CHAPTER 28

2.8K 198 10
                                    

Leko kanta tayi taga wani tsararren parlour wanda bata taba ganin irinsa Ba
Ko babban parlourn dake gidan taga baikai wannan kyauba dukda ko wannan din Ba wani girma bane dashi na hauka amma ya hadu

Kamshin daya bigi hancinta ne yasata dawowa saga tunanin data Shiga ga wani AC daya bugota har yanasa tsulan cikinta tashi
Shahada tayi ta Shiga da yar karamar sallamarta Wanda ko ita kanta bata jishi dakyau Ba

Sanyi ne sosai a parlourn Dan har tadan soma rawar dari a kasan ranta tace kaji daki sai kace cikin fridge Allah yaso da hijabi nazo....
Kalle kallenta tayi kamin ta soma abinda ya kawota

🌹

Yazeed kuwa tunda ya Koma bacci bashi ya tashi Ba sai around 12:00pm
A sukwane ya tashi daga kan gadon nasa ya sauka Kamar bayason jikinsa ya rabu da lallausar katifar.
Bandakinsa ya bude Wanda yake tsaf Kamar Ba namiji ke amfani dashi ba, wanka yayi kamin yafito ya shafa mai yana tunanin yadda rayuwa ta juye masa

Wai yanxu shine yake da mata biyu,Wai jiya shi aka kawowa amarya kuma ma shi Ba wannan ke damunsa Ba
Ace mom ta rasa Wanda za'a aura masa kaf fadin duniya sai wannan yarinya,wannan fitsararriyar.
Hmmm nannauyan ajiyan zuciya ya ajiye sannan ya fara shafa wani mai me kamshi ajikinsa a hankali Kamar bayason ya shafa duk da ko nazarin da yake yi ne ya haddasa hakan.
Daga mutum ya gansa yasan Cewa lallai wani Abu na damunsa dukda ko hakan bai yiwa kyawunsa wani lahani ko sauyi Ba

Ahankali ya tashi yana tafiya Kamar bayason yayi tafiyar,Ahankali ya Daga Zara zaran yatsunsa Wanda ke dake da fararen nails ya danna pin din dressing room dinshi ya Shiga sannan ya tsaya agaban wata kofa na glass a hankali ya bude sannan ya dauko wani gray hoodie tare da black three quarter.
Drawan under wears dinshi ya bude sannan ya dauko gajeran wando amma banda singlet jin Kamar motsi a part dinshi yasa ya leko
Amma baiga kowaba hakan yasa ya koma ya sanya kayansa cikin nutsuwa
A hankali yaji kamar an bude kofan dakinsa Dan haka ya kara lekowa domin ganin Waye Ba tare da dauko socks din dayayi niyya Ba.

Atake Dan guntun annuri dake tattare dashi ta dauke. Minal ya gani tana leken dakin domin tabbatar da Cewa bayanan ajiyan zuciya ta sauke tare da shigowa da Da karfin guiwanta amma Ba a rashin nutsuwa Ba.

Baice mata kala Ba itama bata lura dashi ba domin kuwa idanunta ta ware bil hakki da gaskiya tana basu abinci

Jingina yayi a bakin kofar da yake sada dakinshi da dressing room din yana kallonta kawai yama rasa mai zaice ko yayi mata

Sanda ta karewa dakin kallon tas tanata murmushi Kamar wata shashasha

A hankali ta tube hijabin dake jikinta tayi wulli dashi kan stool din dake gaban mirror Wanda tayi nadamar yin hakan domin atake wani sanyi ne ya daketa Wanda har yafi na falon hakan yasa tadan shafa jikinta

Wannan hali nata tunba yauba inna ke fama da ita na cillar da hijabi ta ko'ina Ba tare data ninke Ba acewar inna wata rana Zara wulla kan Dan aljani

A hankali ta karaso izuwa bakin gadon sannan ahankali ta janyo bargon dake kan gadon kamshin yazeed ne ya daki kofar hancinta Wanda yasata lumshe idanu tare da kara bude kofofin hanci domin ta shaki kamshi

Wani Abu taji yana mata yawo ajiki amma ta share Dan a halin yanzu bata bukatan wani distraction a ranta ko tunani take masu kudi suna sha'anin su saide ita matsalar ta da dukiya in bakayi wasa ba sai ya raba ka da mahaliccin ka.

Abangaren yazeed kuwa kallonta ma kawai yake takaici ya cika masa zuciya Kamar ya mata duka ya rasa yadda zaiyi

Wani karago ne ya tsaya masa a makokoro flinching and unflinching fist dinsa yake kawai saiya Komai cikin dressing room din nasa.

Minal ko ninke bargon tayi sannan ta ajiye badan ranta yaso Ba sai Dan kada hawan jini yazo ya tarar da ita a dakinsa (aikin gama ya gama)

Gadon ta fara gyarawa sanda ta gyara tsaf sannan ta kalli gadon taji batada burin dayawuce ta kwanta akai

Kunji mutuniyar Ku fa na dakinta ma anhanata hawa balle na oga kwatakwata

Aiko kankace me,saiga minal ta tsuguna a gefen gadon sannan ta daura fuskanta akai tanashafa gadon da hannunta mai dauke da baby fingers masu tayi da laushi Wanda suka sha lallen amarci

A hankali ta mike sannan tayi abinda ya kawota dukda Cewa dakinnasa Ba wani datti bane dashi domin yazeed dinma Ba baya bane wajen tsafta.

Tas ta gyara Komai sannan ta dibi kayan aikinta tayi gaba tare da manta hijabin nata adakinsa.

Shiko yazeed koda ya fito ya kalli Inda ta ajiye hijabin kwafa yayi dabadan dukan mace baya birgeshi Ba da babu abinda zai hanashi gyara mata zama,aiyana irin zaman dazaiyi da ita na halin ko in kula acikin gidan yake. Daga karshe ya tashi ya bude wani kofa na daban Wanda shi kuma balcony dinshi ne. 
Mika yayi tare da furzar da iska yana mai shafa lallausan sajen dake habarsa Wanda suka a kwance luf luf.

Wayansa ya zaro a aljihunsa sannan ya latso number mahaifiyarsa domin taci ace sun isa yanxu amma yaji shiru bata kirashi ba

MEET MOM

Ringing uku yayi zuwa hudu ta dauka aiko atake yazeed ya shagwabe fuska Kamar tana ganinshi

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Ringing uku yayi zuwa hudu ta dauka aiko atake yazeed ya shagwabe fuska Kamar tana ganinshi

Haba sweetheart dina ace kin isa tun yaushe amma shine  ko ki kira Babyn ki kiji yanake?

Dariya mom tayi sannan tace Allah sarki baby na ai Nasan yanxu akwai wacce zata kularmin Dakai shiyasa kaga hankalina kwance Ashe har ka tashi Daga bacci.

Kwabe fiska ya dad'a yi yace haba mommy ni tun dazu na tashi yafadi hakan yana mai tura baki Kamar mom din na kallonshi.

Mom tace ai na dauka yau sai an hada da duka tukun zaka tashi saboda angwanci

Muryan kuka yazeed yayi yace "moooooom!"

Dariya mom ta karayi yace mom yaushe zaki dawo ? Tace aini son bazan dawoba har sai mun kusa sauka. Yace what!? Tace dagaske nake fa shiyasa na Baku space ma idan Ba kawomin labarin danakeson ji Ba tofa bazan dawoba yace haba mana mummy na! Tace uhm kai yazeed ni kaga tafiyana kit yaji ta kashe wayan.

Yasan Cewa she is very serious da abinda ta fada tunda har ta kirasa da sunansa na asali amma shi the last thing he wants to do on earth shine ko hannun yarinyar nan ya tana Allah ma ya kiyaye bara kawai yaje wurin zakiyya su samawa Kansu mafita.

Allah sarki fans Nayi missing dinku. Karku manta dayin voting, sharing and commenting.

Love you all😘

Karamarsu babbarsu ce

Miss untichlobanty💕

7th October, 2019.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now