CHAPTER 58

3.1K 256 26
                                    

Saukowa minal tayi cikin navy blue Arabian gown. Murmushi take sakewa yazeed harta iso Inda yake zaune ta tsuguna tareda fadin sannu da zuwa sannan ta dauki office bag dinshi zata juya tana fadin zo muje kasha ruwa ka Shirya ko bak.....? bata karasa Ba yazeed ya finciko ta ta fado jikinsa turo baki tayi tareda fadin kaga ka batamin kwalliyata ko?dariya yadanyi tareda Cewa ina kwalliyar Anan ji yadda kika lafta man baki.

Tace kana nufin banyi kyau Ba?yace wa ni na isa?irin wannan kyau dakikayi ai ko Amarya kawai dai kin tunamin da ranan dana fara ganinki. Turo baki tayi tace shine kukayita min dariya ko? Shafa bayanta yazeed ya fara tareda fadin Kiyi hakuri baby na lokacin ai bansanki Ba.

Kuka ta fara bilhakki da Gaskiya harda shessheka tace shine kuma....kuma ranan da na Shiga motarka...ka..kaci zalina a gidannan har ciwo kaji min. Serious face yasa tare da gyara zama mai kyau sannan itama ya gyarata sosai akan cinyarsa murya kasa kasa abin tausayi Kamar wani maraya yace Kiyi hakuri MINAL dina kinsan kuskure ne da Bacin rai sannan kuma da rashin sani amma Nayi miki alkawari Indai ina cikin haiyaci bazan kara cin zarafinki Ba tace kuma har lebena ka dalle Mun😭 yace na tuba please tareda hada hannaye. Hannun Nasa ta riko tare da turo baki da alamu zata fara shagwaba ne tace to na yafe maka amma da sharadi.

Zaro ido yayi yace yafiyan ma sai an kara min sharadi?yace toh ko bakaso a yafe ne? Yace a ah Ba haka nake nufi Ba inajin wannan sharadin.
Janyo kunnansa tayi tace tashimuje daki ka Shirya sai.......

Yace ehm sai me?gyaggyara tayi ta kwala masa ihun SAI MUJE KACI SINASIR! Sannan ta diba a guje Yazeed har wani zuuut yaji a kunnansa tashi yayi hannunsa daya kan kunnansa yana fadin yau kin Shiga uku a hannuna.

Dakin ya bita ya samu tana hada masa ruwan wanka.
Ban dakin ya Shiga bayan ya ajiye jakankasa aiko tana ganinsa ta bude baki zata kwalla ihu ya hade bakinsu.
Mukut! Ta hadiye ihunta tare dayin lamoo a jikinsa. Murmushi yayi aiko ya fara mata cakulkuli. Dariya take kyalkyalawa tana bashi hakuri shima sai dariya yake mata yana fadin zaki kara min ihu a kunne?tana dariya harda hawaye take fadin ban karawa waiyo Allah cikina,kayi hakuri bazan kara Ba.

Garin shure shure ta bige makunnin shower nan ruwa ya musu sharkaf.
Dakyar yazeed ya lalumo ya kashe saboda karfin ruwan guduwa zatayi ya janyota jikinsa tareda fadin ai baki isa ki shigar min daki a haka Ba. Tace to kaima a jike kake ai yace dama ni wanka zanyi kinga sai mutu tare ko😉?
Girgiza kai tayi tace a ah fa ni iskanci na baikai nan Ba. Yazeed yace hmmm to ai sai ki jira inyi wankan in dauko miki kaya ta Daga kai alamun Toh.

Hannu yasa a ruwan tunda bata tana hada masa Ba yasanyi.

Kallonta yayi yace irin wannan sanyin ruwa haka. Tace to ai ni banga famfon ruwan zafin bane kuma famfo kawai na iya budewa ban iya aiki da sauran abubuwannan ba. Yace zo kigani Toh. Matsowa tayi nan ya gwada mata suka controls din jacuzzi din tare da aiyukansu sannan yace ga Inda zaki dinga ganin temperature din ruwan kuma ni ina wanka a 40°C. Gyara kai tayi yace good yanzu kunna Inda zai dumama ruwanda kika zuba Daga famfo.

Kunnawa tayi tana monitoring temperature din ruwan yana zuwa 40°c ta kashe yace give me five suka tafa yace my baby minal Ashe kanki yanaja. Tace ka dauka ni din wasa ce? Yace ko kadan kayanshi ya fara cirewa minal ta juya fuskannan yayi ja saboda kunya. Murmushi kawai yayi ya Shiga Ba tareda ya rufe glass dinba.

Dan karkarwa kadan yaga tanayi yace baby minal?tace na'am yace bude drawer din can ki dauko min turaren wanka na. Toh tace taje Inda ya fada mata ta fara dauko abubuwa tana shinshina har ta sami mai kamshin turare ta dauko ta dawo Inda take dazu sannan ta miko masa.
Yace kinmin nisa ai yana smirking Dan shi yasan me ya Shirya mata. Matsowa ta sakeyi tare da mikowa aiko ya cafkota ya janyota findummm! sai acikin ruwan.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now