13

1.2K 160 25
                                    

RAYUWA DA GIƁI  13


Batul Mamman💖

Kada ku manta da bibiyar shafin Hauwa a instagram  @luciousbite.ng ko nemeta a waya ta wannan layin domin
09078075182 odar snacks da nau'ikan youghurt masu daɗi.



***

Irin rawar jikin da Anisa da Anti suke yi da Taj tuni ya sha jinin jikinsa. Shi da ya zo don su haɗu a sirrance ya zame ashe Hajjo tayi masa handsfree da alama. Kuma a ɓangarensu zancen ya sami karɓuwa.

Ɗakin Hajjo aka kaisu. Tana ganinsu ta washe baki tana tarbar Kamal.

"Sai ga Haffiness ɗin Haffi a Abuja. Sannu da zuwa Kamalu."

"Har kin ƙara masa wasali a sunan nasa kenan." Taj ya faɗi yana zama akan kafet. Ƙafafunsa ya miƙe da yake jin sun sage saboda zama.

Kamar ba da ita yake ba.Ta cigaba da yiwa Kamal magana
"Ya ka baro mutanen gida? Ya baban naku?"

Kamal ya amsa ta sake sako wata tambayar. Taj ya gaisheta har sau biyu bata amsa ba. Ya dai gane  fushi take dashi. Bayan kuma shi ya kamata ya nuna ɓacin ransa da tayi saurin sanya shi cikin tsaka mai wuya. Yanzu duk gidan nan za su so jin matsayarsa kan maganar Anisa. Tunda yarinya dai alamu sun nuna ta amince, ana jin zance ya sauya salo nan gaba kaɗan za a ɗora masa laifi.

Share su ya yi ya kira uwayensa ɗaya bayan ɗaya ya sanar dasu sun iso lafiya. Sai kuma ya kira Abba shi ma. Su ka yi magana akan ɗan gyaran da za a ƙarasa a wurin da Taj ya kama musu kafin ya dawo.

"Hajjo in kin gama gaisawa da Haffiness ɗin nima ki ɗan bani lokaci don Allah. Yau za mu koma. Bana son mu yi dare."

A sukwane ta juyo rai a ɓace "banten uba! Ku iso yanzu ka ce kuma komawa za ku yi?"

"To ya za ayi? Aiki ya sako ni a gaba."

Dariyar Kamal a dalilin zolayarta da Taj yake sai ta gane ba tafiyar za su yi da gaske ba. Sha kunu gami da nuna masa yatsunta biyar.

"Buhun ubanka Tajo."

"Toohhh" Kamal ya kalleta da rashin jindaɗi. Dole taji kunya don bata ga alamun yana da idanu a tsakar ka irin na Taj ba.

"Ɗan uwan naka ne bashi da kirki Haffiness. Na yi masa maganar ƙanwarsa ya amsa rimi-rimi sai kuma ya shuka ni. Yanzu ma gajiya nayi ina ta tunanin ko yarinyar ce ta ce bata so shi ne na kira uwar na tambayeta."

Kai tsaye Tay ya tambayeta "Me su ka ce?"

Hajjo ta danƙara masa wani irin kallo "me kuwa za su ce sama da murna. Ko kai makaho ne ya dace ace ka fahimci yadda ake ta nan nan da kai ya sha bamban da lokutan baya."

Shirunsa a yanzu daidai yake da cutar kai. Idan ya kuskura ya fita daga ɗakin nan bai faɗi abin da yake ransa ba to tabbas aurensa da Anisa da wahala in ba ayi ba. Gyara zama ya yi ya ce,

"To ni dai gaskiya Hajjo..."

Yau da gobe tafi ƙarfin wasa. Kuma dai Kamal ya riga ya san ba so yake ba. Amma akwai kunya da kawaicin malam bahaushe. Rashin girmamawa ne idan Taj ya kalli tsabar idon Hajjo ya faɗa mata baya son jikarta.

"Hajjo magana ta gaskiya yanzu Taj tsoron ɗauko zancen aure yake."

"Saboda me? Yana da lalura ne?" Ta soma yi masa kallon ƙurilla.

Ya girgiza kai "a'a, amma kin san matsalar da yake fuskanta daga wajen Alhaji."

"Alhajin me?" Ta fara sababi "in kai ma baka da labari ka sani daga yau. Kakarku wadda ta tsuguna ta haifi Hayatu aminiyata ce ta ƙud da ƙud. Duk taurin kansa bai isa na faɗa ya faɗa ba."

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now