CHAPTER 67

3.1K 225 31
                                    

Ajiyar zuciya dukansu suka sauke ganin ba wani serious Abu bane, glass ne ya fashe

Can bakin kofa kuwa zaliha ce tsaye ido a waje saide su basa ganinta saboda kofar ba a wangale take ba kadan ta bude zata shigo kamin tayi arangama da abin mamaki takowa minal tayi ta karaso wurinta.

Mutsittsika ido zaliha tayi minal tace ke lafiyar ki? Yawu ta hadiye tace don Allah tasheni minal, tasheni yadda kika saba tashina Idan ina baccin la'asar Baccin asara.

Dakarkarewa minal tayi ta yarfa mata tafi a gadon baya. Botsarewa tayi tace kai kede wallahi hannun ki a haka laushi amma a jikin mutum yanda kasan gaskami. Wai Dan Allah da gaske zakiyya ce ta rungumeki. Murmushi minal tayi tace gashi ko kin gani.

Jinjina kai zaliha tayi tace Allah mai iko me yin yadda yaso.
Zakiyya ce ta tako har wajen su tace me ake ci babu ni? A ah minal kice Amarya ya ce a tafe.

Mika mata Hannu zakiyyan tayi tace Assalamu alaiki.
Zaliha tace waiye huhu kai jama'a.
Dagaske gaisawa zaki yi dani zakiyya? Murmushi tayi tare da rungumeta tace hug din ma yafi.

Tsurewa zaliha tayi ta kalli minal tace ke Dan ub*nki yi min bayanin abinda ke faruwa ban gane ba. Me kika mata? Karkice min wani abin ya sami kwakwalwarta.

Dariya zakiyya tayi tace ba abinda ya sameni Allah ne kawai ya nunamin Gaskiya Kiyi hakuri da zagin launin fatarki da takeyi duk lokacin da muka hadu. Girgiza kai zaliha tayi cikin rashin gaskata abinda ke faruwa tace ba Komai ya wuce ai.

Hawaye ne ya zubowa zakiyya tace ina ma ace Inada zuciya irin taku wacce takeda girma kuma ashirye take ta yafewa kowa.

Murmushi minal tayi tace ai zaki iya kawai danne zuciyar zaki yi sannan ki tursasata kuma kinsan shi hakuri jigo ne na rayuwa,gishirin zaman duniya ne Idan babu shi Toh rayuwarka da lami. Sannan kome ya faru da mutum ya daukeshi a matsayin kaddara mai kyau ko Mara kyau.

Jinjina kai zakiyya tayi tace kuma ai inna laha ma'assabirin.

Shigowa ciki su kayi dukansu, suka bags da hira yayinda su sahir suka tafi playing room da aka basu.

Can minal tace kash! Ni har na manta Ashe mom tace naje ta bani tsarabata. A take zuciyar zakiyya ta dunkule, fuskarta ya canja zafi takeji saboda tayi wasa da damarta minal ta kanannade komai amma sai tayi Saurin dannewa Dan tanason ta kyautatawa minal KAMIN SU RABU.

Bayan minal ta haura sama suka cigaba da hiransu saide zaliha ta lura Kamar wani Abu na damunta sai ta share Dan batason ta banbarowa kanta Dan har yanzu bata gama yadda zakiyya ta canja ba. Koda ta isa mom tace my daughter sai yanzu Daga kai minal tayi tare da yin yake. Mom tace ya na ganki haka Kamar wani Abu na damunki, so zauna kinji ?

Zama minal tayi mom tace ina jinki minal tace mom a Gaskiya aunty zakiyya ta canja sosai kuma ni shedace sannan Nasan tayi nadama kuma abinda ta aikata yana damunta mom why not ki kirata mu raba kayannan tare Dan na lura sanda nave kina ne mana zamu raba kaya yanayinta gaba daya ya canja idonta ya ciko da kwalla wallahi tausayi take baniii😭😭 kawai sai minal ta Barke da kuka

Mom kam a zuciyarta tunani take anya zakiyya ba wata manufa bace da ita ? Dubi yadda tasa yar mutane ta damu a kanta Allah dai yasa da gaske ne.

A fili kuwa Cewa tayi haba aminatu manya mata miye abin kuka share hawayenki ki kirata. Da gudu minal ta fita ta kirata sai Washe baki take. Mom kam mamaki take Wai bata kishi ne? Lallai yazeed yana fama.

Zakiyya najin minal tace mom tace tazo taji wani dadi a ranta atake ta tashi cikin farin cikin suka hau sama akabar zaliha da jimami kamin ta bisu sama bayan tasa tala ta share glasses din daya fashe dama ginger juice tayiwa mom.

Koda suka Shiga har kasa zakiyya ta tsuguna ta gaida mom. Amsawa tayi tana kara mamaki da gaskata maganar minal Dan tun jiya zakiyya ta nemi afuwarta amma bata yadda ta tuba ba sai yanzu Dan da ace wani abin takeda shi a zuciya girman kanta bazai bari ta tayi abinda takeyi yanzu ba.

Amsawa tayi tare da Cewa zoki zauna a gefena mana daughter. Rarraba kayan suka farayi kamin zaliha ma ta Shigo ta jonasu bayan ta gaida mom.

Sari biyar ne sai normal Indian attire 12 ta bawa zaliha sari daya da set 2 sannan ta raba sauran ma zakiyya da minal.

Daki suka koma minal ta fara koyawa zakiyya girki kuma ta mYarda hankali sosai tana kota dukda ba'a rasa kusa kurai ba. Daidai lokacin su yazeed suka dawo a tare minal da zakiyya suka rungumeshi suna. Mai sannu da zuwa sandarewa yayi na Dan wani lokaci saboda bakon lamarin daya gani cikin gidansa.

Yau inada ta'alim yanzu haka a boye nake typing sorry ba yawa amma I promise to make it up to you gobe Insha Allah.

SADAUKARWA CE GA MASOYA BAKI DAYA ALLAH YA BARMU TARE TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

Miss Untichlobanty 💕

20th January,2020.

KURUCIYAR MINALOnde as histórias ganham vida. Descobre agora