36

3.1K 214 113
                                    

RAYUWA DA GIƁI  36



Batul Mamman💖





***

A dalilin ba lokaci ɗaya aka saya musu ticket ba, wurin zaman Yaya da na abokan tafiyarta daban daban ne.  Ɗan saurayin cikinsu Yaya tayi niyar bawa boarding pass ɗinta domin ya duba mata wurin zamanta, haka Abba Habibu ya sanar da ita tayi. Ya ceba inda mutum yake so zai je ya zauna ba. Ta ɗaga hannu za ta bashi Mubina ta riga karɓa. Ta kaita har wurin kujerar ta taimaka mata da ɗora hand luggage a sama sannan ta ɗaura mata belt. Ko ba a faɗa ba ta riga ta gane Yaya bata raɓa shiga jirgi ba.

Yaya tayi ta godiya da sanya mata albarka. Ita kuwa Allah Ya sani da biyu take yi. Kafin jirgi ya tashi bayan kowa ya zauna ta zo ta roƙi wadda take kusa da Yaya da cewa mamanta ce su ka yi musanyen seat. Wannan abu yasa Yaya jindaɗi matuƙa. Ta saki jiki da Mubina suna ta hira. Da jirgin zai tashi duk wani tsoronta Mubina ce ta dinga kwantar mata da hankali. Har aman da ta dinga ji Mubina leda ta bata sannan ta dinga shafa mata baya tana cewa ta hura iskar bakinta a ledar. A haka har su ka daidaita a iska.

"Allah Ya yi miki albarka Ya raya miki zuri'a. Ya jiƙan mahaifa."

"Amin Mama."

"Yaya yaran su ke kirana. Kema in babu damuwa ki dinga kirana da hakan."

Da murmushi Mubina ta ce "to Yaya."

Lokacin da aka kawo abinci Yaya bacci take yi. Mubina ta tasheta ta ci  sannan da dabara ta sako zancen da ta zauna dominsa.

"Takardar nan ta passport ɗin ki naga jininki O- ne ko?"

"Ban dai riƙe ba amma tun a gida yara ke cewa O. Wani abin ne?"

Da sauri Mubina ta girgiza kai tana mai son ɓoye zallar farincikinta sai dai Yaya ta fi ta wayo.

"Babu wata matsala. Jinin naki mai kyau ne domin babu wata lalurar da za a buƙaci wani abu na sassan jiki da ba za ki iya taimakawa ba."

"Ikon Allah. Ki ce idan na koma in nemi ƙarin sadaki a wajen Abban su Hamdi."

Dariya Mubina tayi kawai sannan ta kuma tambayarta ƴaƴanta nawa.

"Huɗu ne."

"Kin taɓa yin ɓari?"

"Wai, sosai kuwa. Biyu nayi kafin babbar. A tsakaninsu kuma yaran na ƙara uku. Wani lokacin sai na sa rai da cikin sai ya zube."

Mubina bayani gamsashshe tayi wa Yaya game da rhesus da irin rawar da yake takawa idan aka sami saɓaninsa a tsakanin mata da miji wurin haihuwa.

"Ilimi kogi. Dole ake cewa tafiya mabuɗin ilimi. Kinga zaman abin da bai kai wuni ba amma na ƙaru." Da yake ita ɗin akwai zurfafa tunani sai ta tambayi Mubina me yaja hankalinta har take ganin farinciki a tattare da ita game da jinin.

Kunya ta kama Mubina.
"Allah ni likita ce. Yana ƙayatar da mu ganin masu abin da wasu su ke buƙata ido rufe." Tayi dariya "kada ki ce yau kin gamu da mayya."

Yaya ma dariya tayi. Sai dai kuma daga lokacin ta dinga karantar Mubina. Akwai abin da take ganin ta ɓoye mata. Kai gani ma take tana son faɗa mata amma kamar tana jin tsoro. A zuciyarta ta ce 'Allah Yasa alkhairi ne'.

***

Yau sun tashi jikin na Kamal kwata kwata babu daɗi. Anyi alluran, an saka ruwa amma duk da haka ciwo yaƙi sauka. Su Umma ke kuka Hajiya na rarrashinsu. Tun zuwansu ko sau ɗaya bata zubar da hawaye ba. Halin da ta riski Kamal a kullum gani take ba zai shiga wata sa'ar ba. Sai dare take zuwa asibitin. Kullum tana hanya daga Jeddah inda asibitin yake zuwa Makka ta wuni a Harami tana ibada. Ta zabge sosai kamar ba ita ba. Masu rarrashin nata kuma sun fita nuna rauni. Suna tausayin Kamal suna tausayinta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 08 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now