16

1.5K 184 85
                                    

RAYUWA DA GIƁI  16

Batul Mamman 💖


_Ya Rabbi. Ya Zhuljalal wal Ikhram. Allah ƴaƴanmu sun koma makaranta. Ka duba mana su da dukkan abokan mu'amalarsu da sauran ƴaƴan bayinKa. Ya Allah Ka tsare su daga dukkan sharri. Ka kare su daga zamewa kowa sharri. Allah Kada a kai ƙararsu, kada su kai ƙarar wani. Ka basu ilimi mai albarka da amfani. Kasa aci moriyar abin da ake nema na boko da addini. Ya Sami'ud du'a Ka fimu sanin mawuyacin halin da ƙasarmu take ciki. Ka horewa iyaye abin da za su ciyar da iyalansu daga halali. Ka makantar damu akan haram. Duk uzurin da zai taso Ya Allahu kada Ka sa mu roƙi kowa. Ka buɗa mana. Ka albarkaci nema da samun mu. Ya Rabbi Ka kawo mana sauƙi da sassaucin rayuwa. Ka azurtamu daga taskarKa wadda bata da iyaka. Amin_


***

Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar ƙauna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki. Ya miƙe tsaye ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu.

"A duniya bayan iyayena da matata da kuma ƴan uwana da ba su guje ni ba da kuma ƙalilan cikin abokai, kai ne mutum na farko da jini bai haɗamu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata."

Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da ɗanyen aikin da Taj ya ɓallo.

"Abba..."

Kallonsa Abban ya yi yana murmushin danne ciwon dake cin zuciyarsa.

"Kada ka damu Kamal. Ba zan taɓa zama butulu gareku ba. Na san duka abin da kake gudu. In sha Allahu ni Habibu ba zan bari son zuciya yasa na zama mai ƙara nesanta uba da ɗansa ba."

Daga Taj har Kamal ba ƙaramin tausayi ya basu ba. Taj ya rufe ido ya ce,

"Abba, Alhaji ya daɗe da zare hannunsa a kaina. Auren Hamdi ba zai ..."

Kamal ya katse shi da hanzari "wallahi zai ƙara girman fushinsa a kanka. Haba Happy, ba ka tunanin su Inna ne?" Ya mayar da idanunsa ga Abba "ni zan auri Sajidan in sha Allahu. Laifin ba zai tattare akan Taj ba."

Abba jinjina zumuncin ƴan uwan yayi. Kuma bai bar zancen a cikinsa ba ya faɗa musu.

"Lallai Yaya Hayatu ya iya haihuwa. Ko shaƙiƙan da su ka fito ciki guda ba lallai su yi zumunci irin naku ba. Amma ku tafi gida, nagode. Zan bawa Sajida haƙuri. Na san za ta yi min uzuri."

"Sai dai idan ni ne baka son bawa ƴarka. Ba auren taimako zan yi ba. Allah na fi shekara ina sonta."

"Har a yaushe ka santa?" Kamal ya tambaye shi don bai yarda da zancensa ba ko kaɗan.

"Duka wannan bai taso ba. Ku je gida. Nagode"

Abba zai shige gida Ƴar Ficika ya kamo shi da sauri. Duk sun manta dashi. Kwarwar da yake da ihu ma ba sa ji saboda mahimmancin abin da su ke tattaunawa.

"Simagade....au Habibu ashe baka da hankali? Ya Allah zai kawo maka agaji a lokaci irin wannan ka nemi ka watsa mana ƙasa a ido. Ina mai tabbatar maka da cewa Sajida kai za ta ɗorawa alhakin rabata da farincikinta. Daga nan kuma bamu san halin da za ta shiga ba. Ni a tawa shawarar kawai ka bari su aure su duka."

"A'a Balarabe. Baka san komai akan yaran nan ba. Son zuciya a yanzu ita ce ƙiyayya mafi girma da zan nuna a madadin kyautatawar da su ke min."

Ƙofar gidansa ya ƙarasa da sauri don ƙirjinsa zafi yake. Sai dai ko rabin jikinsa bai samu shigewa ba ya faɗi a wurin. Ƴar Ficika aka sake samun abin yi. Ya ɗora hannu a ka zai cigaba da ihu, Kamal ya daka masa tsawa.

"Kada ka kuskura ka sake tara mana jama'a. Yi sallama ciki ka yi min magana da Yaya."

"To, to" ya amsa kamar ba ɗan cikinsa bane ya yi masa tsawar. Yadda mata ke ruɗewa a irin wannan yanayin, haka nasa hankalin ya gushe.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now