CHAPTER 95

2K 147 45
                                    

Yin duniya mummy tayi safina bata yarda ba daga karshe ma dariya ta sheke dashi ta koma dakinta. Ta kwanta tare da kashe wuta ahankali ahankali iska ke kadawa a jikin labule yana kara karfi kofofi da da taga ne suka fara kara ga bakin kura yana kadawa hajaran majaran. Ruwa mai karfi ne ya tsinke tare da cida daidai lokacin kuma yazeed ya sumbaci minal yayinda safina............

A bangaren ayush kuwa aljanin nan daureta yayi kullum zaizo ya sha jininta bayan azaba da yake Mata da wuta tare da bata tafashasshen ruwan diwa mai jini da azabar wari. Gashi bata ganin komai sai jarirai. Kullum tamabayar ta me tayi masa? Ganin ta dameshi yasa yace ke saurara kiji, nine aljanin da aka tura na mantar da kowa da sharadin duk randa suka sake yin aure zan rasa nawa auren ba wannan kadai ba matar tawa ni zan kashe da hannuna.
Dan haka yanzu na rasa matata, amarya ta a sanadin ki shiyasa ya zama dole ki zauna da ni.

Kuka ta fara yi tana bashi hakuri shikam ko ajikinsa. A kwana a tashi babu wuya har wata daya ya shude. Su minal sunje sunyi ma ummu amina godiya sosai na yadda ta kula da minal inda yazeed ya dauki main aikin da za'a Mata. Anan suka samu sabi'u wagon sabi ya makance. Ummu amina ke sanar dasu AI tun randa minal tasa kafarta tabar gidan yake kuka ashe yana sonta kawai haushin mijin da ya AURETA sannan ya wulakanta  ta ahalin tana dauke juna biyu yakeji. Hakan yasa yake sauke haushin akan yaran.

Talauchi da yanayin rayuwa tasa yake dabanci amma deep down can cikin zuciyarsa mutumin kwarai ne. Yayi kuka har ya gaji har ya kasa controlling hawayen sa. Hakan yayi sanadiyyar makancewar sa cikin shekaru 4.

A yau ne ta kasance an bawa su zayya hutu zata dawo gida yayinda sahla kuwa dama day takeyi Dan haka kullum zuwa taje ta dawo ne amma dai tare akayi hutun Dan makaranta daya ne.

Kuma a yau dinne LUKMAN da matar sa kuma aminiyar minal ZALIHA zasu dawo kasarsu ta gado wato NIGERIA.  Saide su Allah da daya ya basu dukda cewa karami ne shekarun sa bakwai. Amma har yau fa jiya I yau ne kullum sai sunyi rigimar nan dai tasu.

Minal an cakare anci ado sai walwali take tana ta zirya tsakanin kitchen da dinning room zakiyya ce ta shigo da abun koyar tafiyanta Dan shekara 15 a zaune ba wasa bane. Mashkur yace suma gode Allah akwai hope zata iya taka kasa Dan yanzu leave shima ya dauka yazo zai Dan zauna da su yazeed a sake karfafa zumunta da shakuwa.

Hira suka fara ita da minal suna jimamin ko  ina ayush ta shiga? Zakiyya  tace ke ni bar banza AI wallahi ma taje Allah kiyaye hanya. Minal tace uhm uhm fa idan kuma taje ta bata rayuwar wasu yanda taso yi wa namu fa? Zakiyya tace  kuma fa maganarki gaskiya ce toh amma... bata karashe ba sanadiyyar Umma hani da ta shigo da saurin ta tana  fadin uwar daki akwai matsala banga hajiya ba. Minal tace ai hajiyoyin maki yawa garesu wacce ? Tace hajiya babba mana na duba...... hayaniyar da suka jiyo ta window din kitchen yasa ta yin shiru kamin suka fita.

Aikuwa mummy ce ta tattare zani tana sharar gudu kamar mota sharon.kai kace standby generator aka jona Mata ga security da masu aiki sunyi ca sai binta suke amma ta file musu.
Waje ta fice ta ari titi suna bin ta a baya.   Ba komai take fadi ba sai kai jama'a ga mutuwa ga yan boko haram, ku gudu.

Irin yan acabar nan sun taru dama kawai sukaga Mata cikin kaya mai tsada harda sarkin gwal tana gudu tana fadin ga mutuwa shiyasa kafa me naci ban baki ba? Gudu suma suka fara, wasu nayi adungure su diro daga machine din suyi kolin koli su kwalu da kasa sannan su Mike su cijewa rigar su iska. Irin stop stop dinnan na yan napep suka wuce shugaban wajen sunan shi dogo me babban Riga.

Ana cikin cakwakiya da shi akan kudi ya sakami mai napep kenan zai nana da kasa yaga taron mutane ana gudu cuceshi kawai ake wani fiwt ! Fiwt ! Kakeji abinda akee fada yaji aiko ya sako mai napep din dam a kasa ya fita da gudu shine a gaba gashi yafi kowa tsayi rigar iska ta cikata ji kake fafar  fafar baka ganin komai se babbar rigarsa yayinda yake sambado gudu zundum zundum.

Inyamurai masu saida doya sukazo wucew inyamurar ka bajin hausa suke ba amma sunji Boko haram take suka bi ta Kan doya yayin da mamar su tsohuwa kafa ya hau mazari ji kake curr ta saki fitsari.

Haka suka dinga kwasar mutane, me shayi ne, masu kasa irin kayan marmari a titi ne.... sanda akayi gudu iya gudu aka gaji aka tsaya hutawa dogo yace wai ni wa ya gansu ne samrin nan sukace wannan hajiyar ce.  Yace wai to ma a ina kika gansu ne? Dariya tayi tace zakusha mamakin inda na gansu. Cikin mafarki nagansu in fada muku. Ashar irin ta yan daba ya danna yace wannan matar ta ma raina mana hankali wallahi kai kuyi Mata na jaki.

Rufeta akayi da mugun duka matan inyamuran nan suka zage dantse suka kiranta kamar sun Sami sakwara. Akayi Mata ruf dubu aka jijjibge ta. A TAKUCE de daga nan itama tasan inda dare yayi Mata domin haukace wa tayi dalilin da yasa haukace kuwa shine saboda lokacin da za'a tsafin anyishi ne cewa in dai ayush tana raye mom din yazeed bazata taba yin hankali ba toh yau da safe ayush tayi gaba sanadiyyar cinye gaban ta da aljanin yayi domin satin ta daya a gidan wasu halittu masu Lama da kuda suka fara fitowa daga kasar ta suna cinye Mata fata. Atakaice de tayi mutuwar wulakanci iya wulakanci ga bata sallah ga shirka ga zalinci ai kowa ma yasan makomar ta.

A gida kuwa safina fadi take nikam yanzu komai nawa ne nayi baje baje kawai abinda yamin saura shine na fitar da wannan kucakar matar tasa.  Waka take tana rangaji daure da towel zata shiga wanka saboda ance za'ayi baki kar su kawo Mata raini.

Bude bandaki tayi tana rangaji da juyi. Jijjiga tayi zatayi juyi, juyin ta ke da wuya santsi ya kwasheta ya hada da gini sannan ta fadi ta baya ta doke da toilet sit a take a wajen jini ya cika kwakwalwar ta sai barzahu.  Allah yaji kan mu'umini ameen!

Motar su zaliha ne ta faka a cikin gidan su minal.  Da sauri yaransu me suna kabir ya fito yana fadin wow daddy! Gidan uncle dinnan ya hadu. Kace ya ma sunanshi? Luku yace sunan shi uncle yazeed. Ciki ya shiga da gudu yana fadin kowa ya fito , king kabir yazo. Nine sarki kabir Dan lukman dariya minal tayi tana saukowa tace maraba sannu da zuwa Dana sarki kabir.

Alamun tunani yayi kamin yayi sauri ya riko hannun minal yace kece wannan kyakkyawa matar uncle handsome ko? Murmushi tayi masa sannan tace kaima AI kyakkyawan saurayi ne kabir Dina. Yace toh ya akayi kika sanni? Tace mommyn ka ne ta tura min hotonka.

Dadai lokacin su zaliha suka shigo rurrungume juna akayi aka Dan zubda kwalla abin ka da Mata. A one sitter  zata zauna shima luku na yayi kokarin zama. Tureshi tayi shima ya ture ta. Ture ture suka soma kabir ya girgiza . Dan in da sabo ya Saba ya samu guri tare da fara latsa tablet dinsa yana shan alewa. Sahla ne ta sauko da tayi bulbul da ita tana dauke da juna biyu karami shekaran jiya suka San hakan fadi Dan samri Kaine kanin namu? Dago kanshi kabir yayi yace wow! Kaga mata kyakkyawa fara sol idan na girma yar ki zan aura.

Zaliha ne ta zauna a kujerar luku ya ciccibeta ya dagata shi ya zauna. Dariya tayi tace daidai kenan ta dake cinyarsa. Wani tunani ne yazo masa Dan haka ta kasa kasa ya fara tattaba Mata jiki ganin zai nemi ya tsinkata gaban yara yasa ta tashi kuma duka abinda sukeyi akan idon minal.

Sahla kam tuni game ya 'bage tsakanin ta da mutumin ta kuma sirikin ta acewar sa fa kenan. Hira su minal suka kafa yayinda luku yace ina mutumina ne? Minal tace na barshi a daki yana shiryawa yaci ace ya sauko ma yanzu.

Daidai lokacin yazeed ya fara saukowa yana fadin my man ! Tare da fadada murmushin sa. Rungume juna sukayi kabir kam ajiye game yayi yazo ya kewaye yazeed sau uku sannan ya kalli baban sa yace daddy zan iya zama gidan uncle dinnan Dan inyi kyau? Luku yace kai de da masifar kyau dinka. Indai Abu na da kyau toh kai shikenan kabi ka damu mutane kenan akai.

A mota kuwa tunda zayya ta shiga take ma wa sahir magana amma ko inda take bai kalla ba Dan yasha alwashin koya Mata hankali.
Tace wai me nayi maka ne kawai murmushi yayi Mata yace .......

......

A gidan sabir da bushra ba laifi ana Dan zaman lafiya,yana Dan aikinsa saide me ya lura tunda sukayi auren bushra tayi sanyi dayawa bawai tuban bane kadai akwai matsala hakan yasa yauwa kamar kullum ya tisata a gaba yake tambayar ta matsalar ta. Da Kumar ya samu ta budi Baki zatayi magana ta "ance ana bukatar bone marrow transplant cikin gaggawa da a lissafi na yanzu kwana 20 yayi min saura."

TO WAI SHIN ME SAHIR ZAICE MA ZAYYA ?

KUNASON KABIR KUWA?

YAYA ZA'A KAYA DA JINYAR BUSHRA ? ZATA MUTU KO ZATA RAYU ?

Takuce KARAMARSU BABBARSU,  Jared Ku manta da VOTE, follow And  comment .

Miss untichlobanty 💕

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now