe ki kayi al'adar ki ?shiru tayi kamin tace kwana 28 da suka wuce.
Aunty fauziyya tace bayan kwana bawa yake kewayowa? Tace hakan kewayo min bayan kwana 27 ko 29 tace kina nufin jiya ya kamata ki fara. Ta Daga kai tana mai nazari domin itama ta fara hada possibilities da aunty fauziyya ke hadawa.
Tace Idan kina al'ada kina ciwon Mara ne?ta girgiza kai alamun a ah
Aunty fauziyya tace tambaya na karshe shin kinajin wani zafi hakannan Kamar ciwo Daga ciki banda na maranki? Ta sake girgiza kai.

Murmushi aunty fauziyya tayi tace ina tunanin bayi raping dinki ba. Kallon neman Karin bayani Laila ta bita dashi tace ban tabbatar ba amma alamun sun nuna bai miki Komai ba ni a ganina kafin ya miki wani abu al'adarki tazo Dan haka dole ya rabu dake.

Atake Laila ta fito Daga ruwan daya Koma jaa Dan basu ma lura da launin ruwan yana canjawa ba.
Kusa da aunty fauziyya tazo tace toh amma me yasa Mara ta kemin ciwo? Ta fadi hakan tana mai daina zubda kwallah Dan hope ya samu.

Aunty fauziyya tace abu biyu nake tunani ko stress yakawo miki cramps din ko kuma sauyin jikinki Dan wasu Idan suka fara baya musu ciwo da sunyi shekara 18 sai ya fara cramps wasu kuma da ciwo zasu fara da sunkai 18 sai ya dena wasu kuma kwata kwata baya musu ciwo wasu kuma da ciwon zasu fara kuma ko sunkai 18 baya dainawa sai sunyi aure yake ragewa.

Jinjina kai Laila tayi tace aiko 18th birthday na is few months Away. Aunty fauziyya tace bari na kira wata kawata likita ce ta dubaki.
Dakinta yaje ta dauko wayanta sannan ta kira kawarta ta mata bayani a takaice. Nan likitan tazo ta dubata tace babu wani abu daya sameta mensuration ne kawai. Dadi kashe laila. Painkillers ta bata sannan tace ta rage damuwa Dan shi yayi causing zuban jinin dayawa. Murmushi tayi tace Insha Allah Dan farin acikin daya lullubeta a wannan lokacin tama manta da Cewa an mata rasuwa kuma mahaifiyarta na asibiti.
Kiran ya Abubakar aunty fauziyya tayi tace yazo da gaggawa akwai abinda zata fada mishi shiko duk ya tsure karfa aje cikine da ita dukda ko da wuya a gane cikin kwana daya inba Anyi test ba.

🌹........

Itakam auntyn Laila da ta dawo bata ganta ba bata wani damu ba ta dauka gida ta tafi. Itace ma me Dan kokarin da take zuwa tana Dan zama akan ummin nasu Dan wasu Daga cikin dangi Cewa sukema Wai bata lokacin ne su zauna akanta Dan babu abinda zai hanata mutuwa. Sai kace su suke kashewa.

Koda taga har safiya shiru babu Laila babu alamarta kawai sai ta kirawo nurse tace ta kula da ummin zataje gida tayi wanka.

Allah sarki umminsu lailai!duk abunnan da take fuskanta saboda ita daya mamanta ta Haifa kamin ta rasu wanda ake zargin tsafi akayi mata. Shiyasa kaf Yan uban babu mai sonta saboda irin kaunar da babansu ke nuna mata.
Auntyn nan ce ma suke dan Fadawa kaf gidan.

Gida ta wuce abina ta Shirya sannan ta dawo asibitin wayan lailan ta kira taji a rife kawai sai tace bari zata sake gwadawa anjima maybe network ne sannan ta zauna taci gaba da taryan kawayen Ummi Yan gaisuwa da dubiya.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Abangaren su minal kuwa ita ta fara tashi jinta kwance jikin yazeed yasata yin murmushi sannan tadan kamo sajen dake kwance a fuskansa luf luf tana wasa dashi........

Gaskiya na gode sosai da supporting dina da kuke yi Allah ya biyaku.

Sainaji comments dinku yau bakuga yanda na dinga murmushi da ina karantawane ba Kamar wata shashasha.

Insha Allah zanyi kokari ina yi muku reply

Ya kukaga yadda na warware matsala Laila?yayi ko?

Karamarsu babbarsu ce fa😉

Miss untichlobanty💕

11 December, 2019.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now