1

3.6K 249 55
                                    

RAYUWA DA GIƁI

Batul Mamman💖

Bismillahir Rahmanir Rahim



In loving memory of Aisha Aminu Balbalo (mai lalurar numfashi da take sayen cylinder ɗin oxygen wadda aka fi sani da Carofee). Allah Ya jiƙanta Ya gafarta mata. Amin

***

Wanki take a tsakar gida tana sauraron hirar mahaifiyarta da ƙanwarta Zee. Ba ta saka musu baki saboda tun ainihinta ba mai son hayaniya bace. Sai murmushi kawai idan sun yi abin dariya.

"Wannan wankin naki zai sami shanya kuwa Hamdi?"

Sararin samaniyar da Yaya ta kalla ita da Zee su ka zuba wa ido. Ga dai rana ana gani tana haska ko ina. Amma idan mutum ya miƙar da ganinsa zai yi tozali da baƙin hadarin da yake ta gangami daga nesa. Tunanin taƙaita wankin ta soma yi yadda wanda ta gama za su sami wuri akan ƙofofin ɗakunan gidan su ka ji sallamar wasu mata.

Da farinciki Yaya ta tashi daga kan tabarmar da take zaune ta nufi zaure tana cangala ƙafarta ta hagu wadda shan inna (polio) ya cinye. Da alama baƙin da aka kwana aka wuni ana zancen zuwansu ne su ka ƙaraso.

"Maraba lale da Altine."

Shewar Yaya da baƙuwar su ka ji daga zauren da taje ta taro su kafin su dawo tsakar gidan hannun da baƙuwar a kafaɗarta.

"Oh ni jikar mutum huɗu. Ashe rai kan ga rai Jinjin? Ya bayan rabuwa?" Matar ta jero mata tambayoyi su na daga tsaye.

"Sai alkhairi. Rayuwar nan sai godiyar Allah." Su ka sake rungumar juna su na dariya.

Ƴan matan da baƙuwar tasu mai suna Altine ta zo dasu da kuma Hamdi da Zee sai su ka tsaya kallon abin al'ajabi. Labaran da su ke ji game da juna ashe gaskiya ne don ga zahiri sun gani. Iyayen nasu sun yi zumunci sosai kafin a haifesu lokacin suna zaman Agege a Lagos. Abubuwa da dama sun faru waɗanda su ka yi sanadiyar dawowar su Jinjin garin haihuwarsu Kano. Ƙarancin hanyoyin sadarwa da faɗi tashin yau da gobe ya dakusar da wannan zumunta ta makwabtakar gidan haya ɗaya. Shekara bakwai kenan da dawowar su Altine Kano su ma amma basu taɓa haɗuwa ba sai da Allah Ya haɗa mazansu da wani da ya san duk su biyun. A wurinsa su ka sami labari harma da lambobin wayar juna.

Altine kakkaurar mata ce mai fara'a kamar gonar auduga. Mijinta Maje mahauci ne yana sana'arsa ta fawa. Da yake kakanninsu ɗaya duk su na da billensu na gadon sana'ar a kuncinsu. Akwai ta da kazar kazar don in tana abu sai ka rantse wannan jikin ba nata bane. Da wannan yanayin nata ta ja Jinjin a jiki duk da farkon zuwanta saboda yanayin mijinta da lalurarta bata sakewa da kowa. A gidan nasu na iyali goma sha biyu ƴan ka zo na zo aka taso ta a gaba da tsokana. Don ma maigidan nata ba ƙyalle bane. Bakinsa kaɗai ya ishe su ƙwatar kai. Idan ya fita ne dai ko banɗaki ta fito zagawa an dinga dariyar tafiyarta kenan. Sai da Altine ta gama lura da ita ta gane tsoron ƴan gidan da su ke duk hausawa take yi. Sai ta zame mata baki harma da hannuwa. Don idan abin bawa hammata iska ya kama dukan tsiya take yiwa mace la'ada waje. Ɗan Altine ɗaya lokacin ita kuma Jinjin da ciki su ka rabu.

"Ina Baballe kuwa?" Cewar Yaya cikin yanayi na kewa.

Da jindaɗi Altine wadda ƴaƴanta su ke kira Iyaa (kamar yadda Yarbawa su ke jan sunan) ta bata amsa.

"Ya tafi bautar ƙasa Binuwe (Benue)"

"Allah Sarki. Shekara kwana. Yaron da na tafi na bari yana tatata"

Dariya su ka yi farinciki da jindaɗinsu ba zai kwatantu ba. Duk wannan abin da su ke yi Hamdi da babbar cikin ƴan matan Iyaa kallon gane juna su ke yi. Ganewa mai cike da tsoro da fargaba a ɓangaren kowacce bisa dalilai daban daban. Kamar iyayen sun sani kuwa su ka zaɓi wannan lokacin wurin gabatarwa juna ƴaƴan nasu.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now