20

1.5K 183 113
                                    

RAYUWA DA GIƁI  20

Batul Mamman💖


Gaisuwa ta musamman ga baiwar Allah da ta tura saƙo OpenDiaries. Ina fata kin sami sauƙi. Allah Ya inganta Ya raba lafiya. Abba Habibu Simagade yace a baki haƙuri ba niyyarsa kenan ba. Shafin yau naki ne.

Ina ƙara tunatar da masu karatu posts weekdays ne kawai don Allah. Nagode sosai. SonSo

***

Na ɗan taƙin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta so ƙullewa har ma ya faɗi abin da bai yi niyya ba. Cikin sa'a sai ya tuno abin da ya tanadi faɗawa duk wanda ya ganshi a wannan yanayin. Murmushi ya yi mata sannan ya ɗaga hannuwa da ƙafafunsa yadda za ta gansu sosai.

"Mene ne wannan Kamal? Me ya same ka kake irin wannan kumburin?" Ta ƙarasa inda yake tana tattaɓa shi.

"Allergy ne Umma. A haka ma kumburin ya sauka sosai."

"Subhanallahi" ta matsa hannunsa na dama "akwai zafi?"

Kai ya girgiza mata. Ya zauna ya shirga mata bayanin ƙanzon kurege wai allergy gare shi kuma har yanzu likitan bai gano mene ne jikin nasa baya so ba.

"Anya ya san aikinsa kuwa? Me yasa baka je wurin yayarka ba?"

Gaban Kamal ya faɗi da tsoron kada Umma ta matsa masa akan zuwa wajen Yaya Kubra. Ita ce babba wajen Mama kuma sananniyar likitar ɓangaren lalurorin mata. Yana zuwa wajenta asirinsa zai tono.

"Ita da take gynae? Wannan ba ɓangarenta bane."

"Amma ai ba za ta kasa sanin likitan da ya dace da kai ba a asibitin Malam (AKTHA) ko? Ni dai bari nayi mata waya. Wannan kumburin ya bani tsoro. Har wani baƙi naga kayi."

"Kai Umma, idonki ne." Ya wayance.

Da ƙyar ya hanata kiran yayar tasu. Ya tabbatar mata likitan da yake gani ma ƙwararre ne. Harkar allergy wani zubin sai an wahala kafin a gano mene ne jiki baya so har yake reacting irin haka. Baiwar Allah sai ta yarda da zancen nasa. Ta kira masa Abba ta ce ya zo ya kai shi asibiti.

"Amma me ya sa ka ɓoye mana? Jiya ina kallonka kafin ku fita wajen sirikin Taj da Innarku ka shige kitchen ka watsa magani. Kuma yau kowa ya ce bai sanyaka a ido ba. Shi ne tsoro ya kamani. Ko ƙwaya ka fara sha."

Halin ciwon da yake ciki bai hana shi dariya ba.

"Abin da ban yi da ƙuruciya ba Umma?"

"Yo Allah na tuba shaye shaye lokaci gare shi? Kai dai kawai Allah Ya kare ku da sauran zuri'ar musulmi. Zamanin ya zo da hanyoyin ɓata tatbiyar tsofaffi balle kuma matasa masu jini a jika."

Tunaninsa na yadda zai je wajen likitarsa cikin sauƙi ya sami solution. Umma ta sa Abba ya kai shi asibitin. A hanya kafin ya ƙarasa ya tura mata saƙo ta bashi amsa. Roƙonta ya yi da sirranta lalurarsa a gaban Abba.

Da taimakon Abba ya iya shiga asibitin. Dauriya da ƙarfinsa sun soma ƙarewa. Wata Nos tana ganinsu ta hanzarta kiran likitar wadda dalilinsa ma ta fito don yau ranar hutunta ce.

Wata kyakkyawar matashiya ce ta fito sanye da baƙar abaya da ƙaramin hijab. A fuskarta gilashi ne mai ɗan kauri dake taimakawa ganinta. Madaidaicin tsayi gareta amma kuma she is a bit chubby. Sai dai ƙibar ba mai yawa bace. Ɗakin taimakon gaggawa tasa aka shigar mata da Kamal aka kwantar akan gado.

Abba ya gama tsorata da yanayinsa. Yana ganin ta farke sirinji cikin sauri ya ce "Doctor kinga jikin nasa duk ya rikice kafin mu ƙaraso. Don Allah ki gane mene ne ba ya so sai mu kiyaye."

"Ɗan bamu wuri" ta ce idanunta akan Kamal. Patient ɗinta mai ɗan banzan taurin kai.

Hankali a tashe Abba ya fita. Ya shiga fareti a wajen yana addu'ar a shawo kan matsalar da wuri.

RAYUWA DA GIƁIOnde as histórias ganham vida. Descobre agora