CHAPTER 29

2.6K 213 3
                                    

Bai tsaya yin wata wata Ba ya koma cikin dakinshi direct laptop dinshi ya dauko ya haye gadonsa sannan ya kunna CCTV dinsa domin rabonsa da ya Duba meke wakana acikin gidansa run shekaranjiya domin baya bukatar cin karo da kayan bakin cikin da baki ke aikatawa

Koda ya kunna forwarding yayi har izuwa na jiya tukunna ya tsaya
tundaga jiya da yamma ya fara kalla har izuwa Inda aka kawo minal zaliha ya hango tana rawar kai,tsaki yaja cikin ransa yace dubi wata me bakin fiska sai shegen rawan kai.

Kalla ya cigaba dayi har izuwa sanda mom ta kawoshi wani tsakin yaja tare da yatsine fiska sannan yadan kamo gefen lip dinsa na kasa yana tsotsa saboda takaici forwarding yayi har izuwa yau da safe

Bangaren masu aiki ya kalla yaga suna ta zirga zirgan su once In a while tunda asuba ne yawanci ma alwala Duke kamin sukayi wanka na minal ya Duba yaga ta tashi tana tafiya ahankali Kamar kazan da kwai ya fashewa take tafiya domin baccin bai isheta Ba .

Cikin nutsuwa yaga ta Shiga sanda ta Dade bata fito Ba ran yazeed ne ya kara back a hanklai yace shegiya kome takeyi aciki haka oho...
Can saiga minal tafito tayi sallh ta fita
Duba parlour yayi yaga banan yaje Ba Dan haka ya Duba na kitchen aiko anan yaganta tana neme neme
Tsaki ya kara ja yana mai cizan lebensa na kasa,can yaga tayi murmushi ta dauki tsintsiya ta fita abinta. kwafa yayi wato ma aikin dadi yaje mata tasaba kenan Ba irin zakiyya bace.

Zuciyarsa ce tace masa yo kai what do you expect from a low class human being like her.
Girgiza kai kawai yayi irin zai San abinyi.
Ganin shiru bata dawoba yasa yasan Cewa ta fara aikin Dan haka bai bata lokaci Ba ya canja izuwa na dakin uwar gida sarautar mata.

Yawwnci Ba Komai bane sai yadda take kuka lokaci zuwa lokaci da yanda su sahir ke sha'aninsu hankali kwance illa in sunga tana kuka su tambayeta matsalarta in tace  babu sai su goge mata hawaye suna masu jin tausayinta hardai izuwa jiya da akakai minal wajenta da kuma sanda yazo dakin da yadda su kayi fada har yau da safe.

Da wuri yaga ta tashi Wanda hakan yabashi mamaki matuka Dan shidai yasan Ba sallah take akan lokaci Ba yayi magana,yayi fada,yayi fishi har ya hakura amma yau ta tashi da asuba Alhamdulillah shiryuwa ya samu matarsa ta fara gyarawa.
To his disappointment wanka tayi ta Shirya tsaf shirinta na zuwa office Kamar yadda ta saba wani ras yaji a kirjinsa,bakin ciki yayi masa kaluluwa a zuciya,wato ba'a yaban Dan kuturu saiya shekara da yatsu. Ganin ta dauki jakanta DIOR yasan Cewa ta tafi hakan yasa ya koma kitchen yayi playing Daga Inda ya tsaya sannan ya fara forwarding a hankali can yaga su atine sun Shiga Suna hayaniya ba'ajin me suke Cewa saboda yadda muryansu ya kacame Kamar gidan Suna

Parlour yaga sun nufa Dan haka yayi pausing yaje yayi playing na parlour ya fara forwarding aiko atake yayi playing yana mai kara hade fiskaganin abinda ya tsana ta fito tana tafiyar nan nata Wanda ke kara bata masa rai saboda yadda zuciyarsa ke bugawa aduk lokacin daya gani

Shara yaga ta fara tana aikinta cikin nutsuwa da kwarewa,shi kansa idan yace batada kyau yasan San zuciyane kawai amma ai she is not his type worse of all she is a gold digger. Mtswww wani wawan tsaki ya kara ja sannan taci gaba da kalla su binta yagani sun shigo nan yaga sun fara yiwa minal murmushi Suna magana tare kokarin karban aikin duk yadda yayi kokarin jin me suke Cewa ya kasa saboda yadda suke maganar kaman marasa Gaskiya can yaga sun kara hanyar kitchen hakan yasa yayi pausing tare da komawa na kitchen yayi playing aiko gaji yayi sun Shiga kafin suka fara aikin tare sunata hira minal nata musu murmushi

Aransa yace lallai yarinyannan wato ta rainani ko?wato har wani nasu aikin da nasata take kuma har tana murmushi lallai rayuwa batayi mata kunci Ba tukunna kwafa ya kuma yi yana kara gyara kwanciyarsa tare da janyo laptop dinnasa sosai sannan ya kashe Dan takaici ya masa yawa. Ruf da cikin yayi yana mai lumshe rikitattun idanunsa tare da sauke ajiyar zuciya.

Bayan yayi sallar la'asar ya dawo gida tundaga mai kofan parlour yajiyo kamshin abinci wani kurrr cikinsa ya bada sauti aiko yana dago Kansa karaf ya hango minal tana saukowa Daga stair case sanye take da black short bun da white t shirt sai dogon hijabi mai hannun Dan haka baya iya hango abinda ke jikinta.

He was expecting her takoma da gudu Dan ta buya amma to his surprise yaga tana pretending Kamar bata ganshi Ba

Itako minal kokari take ta Koma kitchen domin Duba abincinta,Dan haka da Dan sassarfa take saukowa,wani Abu yaji ya tokare masa numfashi saboda bakin ciki taga alamun yarinyarnan zata kawo masa rainin sense,Dan haka shima da sauri ya fara yawa aiko minal bata ankare Ba taji tayi karo da gini amma abinda ya bata mamanki shine irin kamshin da gadon yazeed keyi irinshi taji ya bigi hancinta

Taga taga tayi Kamar zata dadi yazeed yayi sauri rikota aiko tsayuwarta na daidai tuwa taji tassss! Ya dauketa da mari wutanta ne ya dauke na Dan wani lokaci.
Yazeed ko baice komaiba kawai sama yayi abinsa ya nufi side dinsa hankali kwance Kamar Ba shi ya kaftawa har mutane mari Ba.
Minal Kam sanda ta daskare awurin for almost five min kafin hawaye ya tsiranyo a idanunta

Ahankli take Daga kafafunta har ta isa zuwa kitchen ta samu har atine ta kashe mata Dan haka kawai tace wa atinen su dibi nasu domin dama yam porridge tayi
Aiko atine tace to aunty Amarya sannan ta diba musu Dana securities din da'ake bawa abinci guntun ta juye a flask takai dakin minal da sallama ta Shiga amma bataga kowa Ba Dan haka ta ajiye kawai ta fice abunta zuciyarta kal yawunta har tsinkewa yaje tana Allah Allah taci abincin minal Dan bazata manta sanda taci tuwo Ba.

Minal ko tana dawowa daki toilet ta fada tabaje akasa sai kuka
Jin alamun antaba kofar dakinta yasa ta sassauta murya

Tanajin anfita ta kara bude makokoro ta sha kukanta Kamar umarni Daga Allah.

Da daddare.......

Show some love by voting and commenting.

Sauri nake so bye, love you all😘

Miss untichlobanty💕

9th October,2019.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now