CHAPTER 97

1.8K 112 41
                                    

RECAP

Anyi jungum jungum a parlour kowa na kallon kowa, zayya de magana daya ke ci Mata tuwo a kwarya,  ganin kamar basu damu ba yasa ta gyara zama. Parlourn yayi tsit Dan haka tayi gyaran murya tare da turo baki tace gaskiya ina magana. Wai ya naga kowa yaki ya fadamin sirrin ne? Abinda ya fito na gaba a bakinta ne yasa kowa yasha jinin jikinsa.

YA SAHIR GASKIYA FA DOLE NIMA KAYI MIN CIKINNAN EHE!

CONTINUATION

Bata rai yazeed yayi dukda bece komai ba yayin da minal ta dage goshi domin shirme zayya ya fara fita Mata akai. Zaliha ne ta e ke tashi ki bawa mutane waje bamason rashin kunya. Kallon sahir tayi ya kawo agaji amma baice Mata komai ba sai harara daya falla Mata yabar dakin. Tashi tayi a kufule tana bubbuga kafa da yarfa hannu ta tafi dakinta ta fada kan gado kuma ta sake tana fadin to ni me nayi ? Daga cewa inason na haihu shine ya zama rashin kunya? Kowa bayason ya taimaka mini? Toh AI in kunsan wata bakusan wata ba.

Wayarta ta janyo ta rambatsa ma halsey Kira dukda ko tana jin haushin katin ta da zai kare Dan international call kati yake sha kamar me.... ringing wayar ya fara yayinda take gunagunin gara ta Kira halsey Dan yeonsil sai tayi ta tsokanarta kuma bata wani bata shawara arziki ba. Dauka halsey tayi tare da fasa ihu tace besty har nayi missing dinki, nina kings yanzu na iso kasarmu wai shin kinyi magana da yeonsil kuwa? Me yas......

Zayya ne ta datseta ta hanyar cewa ni duk ba wannan yasa na kiraki ba taimako ko ince shawara nake nema. Gyara tsayuwa halsey tayi Dan a airport ma take tace toooo ina jinki.

Muryan abin tausayi zayya rasa tace kinga ni ina dawowa gida kawai sai na tarar yan biyu na tana da ciki.... halsey tace toooo? Kukam hausawa haihuwar wuri gareki daga aure? AI aurennan ma yayi wuri mukam kinga........
Zayya tace zaki saurara ko surutu zaki min? Halsey tace toh ina jin ki.... zayya tace toh nima fa so nake na haihu... halsey tace mene? Kee zayya yar yarinya dake kice zaki haihu shekararki sha shida ne fa idan kika fara Yoon fitsari fa? Zayya tace wai ke bakisan zamanin da suma daidai irin shekarunnan suke haihuwa ba? Wasu ma basu kai ba sun mutu ne? Kuma da mutum be kai ya haihu ba ai bazai dau cikin ba nide yanzu shawara nakeson ki bani a garin ya ake samun ciki? Ajiyan zuciya halsey ta sauke tace toh mude a garin mu abinda na sani shine idan mutum yana neman haihuwa bai samu toh sai yaje wajen baita yayi sadaka sannan ya sanar a tayasa addu'a.

Zayya tace toh toh toh na gane... halsey tace ko kuma... zayya tace a ah ya haka ? Kina fatan kar wannan hanyan ta bulle ne da Zaki bani wata? Ki bari na gwada wannan mana. Kashe wayar na tayi tsabar kaguwa bata jira taji sauran zancen ba. Kiran kawarta na tsohuwar makarantar kamin ayi Mata transfer da shike kawar a kano suke.

Tana dauka race Mata ta turo Mata da account number zata tura Mata kudin da za'a ciyar da mutane 20 na kwana uku Allah ya cika Mata burinta.

Kawar Ta ta me suna fati tace ke ko menene wannan buri naki kuma ni ince wa iyayena me? Zayya tace haba fati AI kin fini dabara zakisan abinda zaki fada musu. Kinga kudin da mikewa shi a hannu kenan zan turo miki Dan Allah kiyi min taimakon nan. Fati tace toh shikenan ai. Sannan sukayi sallama.

Shiryawa tayi ta fito har lokacin su minal suna zaune a parlour amma kabir yayi bacci an kaisa daki. Sim sim ta wuce ta dauka basu ganta ba . Ba tare da sun kalleta ba yazeed yace hajiya ina zuwa? Ji tayi kamar ta fashe da kuka Dan bataso sun lura da ita ba. Tsarewa tayi zata fice minal tace kina kara taku daya zan karye miki kafa.

Kukan shagwaba ta fara kamin ta koma dakinta ta fada gado tana kuka. Sahir ne ya shigo fuskar sa a tamke. Rigarsa ya cire ya dale gado baice Mata komai ba. Jin alamun kamar an shigo dakin yasa ta dago kallonsa tayi taga ya kwata ba tare da ya Mata magana ba. Kwafa tayi tace wato kai baka damu ba ma baccin yamma zakayi bayan ni ina nan ina fafatawar yadda zan haihu......

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now