30

2.3K 218 81
                                    

RAYUWA DA GIƁI  30




Batul Mamman💖



Kuna neman reliable data ba cuta va cutarwa? Ku saya a baku na kowane layi cikin aminci da rahusa?
Look no further. Contact MKdataservices for your data, airtime, tv subscription and nepa bills.

08038258489

https://www.mkdatasarvices.com.ng

Sayen nagari....mayar da data gida!

~~~~~






Ya yunƙura zai tashi ba shiri don ya san yau ɗin abin da zai fuskanta sai ya gwammace kiɗa da karatu. Alhaji ya yi masa alama da ya koma. Ya sake yunƙurawa dai sai Alhajin ya kalle shi yana mai buɗe masa idanu. Dolensa ya koma ya tada kai da filo.

Mubina dake tsaye da tasar allura tayi wiƙi-wiƙi da idanu ya duba "Ƙarasa ki duba min shi mana."

Tayi sauri ta isa gaban gadon. Ido Kamal ya rufe don allurar akwai zafi. Alhaji yaji wani irin tausayinsa ya tsirga masa. Kujerar gaban gadon yaje ya zauna. Ya kama hannun Kamal na dama ya riƙe. Irin riƙon ƙarfafa gwiwa da rarrashi.

Dama yaya lafiyar kura? Duk wani emotion na rauni da Kamal yake adanawa tun farkon rashin lafiyar a lokaci guda ya fashe. Ya ƙara ƙarfin riƙon hannun mahaifinsa yana kuka mara sauti. Tsananin tausayinsa yasa Mubina taya shi. Nos ɗin ma kawar da kai gefe yayi. Shi kuwa Alhaji dakewa ya yi duk irin yadda hankalinsa ya tashi.

"Kuka a gaban mace Kamal kamar wani mace? Ni fa ka san ba shiri nake da rago ba."

Hawayen ƙaruwa su ka yi. Ya dawo da kansa saitin Alhaji kawai ya cigaba da abinsa.

Alhaji yayi murmushi "matana basu taɓa ganin hawayena ba duk shekarun nan. Kai kuwa ka saka mace a gaba kana abin kunya. Ko batun alaƙar taku shi ma ƙarya ku ka yi min?"

Girgiza kai Kamal ya yi. Alhaji ya dubi Mubina da allura a hannu tana kallon ƙasa. Allurar ya ce tayi tunda da alama akan lokaci ake buƙatarta. Ba don haka ba ya san Kamal ba zai fito da asuba ba. Bayan anyi allurar wadda yadda yaga an soka ta ciki ya ƙara kiɗima shi sai ya tambayi Nos ɗinnan abin sallah. Gari har ya soma haske basu yi asuba ba. Daga kan gadon Kamal ya bi shi sallar. Bayan sun idar suna zaune su biyu, Alhaji yana zaune akan abin sallah ya tambaye shi game da ciwon.

"Lalurar dake damunka a hanyar fasiƙanci ka same ta ne?"

"A'a Alhaji" ita ce amsarsa.

Muryar Alhaji ta karye domin a tsorace yake Allah Ya sani. Kamar kada ya idar da sallah ya yi tambayar tun farko.

"To me yasa? Mene ne dalilin ɓoyewar?"

"Saboda maganin ba mai samuwa bane Alhaji. Ƙoda nake buƙata kuma ..."

Yana son yin faɗa amma ya san cewa abin da zai sa Kamal yi masa ɓoyon ciwo ba ƙaramin abu bane.

"Gani, ga ƴan uwanka mutum ashirin da bakwai amma ka kasa faɗa? Bayan na san karamcin da Allah Ya yi min a gidana. Yau ko babu ni babu mahaifiyarka ina da yaƙinin cewa sauran uwayenka za su tsaya maka ka samu a jikin ƴan uwanka ko da kuwa ƴaƴan cikinsu ne."

Nan dai Kamal ya yi masa bayani akan matsalar da aka samu. Bai gamsu ba sai da Mubina tayi masa fashin baƙi. Amma duk da haka zuciyarsa fafur taƙi amincewa. Ana bayanin yana jin zufa a duka jikinsa. Gabansa kuwa faɗuwa kawai yake yi.
Yayi salati yafi a ƙirga. Kamal ya yi mamaki domin faɗa yasa rai zai yi masa.

"Alhaji baka yi min faɗa ba."

"Wane irin faɗa kuma Kamal? Ta yaya ma za ka yi tunanin zan maka faɗa? Halin da zuciyarka take ciki na firgicin ciwon ma da ina da iko wallahi zan raba ka dashi. Da ace akwai yadda zanyi cikin ku babu mai yin atishawar da zai ji a jikinsa. Baka ganin dalilin ciwo na dawo da ɗan uwanka? Ta yaya kai kuma zan yi fushi da kai?"

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now