21

1.6K 183 90
                                    

RAYUWA DA GIƁI  21


Batul Mamman💖

This page is sponsored by Scentmania by Sana. A Kano take, amma ƙamshi babu ruwansa da gari ko ƙasa. Wuyarta ciniki ya faɗa. Za ku sami undiluted oil perfumes ɗinku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haɗa kwalabe daban daban ki gigita waɗanda ya halatta su ji ƙamshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeta a wannan layin 07065525409.



***

Da farko da taji ƙarar wayar cikin baccin da ya fara ɗaukarta tsorata tayi don ta manta da ita. Niyyarta ta barta ta gama sai ta kashe, ko waye ya kira da kansa. Ita ba mai son amsa wayar mutane bace. Wani kiran ne ya sake shigowa immediately bayan na farkon ya katse. Ta daure ta wartsake idanu ta kalli sunan mai kiran SALWA B. Wani irin tunani ne ya shiga karakaina a ƙoƙon ranta. Meye ma'anar B ɗin? Bichi, Bunkure? Ba dai brother bane tunda sunan mata ne. To ko dai baby yake nufi? Ko bestie? Haba! Zuciyarta tayi wani irin kumburi ta taso mata har wuya. Harda wani ɗaci-ɗaci kamar  ta tsotsi flagyl. Mantawa tayi da maganarsu da Abba a karo na biyu yau ta amsa kiran ido rufe. Garin sauri harda _record_ ta danna a rashin sani da ta mannata a kunnenta.

"Ya Taj na tasheka ko?"

Salwa tayi magana da sassanyar murya da ta sha kwaskwarima domin yin tasiri a zuciyar wanda ake yiwa.

"Ayya ba shi bane. Ya manta wayar ne." Hamdi ma ta mayar da zuƙaƙƙiyar murya.

Ba shiri Salwa ta zabura ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi. Da ta gama shirin yadda za ta dinga mirginawa hagu da dama saboda daɗin murya da hirar da za su yi da Taj.

Gabanta na faɗuwa ta ce "Wace ce ke?"

Tana buɗe murya normal, Hamdi ta gane wannan wayar ba ta ƴar uwa bace. In ma ƴar uwar ce to tabbas cousin ce.

"Suna na Hamdiyya." Ta ce a kunyace "manta wayar ya yi a wajena ɗazu."

Tsakin Salwa taji wanda ya yi mata ciwo matuƙa kafin ta ji ta ce,

"Wai ƴar gidan ɗan daudun da ya aura last week ce?"

"Laahhh, ashe kin sanni."

Hamdi ta amsa da sauran fara'a a muryarta kamar gaske. Bata so tayi saurin kwafsawa kuma ya kasance Salwan ƴar gidansu ce.

Cikin huɗubar Mami harda kada ta ragawa yarinyar da ya aura. Tunda ance musu sakandire ta gama sun tabbatar babu wayo da wayewa a tare da ita. Tsorata ta da nuna mata ita ɗin ba komai bace zai taimaka sosai wajen samawa Salwa ƴanci idan ta shiga gidan Taj.

"Da alama kina da rawar kai. To amma ba zan hana ki ba. Lokacinki ne. Ki dai sanya a zuciyarki cewa nan ba da jimawa ba wadda ta fi ki son Taj za ta shigo rayuwarsa."

Hanci Hamdi ta ja kamar mai shirin kuka "Anti Salwa nayi muku laifi ne har ku ke son bashi wata daga aurenmu? Ita wadda za ku bashi ɗin bana jin ta kai ni son shi. Don dai bamu haɗu bane da kema sai kin yaba min. Tarbiyya da iya kula da miji duka ɗan daudu da miskiniyar da su ka haife ni sun koya min."

Amsar Hamdi ba ƙaramin tayar mata da hankali tayi ba. Kai tsaye ta faɗa mata magana ta rama wadda tayi mata. Tana so ta ce mata ita da kanta za ta auri Taj amma gani take faɗin hakan zubar da aji ne sai ta gimtse fuska cike da takaici.

"Ni ba ƴar gidansu bace."

"Ikon Allah. Kuma naga ya yi saving sunanki da Sister Salwa? Cousin ɗinsa ce ke kenan?"

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now