CHAPTER 88

2K 163 86
                                    

RECAP

Washe gari tana shigowa floor dinsu taci karo dasu yazeed secretary dinshi ne yace ms mina da alamu hiran jiya yayi dadi tunda birthday din saurayin ki ne. Kwal....datseshi tayi ta hanyar cewa rike zancenka, ko ganin fuskarsa banyi ba. Sannan tabi bayan yazeed tana mai murkutsa baki.

CONTINUATION

A gidan mai nasara kuwa maman su ne tare zaune suna hira da bushra take cewa bushra ya kamata kema fa ki fara aikinnan kinga yar uwar ki minal....
Bata karashe ba sanadin bata rai da minal tayi tace ba yar uwata bace.

Maman tace munji kinga dai yanzu a jeedmar take aiki ya kamata kema ki nemi aiki. Zama tayi tace mom jeedmar kikace fa. Tace eh shi mana. Tsaki taja tace dama nasan ba'a sona ya za'ayi a nema Mata aiki anan ni a hanani ? Mama tace kinaji tace uta Zata Nemo aikinta yanzu zakice an nema Mata.

Tace babu yadda za'ayi ta samu aiki saide in jikinta ta bayar. Sahla yar biyun zayya tace AI uwar mu ba irin su oo bane. Cikin mamaki dukansu biyu suka kalleta. Bushra ta Mike zata daketa tana fadin keda ko usili bakuda shi sahla tace kina duka na zan fada ma daddy duk abinda kika ce akan ummi na, wallahi karkiganni shiru shiru banda kyau Dan haka bazan juri zagin uwata ba daganan ta shige daki.

Sallama aunty jalila tayi shameela na biye da ita. Tace yar karamar kanwata lafiya kike haki haka. Mama ne tace ma shameela taje wajen feena a daki zasuyi magana da mamanta. Amma kun Santa da gulma Dan haka labewa tayi.

Sahla ce ta bude kofa ta hangota Dan haka ta Nemo zare a hankali tasa Mata a jiki. Ihu ta kwalla kowa ya fashe da dariya ashe suna sane da ita.

Aunty jalila tace mummy ga me aikina fa shekarar 5 muna tare sai yau kuka hadu. Sai a lokacin umma ta lura da kyakkyawar matar dake tsaye a baya tana kalle kalle yayinda take zubda kwalla. Mama tace baiwar Allah shigo mana lafiya kike kuka? Zauna anan gefena.

Zama matar tayi suka gaisa umma tace lafiya dai ko? Matar tace kawai gidanku ya tunamin ra rayuwata ne. Nann ta labarta musu rayuwar ta amma ta kasa fadan family name dinta. Yin duniya akayi ta kasa fada ko ymta kwatanta inda za'a samesu.  Matar nan ba kowa bace illa MOM mahaifiyar yazeed. Security dinnan ce ta taimaka Mata ta fitar da ita daga gidan mahaukata.

🌹🍀🌹🍀

Ya Abubakar zaune da matar sa laila  da yaransu guda biyu a parlourn su inna sun kawo musu ziyara.
Tunda dama ta rasa kowa nata tun kamin su mance komai yanzu a nasu tunanin ita Marai niyace gaba da baya domin ko sun mance da wani Dan uwanta goje Wanda ya kasance miji ga ayush idan Baku manta ba.

...........

Direct company ya nufa wajen baban sa ya samu minal da yazeed da secretary sunata aiki. Shigowa yayi babu knocking suna hada ido da minal yaji kamar akwai alaka mai karfi a tsanin su. Baisan yadda akayi ya gaishe ta ba.

Yazeed yace kai secretary taba min goshin sa ko bayida lafiya ne? Dariya yayi yace lafiya nake. Secretary tace ms minal wannan shine sahir, future president wato babban Dan yazeed.  Murmushi tayi masa tace nayi farin cikin ganinka zama yayi a gefenta yace na fiki farin cikin ganinki. Yazeed yace kai banson shirme tayi kama da sa'ar la ne. Wato dama abinda ake fada min gaskiya ne ? Muje. Sahir yace ina zamu? Yazeed yace gidan ka.

Wani kulululu yaji a cikin sa, take yayi kokarin kawar da maganan amma yazeed yace Sam kallon minal yayi yace muje ko? Sahir kuwa Message ya turawa zayya akan ko bata gama ba tabar gidan,Amma me rana can tana shirme.

A cikin mota sahir ya matso jikin yazeed cikin kunne yace daddy dama PA dinka ce matar ka. Yace me kakeso kace ? banason kwane kwane. Yace dadi na dakai saurin gano ni so nake ka AURETA. Mangare shi kadan yazeed yayi Yace hmm yaro man kaza kaida kakeda mummy safina me zakayi da sabuwar mahaifiya? Kaga dai safina.. hannu sahir ya daga masa yace bana bukatar ji. Dariya yazeed yayi yace wai me yasa bakason safina ne? Duk maganar nan da suke minal bataji.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now