CHAPTER 92

1.9K 152 28
                                    

RECAP

Yana fita yayi dariya yace yan Matana aci chewing gum lafiya yana Mata dariyar mugunta. Itama a bangaren ta yana ficewa tace sai kace ban sanka ba kawai zan yarda cewa ka hakura. Hmm nasan so kake kabi dare ka cinye dan haka gadi zanyi sannan tayi ma kofar gwaliyo.

CONTINUATION

A asibiti kuwa ayush tasha plasta a mazaunai sannan kar ta dinga zama saide kwanciya ko tsayuwa. Tafiyar ma gwale gwale takeyi Kamar yar kaciya. Wayarta ta dauko taga missed call aciki harda na Dan iskan mijinta wai ya dawo daga Mali. Tun shekaru biyar da suka wuce ya tattari tarukucensa ya tafi neman Mata ta da harkar gabansa da sunan kasuwan ci saida ya kwaso kanjamau tukunna ya lallabo ya dawo.

Bayan sun kammala wayar ne taga cewa wata number ta Mata missed call Kira tayi bugu biyu aka dauka tare da fadin barka da war haka hajiya ayush ashe de baki canja lamba ba.

Ayush ne tace wai wa ke magana? Dariya akayi ta dayan bangaren tace hehehe su ayush manya shekaru nawa ne har kin manta da SUMAYYA? Ayush tace wace sumaiya kuma? Tace summy de guda da kika sani yar lesbian yanzu kuwa magajiya ce.

Dafe goshi ayush tayi a ranta tace mutum na fama da wata matsalar sai wata ta kunno kai. Daidai lokacin mamata ta turo kofa ta shigo dakin da take hakan yasa ta dawo daga tunanin da ta shiga tace toh summy kike ko wa ya akayi? Summy tace ya akayi? Lokacin da na yi miki aiki ba cewa kikayi idan kin samu dani za'a raba ba? Jini shiru yasa na share na bar kasona tare da ke a matsayin ajiya yanzu ko fatara nake babu kasuwa sosai Dan haka so Nike ki bani. Ayush tace turo account number ki. Summy tace ance miki cikin sauki zan karba na wuce AI wallahi gidan da kike nan zan zauna kima San yadda zakiyi ki shigar dani ayush ta kunduma ashar tace bara in kashe wayar muga tsiya. Summy tace wallahi ko bakar magana kika kara yi min wallahi sai na zo na miki tone tone.

Iska ayush ta fesar tace naji zanga yadda zanyi sannan ta kashe wayar baki daya.
Mummy tace waye ne? Ayush tace waye kuwa banda wancan yar iskar wai ita summy. Mummy tace wacece kuma summy? Tace wannan yar iskar de wacce tayi min aiki akan zakiyya tayi kokarin kwanciya da ita. Tattaunawa sula ci gaba da yi na yadda zasu tsere daga tarkon summy.

Da daddare zayya tana kwance ta rufe Rabin jikinta da bargo taji sahir ya shigo, likimo tayi tana kallonsa yaje wajen Jakarta kamin ya dawo ya kwanta. Bayan minti biyar ta tashi da sauri ta duba chewing gum dinta yananan wani paper ta gani Wanda batasan dashi ba ta dauka. Muryarsa ta jiyo yace finally zan rabu da alakakai dama Dan daddy yayi aure na aureki badan raina yaso ba. Gabanta ne ya fadi hannu na ruwa idonta ya ciko da kwalla tace sakina kayi? Yace duba ki gani ko guda nawa ne sannan yayi kwanciyarsa  ko a jikinsa.

Kafarta na rawa ta dosana mazaunanta akan gado ta bude paper ido shame Shame da hawaye ta karanta kamar haka.

"Zayya manyan Mata gara ma ki tashi Dan nasan ba bacci kikeyi ba fadin cingam kikeyi. Karki dauka Dan na aureki contract din mu ya kare dole ki karashe. Dan haka so nake yanzu ki hadomin shayi."

Tana gama karantawa tayi kicin kicin da ido duka ta kawo masa ya kauce yana dariya ta ƙwale hannunta. Kafa tasa ta turesa daga kan gadon ya fadi fatt a kasa tace idan na ganja a gadon nan sai na cire ma idanu kuma bazan hado shayin ba. Kwanciya tayi a tsakiyar gadon ta juya masa baya. Murmushi me sauti yayi yace idan nan da minti biyar ya cika banga shayi na ba kinsan student ID card dinki yana gurina? Kaiwa zanyi lost and found na makarantar ku ince a club din hotel na samu kamin ya karashe maganar har ta isa bakin kofa. Yatsar tsakiyar hannu ta nuna masa wato alamar f*ck you sannan ta fita tana shiga kicin ta samu sahla da safwan a bakin fridge suna lobewa tsaki taja tace dalla malamai ku tafi dakinku.  Saa ne tace sis Allah ya isa kin kalle min kirji zayya tace dadin abun shekara daya da ya wuce ma tare muke wanka dukda an hanamu sannan taci gaba da harkar gabanta.

Washe gari Monday wato litinin aka sallamo ayush. Koda ta dawo su zayya sun tafi makaranta. Direct dakinta ta wuce amma me tana shiga ta fara jin kukan jarirai hakan yasa babu shiri kafa a faffale kamar baba ari Dan wasan hausa ta fito da gudu ta koma mota tace summy tuka muje wajen mugu, maza kaini wajen boka mugu  Dan wallahi akwai matsala ya taimaka min dama na Dade banji daga gareshi ba.

Bayan tafiyar awa biyu suka iso lokacin ayush tayi lubus Dan ba zama sai kwanciya a karkace shima. Taimaka Mata summy tayi suka shiga ta baya baya suna gafaran ku dai subhanallah sukaji ana fadi ayush toh kuji wata sabuwa ko batan kai mukayi bokan yana ganinta ya ganeta yace aishatu dakata daganan idan har kinsan da mummunar Niya kikazo Dan ni Allah ya shirye ni. Ayush tace taimaka boka taimaka...... datseta yayi yace ke ni ba boka bane ni yanzu gardi ne na makarantar allo....

Datseshi tayi ta hanyar cewa ni mugu duk wannan zance da kake yaushe ma nakeda imani balle na kama sunnar na bar bidi'a? Yace ke ba sunana mugu ba Salmanu nake atakaice ni me sunan salmanul farisiy ne. Tace toh koma wa kake ba salmanu ba nide taimaka wallahi kukan jarirai nakeji a daki na yace AI saima kin fara ganinsu AI duk Wanda muka yanka ne nima nan da kike ganina ina fara jin su na tuba Dan na gano an Sami matsala kiyi gaggawar tuba wata kila Allah yasa kiji kamshin rahama koda baki ganta ba. Kuka ta fara tace kash ba wani taimakawa da kake sai rura wutar ke sumaiya muje. Mikewa sukayi suka fita tana nazarin inda zata Sami sabon boka.

Koda suka dawo sumaiya tace toh ko wani aiki nayi miki za'a kara da kudin sa fa ayush tace ba matsala. Tana shiga ya leka dakin amma har yanzu kukan jarirai take ji haka ta kankame hannun summy har tayi bacci. Summy ne ta Sami mummy ta fada Mata abin da ya faru.

Cikin mamaki mummy taje dakin tana kalle kalle amma bataji komai ba tace ka bibiya kalle kallen film ya janyo Dan gobe sai tace taga kurwa.

Yazeed kam cewa yayi bazashi aiki ba yana makale a gurin minal yayi ma Jamal waya cewa a nemi gurbi a bawa sabir me gadi aiki sannan ya kashe wayarsa cikin hakane sukaji hayaniya ta bayan Window dinsu ta kasa lekawa sukayi suka ga ayush ne da wata amma da alamu ayush a firgice take. Minal har tana Tuntube ta kunna CCTV footage din suka kalli komai.

Minal tace na Sami idea! Yazeed yace na me fa? Tace tunda dai bisa alamu aljanune suke bibiyarta dole zasu hanata bacci da daddare da rana kuma sai mudinga yi Mata kurwa tunda kaji dai abinda mahaifiyar ta tace kaga sun yarda akwai kurwa kenan. Kaga kawai kowa kallon tabbabiya zai dinga Mata daga nan zamu San abinyi.

DON'T FORGET TO VOTE,COMMENT AND SHARE.

LOVE YOU ALL!

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

Miss untichlobanty 💕

1st MAY, 2020

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now