5

946 193 17
                                    

RAYUWA DA GIƁI 5

Batul Mamman💖






"Alhaji..."

"Zan saɓa maka."

Ba yadda ya iya. Cikin minti shabiyar ya sama musu tasi su huɗu suka kama hanya. Mama da Inna ba su san me ake ciki ba. Shi kuwa Alhaji tunda yaga sunan makarantar a bakin gate jikinsa ya soma tsuma. Ahmad dai jikinsa duk ya mutu. Ya yi kiran Taj ɗin da su ka shiga bai ɗauka ba. Da tambaya su ka ƙarasa wurin da ake gasar inda mutane su ka yi dafifi kamar ƙudaje. Basu wani sha wahala ba su ka hango tebura huɗu na ƙasashen da su ka rage a gasar. A yau za a fitar da wani team ɗin sai ya rage uku. Washegari idan an yi na ƙarshe a fitar da na ɗaya, na biyu da na uku.

Cikin wata irin nutsuwa da tsantsar ƙwarewa Taj yake aiki. Shi da Wakili girkinsu cikin tsari yake kamar sun manta da lokacinsu na tafiya. Wannan nutsuwar ita tafi burge alƙalan gasar. Masu sauri saurin cimma lokaci kuwa daga kwano ya faɗi ya fashe sai ka ji su na washhh, mai ko ruwa mai zafi ya fallatso mu su saboda garaje.

Tunda Alhaji ya yi tozali da ɗan nasa wani abu mai masifar ɗaci ya sami wurin zama a maƙogaronsa. Taj yake gani sanyi da dogon wando baƙi da riga yellow mai tambarin makarantar sai apron fari tas ɗaure a ƙugunsa. APRON!?

Inna kuwa tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi. Tunda ta nunawa Mama shi bata sake iya cewa komai ba. Maman ce ma ta iya yin magana da ƙyar.

"Ahmad me idona yake gani?"

"Gasar girki ce" ya bata amsa a sanyaye.

"Ku zo mu koma." Alhaji ya ce da matansa "Kai kuma ka jira ya gama ka taho min da shi."

Ahmad ya so raka su amma ya nuna masa yawo a ƙasar da ba tasu ba, ba baƙon abu bane gare shi. Haka su ka tafi babu mai cewa komai. Da isarsu Alhaji ya ɗauko magungunansa na hawan jini ya watsa sannan ya ce kada wanda ya tashe shi sai Taj ya iso. Dama ɗaki uku ya kama musu. Sai su ka koma ɗayan.

Ido cike da ƙwalla Inna ta ce "Yaron nan so yake ya jaza mana tashin hankali ko me?"

Kallonta Mama tayi ta girgiza kai.

"Matsi da takura yaro bai fiye haifar da ɗa mai ido ba. Taj ya yi masa biyayya an sami abin da ake so. Mene ne aibu don ya ɗan waiwayi burinsa? Don fa mun haife su ba yana nufin dole su rayu kwatankwacin tamu rayuwar ko ra'ayi ba."

"Kayya dai Mama. Rayuwar yara sai da nuna hanya daga iyaye."

"Nima ban musa ba. Amma babu inda addini ya bawa iyaye damar tauye ƴaƴansu akan abin da bai saɓawa addinin ba. Baki ji malamai suna faɗin ko sakin aure indai ba bisa adalci ba, iyaye basu da hurumin tilasta shi ba? Girkin nan kuma maza nawa ke yi? Mene ne aibu a ciki tunda ba daudu yake ba?"

Inna dai duk a tsorace take ta ce "tunda mahaifinsa ba ya so sai ya haƙura ko don neman albarka."

Mama gani tayi cigaba da nunawa Inna illar takura tayi yawa ga ɗa mai biyayya bata da amfani ba sai taga Innar ta kasa fahimta. Idan ta matsa kada abin ya yi kama da tana son sanya shi yin bore. Zaman jiran tsammani su ka yi har bayan Isha.

*
Sakamakon gasa yau dai da su Taj ya tashi. Cikin nasara da taimakon Allah su ne su ka yi na ɗaya. Yawan makinsu idan an haɗa da na kwanakin baya ya basu damar iya yin na ɗaya gobe in sun dage. Banda ihun murnar ƴan Nigeria da su ke makarantar ba ka jin komai. Yanzu ya rage teams uku. Gobe za a fitar da na ɗaya, biyu da uku. Da su ka fito za su tafi Wakili ya tare shi da godiya.

"Ban san a ina ka koyi girki wanda yasa talent ɗinka ya zarce na kowa a nan ba. Your are truly amazing."

Taj ya yi murmushi "ai ban kai ka ba."

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now