CHAPTER 27

2.8K 185 14
                                    

Juyi minal tayi tace inna bacci nikeji,Wai har asuban yayi ne?

Haushi abin yabawa yazeed hakan yasa ya wantsalar da pillow din da take kai,aiko babu shiri ta mike ganin shine yasa taji wani faduwar gaba yazo mata

Tunda take arayuwarta bata tana jin faduwar gaba irin wannan Ba kuma bata taba jin tsoran wani Kamar yadda tsoron yazeed ya shigeta a yanxu Ba.

Wani irin kwarjini yayi Wanda tayi nadamar kallon idanunsa domin kuwa ko lokacin da suka fara haduwa bata kallesa da kyau Ba

Wani kirma jikinta ya fara ta fara karkarwa Kamar mejin sanyi.

A hankali muryatta Kamar zatayi kuka tace sannu da zuwa.
Wani kallo yazeed ya mata Wanda yasa hanjin cinkinta kadawa kamin yace uban Waye yabaki izinin kwanciya balle har kiyi bacci? Tayi shiru...

Bakida kunnene ko yaya?muryanta na rawa idanunta ya cicciko da hawaye tace kayi hakuri yace my friend will you get down, zaki sauko ko saina taka ruwan cikinki?

Zama yayi akan kujera tare da dago kansai yanaso ya karewa minal kallo amma ya hakan ya gagara sabida kirjinsa dake bugamasa da Sauri da Sauri amma dai baikai na minal Ba sai ya dauki hakan amatsayin baccin rai da ke damun sa.

Dan haka sai ya jingina Kansa da allon gadon yana mai lumshe idanu Kamar yadda yayi can baya sanda ya fara haduwa da ita a gidansa saboda takaici da ciwon kai da ta hada masa.

Minal ko gabadaya jikinta yayi sanyi,ta sadakar Dan ita a ganinta Allah ne yake ramawa mutane irin tsiyar data musu sanda take gida.
Tayi tsuru tsuru da ido Kamar Mara Gaskiya,gabadaya jikinta ya jike da gumi ga wani fitsari ga zazzabi ya sauko mata tsabar rudewa.
Dukkanin shikashikan tashin hankali ta cikashi a halin domin ko hawaye sun Dade da fara safa da marwa a kumatunta.

Sanda suka dauki kusan minti goma a haka kamin yazeed yace sannu.

Minal Kam ta kasa dabbaka Komai Dan ita ko a film bata taba ganin irin yanayin da tashiga Ba ganin take ko yaushe ma zuciyarta zai iya bugawa ta mutu zaboda yadda yake bugawa har cikin dodan kunnenta takeji

Abubuwa dayawa ke yawo azuciyar yazeed Wanda yana fahimtar wasu,Wasu kuma baya fahimtar su

Kinsan dai  jarumi sai jaruma, toh amma ba wannan ba ki sani ko ma waye ya aiko ki gidan nan toh fa ki sani ya cuce ki.
Mahaifiya ta ta Riga da ta aura min ke to amma ki sani ni bazan ciyar da ke ba Dan haka zan ciyar da ke da sharadin zaki dinga biyan komai har kudin haya idan ba haka ba kisan inda dare ya miki.

Baki na shirin zubar da hakwaran ta saboda rawa tace Dan Allah Allah Allah ni banida wata sana'a da Nike da ita bazan iya biyan ka ba amma zan iya yi maka aikin wahala.

Shiru yayi har ta fara tunanin ko yayi bacci ne kamin ta ji yace abinda nace kiyi agidannan su kadai zakiyi idan kina neman izinin yin wani abu to ki rubuta a paper ki ajiyemin. Kuma kada ki sake ki shiga sabgata Mata na tsakanin ki da ita gaisuwa. Saura kiyi ginin fadawa wani wannan zancen.

Sannan kar ki kuskura ki hau min kan gado tunda ba da shi kika zo ba. Zan iya miki alfarmar ki kwanta carpet ko kujera before  I know what to do with you.

Itade taji bazata kwanta a gadon Ba sauran kuwa toh sai ta Allah.

Na gode shine abinda kawai ta furta kamin ya Mike ya bude toilet ko me ya duba oho sai ya fice. Wani nauyayyan ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin numfashinta Wanda bata masan ta rikeshi Ba sannan ta goge hawayenta sannan tadau bargo ta Komai kan kujera ta kwanta tare da rufe kafafunta

Yazeed kuwa yana komawa dakinshi yayi wanka tare da brush sannan ya fito dressing room dinshi ya Shiga ya dauko pyjama dinshi blue tare da Rigan ya saka sannan ya haye gadonsa ya kwanta yana mai lissafi yanda rayuwa ta kasance masa

Hakadai bashi yayi bacci Ba sai wuraren asuba koda ya tashin sallahn asuba Kansa yayi masa mugun nauyi hakadai ya daddafa yayi sallah yayi azkar yau ko karatun Qur'ani bai samu yayi Ba ya koma bacci. Dama Ba kullum yakeyi saboda yanayin life.

Minal ko tunda tayi asuba taje kitchen ta nemi kayan aiki aiko batasha wahala Ba ta samu ta kama aikinta karfe 8 cif saiga su atine da su larai sun shigo sukaga babu kayan aikinsu parlour suka leko jin motsin mutum aciki aiko da gudu gudu Sauri Sauri suka karaso

Atine tace Allah sarki yar uwa yaushe Rabon da mu ganki ziyara kika kawo manane ko wajen hajiya kikazo kika bage da aiki saide kash hajiya ma jiya da daddare tabar kasan itada danginta kinsan fa mai gidan ya karo aure
Duka atinen ta fada a numfashi daya zuwa biyu Asabe ta kara da ya karo wulakanci Ba larai tace baza'aji mutuwar sarki abakina Ba

Minal ko murmushi take tana binsu da idanu Dan batada abin Cewa
Aikin sukayi kokarin karba minal tace ah ah sukace to shikenan suyi tare kamin ta yarda amma dukda haka tana tsoro kuma tana ganin kamar haram zata ci.

Su kuwa sai hira suke mata harda tambayarta ko zata kwana musu Dan sunaso suyi kawance da ita tace musu ai Ba kwana Ba kwanaki ma zanyi ta fadi haka tana bawa kwanakin karfi, aiko sunji dadi Dan su basu gane me take nufi ba

kafin karfe 10 sun gama Komai saura part din yazeed Wanda dama tunda basu ke gyarawa Ba lukman ne kuma yazeed yayi masa message Cewa Ba sai yazo Ba.

Su atine sai janta suke da hira tun tana nokewa har ta saki jikinta sumo abin ya musu dadi, binta tace ni wallahi na kosa naga amaryar Allah dai yasa Ba irin madam zakiyya bace

Atine tace yo imma batada mutunci ai ita ya shafa minal de tayi tsit tana jinsu
Minal tace to ita bari taje sama tayi wanka larai tace Wai ko kema bikin kikazo ne naji kina Cewa bari kije sama kiyi wanka ? Rasa amsar da zata basu tayi sai atine tace kinada kayan sawa?
Binta tace ji wani tambaya dole da kayanta zata zo mana

Minal tacewa atine Dan Allah kinga rabu dasu zo Kiyi mini wani taimako

Sukace to sai kun dawo kamin su minal suka wuce dakinta ta cire hijabinta sannan ta kalli atine

Atine ko zare idanu takeyi domin in batayi kuskure Ba nanne dakin da aka kawo Amarya

Minal tace kinga kwantar da hankalinki nice amaryar ni zoki nuna mini Inda zan sami kayan sawa
Atine ta zaro ido tace Kece ME?

Minal tace kinga shiyasa ma ban dadi muku Ba saboda ban Shirya yin bayaniba zoni ki nuna Mani

Nuna mata dakin dressing atine tayi da yadda zata canja combination din daga 00000 sannan ta nuna mata na toilet ma

Kamin ta fita tana mamaki da kuma al'ajabi minal kam wanka tayi sannan ta koma parlour jin shiru yazeed bai fita Ba yasa tace kika ma ya five run asuba idan Ba haka Ba ya za'ayi ace mutum yana bacci har 12.

Alokacin data koma kitchen domin dauko su tsintsiya su atine na kitchen din Suna cin abinci Suna ganinta sukayi caaa Wai meyasa bata fada musu akwai chemistry a tsakaninsu da oga sir Ba ?Wai kuma me yasa yallabai ya mata abinda ya mata kaman wata 3 zuwa 4 da suka wuce?

Murmushi tayi tare da tabe baki tace sirrin ne

Daukar tsintsiyarta da packer tayi ta wuce side din yazeed

Kirjinta ne ya fara tsinkewa karfa yaje yananan,hakan yasa ta fara sanda Kamar Mara Gaskiya sannan a hankali ta bude kofar da take ganin side dinshi ne tunda de tasan na mom

Leko kanta tayi taga..........

Me tagani?

Uhm kun ganni all of the sudden ko?ai bazan iya babu Ku bane kun zama wani bangare na life dina

😭 I have 2 exams on Monday please karku manta dani a addu'o'in ku

Ina sonku sosai wattpad fans dina😘
Don't forget to vote,share and comment

Miss untichlobanty💕

4th October, 2019

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now