CHAPTER 72

3K 204 24
                                    

Kuka ta soma mai tace kai yazzy na wannan fa ba adalci bane,fuskar yara ya Mata yace sorry my love kawai inaso muyi wanka tare ne. Turo baki tayi tace ni yanzu gaka fa sanyi nakeji. Lips dinta na kasan ya kamo ya tsotsa,murmushi tayi tare da rufe fuskarta a kirjinsa. Shima murmusawa yayi tare mai sauti. Dagowa tayi ya dangwali hancinta yace wa yaga minal Dina a kasar waje. Dariya tayi tace kyau kenan.

Haka sukayi wanka suka fito suka shirya tace yazzy baby yace na'am tace  in the next 2weeks birthday Dina ne fa yace haba? Tace eh yace wow ok.

Zaliha zaune a parlour tana kallon zee world taga an mayar Mata tashan ball. Kicin tayi da ido tare da juyawa aiko kamar yadda take tsammani luku ne a tsaye a bayan kujeran da take. Murmushi yake sakar Mata da ka gani kasan na neman magana ne.

Tsaki taja tare da cewa menene haka ni ka miyar min bakaga ina kallo bane ? Shafa gemunshi yayi kamin ya jewayo ya zauna a gefenta tare da riko hannunta. Fincikewa tayi tana aika masa harara janyota yayi zai rungume ta Mike a take tana mai kallon sama da kasa tace wai me kake nufi ne? Kallonta kawai yakeyi kamin shima ya Mike matsowa ya farayi a take gabanta ya fara lugude saboda wani Abu da ta gani a idonsa. Ko wani takunsa daya tare da zuciyarta yake bugawa jin ta hadu da bango gashi kirjinta na gogan na luku yasa gumi karyo Ma ta. Hannu tasa a kirjinsa jiki babu kwari zata hankadeshi amma ta kasa. Hannunsa daya yasa ya kamo nata duka biyu tareda likawa da bango a take ta hadiyi wani yawu kutt. Gaba daya ta tsure ta rude ta kidime sai zazzare ido take numfashinsa ke sauka a fiskanta har ya hade goshinsu. Dayan hannunsa yasa ya riko fuskarta tareda fara shinshinar wuyanta. Ido ta rufe ta ruf yayinda take juya kai gefe domin bashi dama. Jin ya tsaya yasata bude ido. Kallonta yake yana kunshe dariya aiko suna hada ido ya fashe da dariya baya ya fara yi yana dariya harda kama ciki tareda nunata. Cikin dariya yace dubata kin dauka wani abin zan miki sai anyi magana ki bude bakin cakwaikwaiwa kice bakyaso na. Harara ta zabga mai kamar idonta zai fita tare da tsaki ta wuce bangan bangan ta fada daki tareda buga kofa. Kan gado ta fada ta fara chatting ko ta huce haushi ji take kamar ta kamoshi tayi masa dukan tsiya.

Bayan ya gama kallon ball dinshi ya shiga dining area babu abinci kitchen ya shiga shima yaga empty.

Knocking yayi har sau uku amma ba'a amsa ba hakan yasa ya Shiga kai tsaye kwance ya sameta tayi bacci a ruf da cikin tana chatting messages sai shigowa yake kwanciya yayi luf Akan bayanta tare da zura hannunsa ya rungume kunkuminta. Cikin bacci taji Abu me nauyi ya danneta hakan yasa ta bude ido badon taso ba Dan mafarkin sulaiman dinta take wai har sun haifi yara.

Kamshin turaren lukman da taji shi ya tabbatar Mata da cewa shine ba kowa ba. Kokari juyawa tayi amma ina linzami yafi karfin bakin kaza.

Yace my wife ina abinci na tsaki taja tace ban dafa ko kaga alamun nayi girki ne? Nifa la takuramini ehe maida bakinka kace kowa yayi rayuwarsa yanzu kuma zaka wani zo kana likemin. Wata bazawarar Dariya yayi yace hmm bakida dama nide yanzu ba fada naso nema ba so nake ki dafa mana abinci. Dariya ta sheke dashi dashi tace idan naki fa sai ayi kaka?

Yace ki ki yi din kiga ikon Allah tace toh baza'ayi ba. Zip din Riga ya fara bude Mata tace me hakan bai kulata ba ya fara  balle Ma ta bra yace ince bazakiyi ba tace waiyo kayi hakuri dan Allah zanyi wallahi zanyi yace good for you. Rufe Mata yayi ya rufe zip din kamin ya ciccibeta tana wantsal wantsal bai direta ko ina ba sai kitchen a gaban gas cooker yace fara harararsa tayi tace toh ba sai na hada kayan ba lo kanka zan dafa? Hade rai yayi yace baki daddara ba ko? Janyota yayi da karfi ta fadi jikinsa take ya fara kissing dinta a zafafe tun tanajin sugar har taga ba haza ta fara kuka. Shikam yama mance Dan kokarin bude Mata zip ya fara karan kuka data kara shi yasa ya dawo sense dinsa saketa yayi tare da goge bakinsa sannan yace na baki 10mins ki dafo min abinci ki kawomin. Da sauri ta girgiza kai yace good kamin ya fice yana murmushi itako gaba daya ta tsure da sauri ta daura indomie. Tana cikin zubawa a tukunya yace saura minti 2. Ta sake rikicewa hade hannu biyu tayi a gaban gas cooker tayi kneel down tare da cewa kayiwa Allah ka dafo na shiga uku waiyo. Lukman dake labe yana Mata video sai dariya. Itako hawaye take tana yarfa hannu tace noodles ka taimaka ka dahu kar ya dawo waiyo na shiga uku.

Koda ta kawo yace kinyi lattin minti biyu 2 rau rau tayi da ido tace kayi hakuri abincin ne bai dahu ba. Yace hmm zanyi tunani juyawa tayi zata tafi ya make mazaunanta ta jiyo tana kallonta da mamaki yace ko zaki Rama ne da sauri ta girgiza kai tana shigewa daki tace Allah ya isa na kamin ta rufe dakin da sauri Dan mugun tsoron lukman ta farayi.

Minal kuwa karatu ta koyawa yaranta kamar kullum yanzu har sun haddad izu biyar sannan sunyi Rabin hakkul Mubin su usulus Salasa ma duk sunyi nisa azkar ma haka.

Wajen zakiyya taje suka sha hira abinsu domin yanzu sun zama aminan juna. Minal tace nikam ina Jamal fa ya kuka kaya? Murmushi zakiyya tayi tace hmm ai in fada miki...........

Zakiyya zaune a office taji anyi knocking amsawa tayi tare da bada izinin shigowa ba tare da ta dauke idonta daga kan screen din system dinta ba. Zama yayi a daya daga cikin kujerun dake gabanta,kamshin turarenshi shi ya sanar da ita cewa Jamal ne ba kowa ba hakan yasa ta dago suna hada ido ta masa murmushi. Gaisawa sukayi yace ya aikin ? Tace Alhamdulillah gashinan muna fama. Mikewa tayi domin hado masa tea sai binta yake da kallo har ta gama, ahanyarta na kawowa tayi Tuntube da rug din dake shinfide a office din cup din ya fadi ya fashe ita kuma ta fada jikinshi kallon kallo suka tsaya yi kamin tayi saurin mikewa tana fadin astagfirullah am sorry. Gaba daya tama rikice rashin sanin abin yi yasa ta sa hannu ta fara dauke kwalaben amma kamin jamal ya hanata har ta yanki kanta.

Yace subhanallah tare da rike yatsan yana fadin wa yasaki ? Da kin Kira anzo an miki AI dubi kinjiwa kanji ciwo itakam bata masan yanayi ba Dan kawai   kallon yanda ya kidime take tare da yadda yake motsa bakinsa. Kai Anya baifi yazeed kyau ba kuwa( Nace a ah hajiya ta kede kawai so ya rufe miki idanu) tissue yasa Mata kamin ya tisata har company clinic dukda ko tayita magiya ai ciwon ba babba bane amma fa deep down dadi takeji kamar ta mutu.

Dariya minal ta sheke dashi tace kina wuta mutuniyata kamin suka tafa minal tace ni fa na matsu ayi aurenku fa. Zakiyya tace ke😳! Rufamin asiri nace miki muna soyayya ne? Dariya minal tayi tace saima kin fada toh wallahi ko fans din KURUCIYAR MINAL aka tambaya sunsan cewa kina sonshi. Fans ko karya nayi?

TOH ANAN ZAN DASA AYA MASOYA SAI KU AMSAWA MINAL TAMBAYARTA.

ME ZAKU IYA CEWA GAME DA LAMARIN ZALIHA DA LUKMAN?

YA LABARIN AUREN SU YA ABUBAKAR ? KU BIYONI A SANNU TARE DA COMMENTING DOMIN SAMUN AMSOSHIN TAMBAYARKU. 

WANNAN PAGE SADAUKARWA NE GA NAMECY ALLAH YABAR KAUNA.

KARKU MANTA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

miss Untichlobanty 💕

2nd February, 2020

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now