15

1.2K 168 61
                                    

RAYUWA DA GIƁI  15

Batul Mamman💖



Sautin amsa sallamar cika wajen ya yi kamar zai fasa kunnuwa. Kusan a lokaci guda Hamdi, Salwa da Anisa su ka toshe kunnuwansu. Sakamakon ƙatuwar sipikar dake kusa dasu wadda ta ƙara ƙarfin sautin. La'akari su ka yi da toshe kunnen da su ka yi a lokaci guda sai su ka kama dariya.

Anisa dakatawa tayi da ta kalli fuskar ƴan matan dake gabanta. Bata san Salwa ba, amma ta so ta tuna Hamdi. Ita ma Hamdin sai aka yi dace ta kalleta a lokacin. Mamaki ne ya kama ta domin kuwa babu yadda za ayi ta ce ta manta kamanni da sunan Anisa.

Girarta ce ta ɗage tana mai yi mata kallon sani ta ce "Anisan Abuja?"

Gaban Anisa ya yi wani mahaukacin faɗuwa. Ba wai son ganin Hamdin ne bata yi ba. Abin da ya kawota taron buɗe restaurant ɗin Taj wanda bata manta ba shi ya dinga rarrashinta a waya har su ka isa inda take a lokacin nan. Kada dai irin abin da take karantawa a social media a ce vendor tayi snatching miji ko saurayin costumer ne zai sameta?

Hamdi kuwa tunda gari ya waye sai yanzu tayi dariyar da ta kai mata zuci. Fuskarta ta haskaka da farincikin da yake ranta.

"Allah Sarki. Naji daɗin sake ganinki. Lokacin da mu ka haɗu bani da waya. Daga baya da nayi kuma Anti Labiba ta ce ashe bata yi saving number ɗinki ba."

Da ƙyar Anisa ta haɗiyi yawu ta ƙirƙiri murmushi. Yanayinta na rashin nutsuwa duka a idon Salwa. Har ta kai ta matsu da son sanin me ya kawo wannan canji a tare da Anisan. Zuwan Sajida da Zee wajen ne ya taimakawa Anisa ta samu ta daina murmushin dolen da take ta yi.

"Hamdi zo mu zauna ga seat Yaya Kamal ya ce sai an gama speech za a buɗe ko'ina a shiga."

"Har Kamal kin sani?" Anisa ta ce a gigice, sai kuma tayi saurin canja zancen da taga suna kallonta da rashin fahimta "kuna da alaƙa da Kamal?"

Hamdi bata da amsar bayarwa don Kamal ɗin ma bata taɓa gani ba. Sunansa kawai ta sani. Ta kalli Sajida tana jiran tayi bayani sai jin baƙuwar murya tayi tana yiwa Zee magana.

"Abba Habibu ya shigo kuwa Zee? Taj ke tambayar...."

Kasa ƙarasa magana yayi. Ya tsaya kallon Hamdi ba shiri da irin mamakin da ta gama na ganin Anisa. Ya kalleta, ya kalli Sajida da Zee sannan ya yi magana.

"Ke ce Hamdi?"

Murmushi tayi da kunyar tuna abubuwan da tayi a gabansu wannan ranar.

"Ina wuni?"

"Ba zan amsa ba don naga alama da gangan ki ka dinga wasan ɓuya don kada mu haɗu." Ya kalli saman stage inda Taj ya juya musu baya yana magana "bari Happy ya gama speech ya zo ya ga mai kukan bolt."

Ba don hayaniya ba da sai kowa yaji sautin wucewar wani abu kamar dutse da ya tokarewa Anisa wuya tun ɗazu. Maganganun Kamal sun tsefe mata zargin da zuciya ta fara kitsa mata. Ba kunya ta saki fuska tana dariya harda cewa,

"Ai kuwa na san zai yi mamaki."

Kamal kuma ya dubi Sajida bayan ya gabatar musu da Salwa a matsayin ɗaya daga cikin ƙannensa.

"Na jima ina son tuna inda na taɓa ganin mai kama daku na kasa. Da yake ban ma riƙe sunanta ba lokacin haɗuwarmu a Abuja shi yasa ban taɓa alaƙanta ku ba."

"Ikon Allah kenan. Muma fa ta bamu labarin haɗuwar taku." Sajida ta faɗi tana kallon yadda duk wani haske na fuskar Hamdi ya ɗauke kamar an ɗauke wuta.

Taɓota tayi sai tayi firgigit ta dubi Kamal ta sake kallon saman stage inda Taj yake tsaye. Dutsen da ya bar ƙirjin Anisa ashe nata ya koma. Ya haɗe mata da wani irin ɗaci na tsagwaron disappointment. Kallon mutumin da ta kasa cirewa daga ranta har rana irin ta yau a matsayin Happy Taj kawai take yi. Ubangidan Abbanta wanda take baƙincikin shigowarsa cikin rayuwarsu da ƙara ingiza mata uba ya cigaba da girki. Daina jindaɗin komai tayi a wajen sai tsananin son ta ganta ƙudundune akan katifarta a ƙuryar ɗaki. Ƙafafunta su ka koma tamkar leda don ji tayi kamar ba za su ɗauketa ba.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now