34

1.4K 154 36
                                    

RAYUWA DA GIƁI 34



Batul Mamman💖



*
Saɓanin baƙin jiya da bata gama sabawa dasu ba, yau da yake Yaya Hajiyye da Firdaus ta zo sai Hamdi tayi saurin sakewa. Ga albishir ɗin tafiyar Yaya da ya sake faranta mata rai. Kitchen su ka shige da Firdaus suna ƙusƙus. A falo kuma Taj ne da Yaya Hajiyayye su ke tasu hirar.

"Wai ka san Kubra tare su ka tafi da Alhaji? Ko ni kaɗai ce ban san da tafiyar ba?"

"Bana son jin kowa na faɗin bai sani ba. Sai nayi ta wasu irin tunani." Taj ya faɗa da damuwa a tare da shi "kamar wani abu ake ɓoyewa."

"Kai ka san Alhaji bashi da wannan. To ma me zai ɓoye? Kawai maybe taji maganar ne ta ce ita ma zata sai ya barta."

"Amma ta kasa faɗa a Home group?"

Waya Yaya Hajiyayye ta ɗauko ta dubi Taj "zan yi sanarwa yanzu. Duk mai ƴan matsabbai da lokaci da kuma niyya ta shirya sayen ticket mu bi su."

"Ayi min alfarma. Jiya na kai Hamdi anyi passport. A jira ya fito a sami visa."

"Gaskiya za a iya jimawa. Mu tafi za ku taho?" Ta ce don akwaita da wutar ciki. Bata son ɓata lokaci idan aka ce za ayi abu.

Taj ya bata amsa da cewa "Alfarma na nema" yana sa ran komai zai samu da wuri in sha Allahu.

Basu gama hirar ba Salwa ta ƙwanƙwasa ƙofa. Taj ya tashi zai buɗe sai ga Firdaus ta fito daga kitchen. Maimakon ya koma wajen zamansa sai yayi kitchen.

Ita kuwa Firdaus hannun ƙofar ta kama da murnarta tana cewa "Ko ƴan gidanmu ne?"

Wani irin kallo na rashin fahimta ta yiwa Salwa da ta gani a tsaye taci kwalliya irin wadda bata taɓa ganinta da ita ba.

"Anti Salwa ke kaɗai? Ina Anti Zahra da su Hayat?"

"Ni kaɗai ce. Ya Taj yana nan?"

"Eh, shigo ciki."

Ƙamshin turarukan da Salwa ta yiwa fesawar Allah tsine saboda yawa ya doki hancin Yaya Hajiyayye da Taj. Ta dinga taku ta shigo ciki da kwarkwasa. Ta kuma rasa inda za ta zauna sai kusa da Taj dake zaune akam two-sitter. Shi da yayarsa tsayuwa ganin ikon Allah da tana nufo shi suka yi. Shi yasa babu wanda ya iya dakatar da ita.

"Ya Taj ina wuni?" Tayi magana da wata zuƙaƙƙiyar murya.

"Lafiya ƙalau."

"Ka ganni sai yau ko?"

Tashi ya yi tsaye da yaji me ta ce ya ce "mun yi dake za ki zo ne?"

Ko a jikinta ta sake kashe murya ta ce "Noooo, I thought you want to see me. Miss me?"

"Ba sai kin canja harshe ba Salwa, gidanmu babu wanda bai yi karatu ba." Yaya Hajiyayye ta ce tana jifan Taj da wata muguwar harara "akwai wani abu a tsakaninku ne?"

Duk da ya gane tambayar domin abin da Salwa take yi da kalamanta kowa zai harbo jirginta da wuri.
"Me ki ka gani?"

"Me ta zo yi gidanka a haka?" Yaya Hajiyayye ta nuna ta sama da ƙasa.

Danne ɓacin ranta tayi ta ɗauke kai ta dubi Taj.

"Ya Taj a ina za mu yi magana?"

Gajiya da sauraronsu Hamdi tayi ta baro ƙofar kitchen ɗin inda take tsaye ita da Firdaus tun bayan ta faɗa mata baƙuwar da aka yi.

"Ga hanyar ɗakinsa can ku je can ku yi."

"Ba laifi, gara na san yadda yake tun yanzu kafin na dawo cikinsa." Ko shakka bata ji ba ta bada wannan amsar tana murmushin cin nasara.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now