CHAPTER 76

2.6K 223 52
                                    

RECAP

Back up na 20 cars aka aiko ma yan sanda yayinda sojoji ma suka karo back up, kaucewa mutane suka fara yi Dan sunga fadan yafi karfinsu. Shugaban yansanda na lokacin ne ya zo shima sai ga shugaban sojoji ma .
Cikin isa shugaban yan sanda yazo ya danko hannun yazeed wai zai wullashi a mota minal tayi kukan kura ta raba hannun su tare da cin kwalarsa ta yarfa masa Mari 3 masu kyau. Sama yan sanda suka harba tare da saita ta da bindigogi amma ko gezau batayi ba sojoji ma suka harbi sama suka saita shugaban yan sandan sukace ana taba minal sunanshi sorry.

Huci minal keyi tare da kara matse damkar da tayi masa har yana ƙaƙarin amai , kawai wani Dan sanda mai rawan kai ya saita ta tauuuuu! Kakeji.

CONTINUATION

Shiru wajen yayi tsit kowa yana register din abinda ya faru.
Faduwa minal tayi akan guiwanta tare da rike hannunta da aka harba. AI nan kakejin dau!dau! An sakewa Dan sandan nan bullet biyu a hannu.

Nan fa shugaban nafdac ya fara hadiya yawu tare da kokarin zamewa ya gudu, wabi cacuma sojoji suka masa sukace ko ya fadi gaskiya ko yaji ba kyau. Tsilli tsilli yayi da ido Dan yaga mutuwa a gabansa. Nan fa ya fara in ina,wani soja me zafin rai me suna musa ya gwabje sa da bindiga atake ya soma bayani cewa kudi aka biyasa ya fadi hakan.
Akace wa ya biyasa yace Alhaji tukur gadon kaya ne. Nan take ya basu registration number tare da bada hakuri yazeed yace ai dole a tsigeshi nan fa ido ya Rena fata m, haka ya dinga bada hakuri yana nuna nadamar da yayi sanda yazeed ya tabbata ya wahala yace yaji ya tafi zaiyi tunani amma fa hakan batayi wa Musa dadi ba Dan haka yasa shi lungu ya dan jijjibgesa ya sauya masa halitta kamin ya barsa.

Asibiti aka kai minal da Dan sandan nan jina jina nanfa magana ta lafa, chief of police din yace a masa afuwa ba laifinsa bane na yan NAFDAC ne da sukayi musu karya kuma munafiki harda shi a ciki.

Haka dai magana ta watse aka sasanta toh anan ne mutane suka sake tada kayar baya akan a sakewa yazeed dukiyarsa.
Shugaban yan sanda yana zaune a office gadon kaya ya kirashi yace asan yadda za'ayi da mutanen nan dake zanga zanga. Nan ya Kira yan sanda 3 yace a saki teargas a wajen zanga zanga. Daya daga cikin su mai suna lieutenant sabir murya kasa kasa cikin girmamawa yace :sir! This is totally dishonest and unfair, some police are the cause of the negative views people have on us. If not for dishonesty  these people did nothing wrong, they did not temper with government property neither did they go against the law. They are just practicing a peaceful riot. To tell the truth me and my people will not participate in this (yallabai wannan fa rashin gaskiya da rashin adalci ne, wasu yan sandan su ke jawa wasu bacin suna,idan ba rashin gaskiya ba mutanen nan basu taba kayan gwamnati ba basu yi wani Abu da ya Saba doka ba, peaceful riot sukeyi Dan haka shi bazai sa yaranshi suyi ba.)

Mari chef of police din ya wankawa lieutenant sabir kuma yace yaje shi bayan kwana 3 ya dawo ya karbo dismiss letter. Yace shidai da ayi aikin rashin gaskiya dashi gara ya rasa aikinsa.

A bangaren su yazeed kuwa bayan an cirewa minal bullet din ta farfado yazeed yana bata shayi sukaji hayaniya a hall din asibiti,saukowa minal ke kokarin yi daga bed dinta yazeed ya kwantar da ita kuka ta fara masa wai tanason ta gani dan haka ya dauketa suka fito Dan sandan nanne suke cakwakiya da sojoji zasu tafi dashi Dan ya harbi matar oga yayinda yake kuka yana fadin bashi ya harbeta ba. Yazeed yace a dakata. Tsit kowa ya yi yazeed ya iso gaban shi yace :kace ba kai ka harbeta ba? Da sauri gyada kai yazeed yace idan na gano kai ka harbeta wani hukunci zan maka yace a tsire ni.

Yazeed yace a kai bullet din da aka harbeta da kuma bullet din bingigarsa a duba su shi kuma kar a tafi dashi a mayar dashi daki aci gaba da kula dashi.
Koda aka Dubo bullet din ba na bindigar sa bane nan yazeed ya fara tunanin yadda zai gano na waye tunda yan sanda ke duba wannan kuma yan sandan ba mutuwa dashi sukeyi ba.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now