26

2K 202 139
                                    


RAYUWA DA GIƁI  26



Batul Mamman💖




***

Shirin fita zuwa wani katafaren wurin gyaran jiki da Amma ta biya kuma ta ce za ta turo direba ya ɗauki Hamdi kafin ƴan kawo lefe su iso take yi. Zee da ƙanwar Anti Labiba mai suna Fadila ne ƴan rakiya. Komai cikin mutuwar jiki take yinsa musamman da jiya bata sami isashshen bacci ba. Tayi ibada kuma tayi kuka sosai. Yawanci akan ce asiri birkita tunanin mutum yake yi har ya kasa gane taƙamaimai me yake damunsa. Halin da take ciki kenan yanzu. Tana son Taj, sannan kuma tana gudun kasancewa inuwa guda da shi.

A daren jiya ne da tana addu'a ta fara mamakin wannan sabon al'amari  da ya tunkaro su. Alaƙarta da Taj ba irin wadda ake shan wahalar farata bace. Lokaci guda su ka yi clicking kamar hagu da daman mayen ƙarfe. Irin wannan rashin sakewar kafin a saba duk basu fuskanta ba. Lokaci guda su ka karbi juna a sabon matsayin da Allah Ya ajiyesu.

"HAMDIYYA!"

Firgigit ta dawo hayyacinta da jin kiran Yaya da ƙarfi.

"Tunanin me kike yi haka?"

"Babu komai" ta miƙe tsaye tana neman mayafinta.

"Me ki ke nema?" Yaya ta tambayeta.

"Mayafina."

"Wanda ki ka yafa kuma fa"

Kallon jikinta tayi ta ce "au..."

"Zauna Hamdi. Magana za mu yi."

Bata kawo komai ba tunda a tunaninta ta ɓoye yanayinta sosai ta zauna. Yaya ta tsareta da tambayar me yake damunta kwana biyu. Ta fara rantse rantse Yaya ta ce bata san zance ba.

"Idan ba wata uwar gareki a waje wadda ta dace da sanin damuwarki ba ina son sanin me ya sanyaki kwana kina sallah da kuka."

Gaban Hamdi faɗuwa ya yi. Ba za ta iya faɗawa kowa Taj ya mareta ba. Haka kawai take ganin kamar za su yi rabuwa ta har abada idan aka sani.

"Yaya babu komai."

"Kina ganin saboda lalurata da yanayin Abbanku bamu isa mu share miki hawaye idan kina da damuwa ba ko?"

Ɓacin ran uwa abin gudu. Nan da nan hankalinta ya tashi ta soma bata haƙuri.
"Ki daina faɗin haka. Wa nake da shi bayan ku?"

Da wata irin murya mai ban tausayi Yaya ta ce "Ba yau ki ka fara ba. Tun ƙuruciyarki na san kin tashi da ganin kamar bamu cika iyaye ba."

Kuka sosai Hamdi tayi. Wannan banzan tunanin tun yaushe ta ajiye shi. Ummi ta ankarar da ita girman mahaifinta a lokacin da take ganiyar gudun a alaƙantasu. Yaya ce dama tun farko bata taɓa rainawa ba. Tana son abarta a yadda take. Wannan furucin da tayi ne dai ya sake karyar mata da zuciya tayi ta kuka tana bata haƙuri.

Bayan wani ɗan lokaci da Yayan ta ce ta haƙura shi ne ta faɗa mata rabin gaskiyar zancen. Akwai mai son Taj, ta dawo da wayar da su ka taɓa yi ta ce ai matar har kiranta tayi ta tsorata ta.

"Wai idan na yarda na tare sai ta illata rayuwata."

Dariya taga Yaya tayi kafin kuma ta ce,

"Shi ne kike kuka? Kodayake Allah ki ke gayawa. Ya isar miki akan komai. Duk da haka cewa Yayi ka tashi In taimakeka. Kada ki yarda wata mace ta zama silar hawayenki a gidan miji."

"Ko da yafi sonta?" Hamdi ta tambayeta tana kuka.

Da yake Yaya bata saba ganin ƴar tata ta nuna rauni irin haka ba sai take ganin son da take yiwa Taj ne kawai bata son abin da zai shiga tsakaninsu. Kalaman da za su kwantar mata da hankali ta zaɓo. A cikin ranta kuma tana ƙudurta yi mata addu'a da sauran ƴan uwanta akan kada Allah Ya haɗa mazajensu da matan banza.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now