32

1.2K 124 19
                                    

RAYUWA DA GIƁI  32


Batul Mamman💖


This page is sponsored by NAFS-BEDDINGS (Nafisa Tofa 08034581454). A trusted and reliable plug for bedsheets and duvets. A trial is all it takes to get conviced. Ƴar uwa a yar da ɗan yagwalgwalin zanin gadon nan da ya gama tashi daga wanki ɗaya a sayi garanti!






*

Rashin walwala da kuzarin Taj har su ka idar da sallah yasa Hamdi wasu irin tunani marasa daɗi. Me tayi masa? Ko wani abu ne ya same shi? Ko kuwa wani abu yaji wanda bai yi masa daɗi ba? Idan sun haɗa ido sai ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki. Cikin idanunsa fargaba take  gani. Tayi zaton mata ko ace amare ne kaɗai su ke shiga yanayin tsoro a irin wannan dare. Ashe harda maza. Kai, amma bata zaton haka a wajen Taj. Anya kuwa irin abin da yasa zuciyarta tseren da take yi tun ɗazu shi ne a ransa?

Suna zaune kowa akan abin sallarsa ta zuba masa idanu. Abu ne da bata taɓa samun damar yi ba a baya. Indai suna tare shi ne da kallon. Ko satar kallonsa ta so yi da wuya ta sami cikakken minti guda kafin ya sake juyowa. Amma abin mamaki yau da ake zaton wuta a maƙera sai aka sameta a masaƙa. Tafi minti goma tana nazartarsa bai sani ba. Daga zaune ta ja jiki ta matso kusa dashi tunda dama babu nisa tsakaninsu.

Muryarta a tausashe ta ce "Wani abu ne ya faru?"

"Me ki ka gani?" Taj ya faɗi yana miƙe ƙafafunsa. Sannan ya sanya hannunsa a kafaɗarta ya dawo da ita jikinsa.

"Babu komai tunda baka son faɗa min."

"Am fine Hamdi. Gajiya ce kawai."

"Allah Ya warware. Ka kwanta kayi bacci zuwa safiya za ka ji sauƙi in sha Allah." Bata yarda ba. Kuma ta san cewa shi ma da ya faɗa ya san bata yarda ba ɗin.

Neman abin cewa yake yi wanda zai kwantar mata da hankali sai wata ƙaƙƙarfar atishawa ta zo masa. Sau biyar yayi ta a jere. Kowacce ta fito sai ya ce Alhamdulillah. Ita kuma ta bi masa da YarhamukAllah.

Tabbas a cikin ambaton Allah akwai rangwame ga bayi. Tun a ta uku Taj ya soma jin ƙamshin ɗakin da na jikin Hamdi sun cika ƙofifin hancinsa. To dama sihirin ba ayi shi don ya kama shi da wuri ba. Musamman Alh. Usaini ya nemi wanda zai shiga sannu a hankali saboda Taj ya zata cuta ce. Idan haka ta faru asarar dukiya kawai zai yi ta yi wajen neman magani. Babu lallai in shi ko wani nasa ba masu yarda da harkar sihiri da bokanci su yi tunanin neman karya aikin da Ayar Allah.

Shi dai tunda yaji wannan ƙamshin ya  tashi da ƙarfinsa ya sungumi Hamdi yana faɗin Alhamdulillah.

"Wai don Allah me ya faru?"

Hancinsa ya ɗora akan nata tana cikin hannuwansa ya ce "its nothing" ya kama juyi da ita. Daga nan ya manta da komai ya kuma mantar da ita. Daren ya zama tarihin Tajuddin da Hamdiyya su kaɗai.

***

Wai bahaushe ya ce kayi da kanka kafin ayi da kai. Tunda Kamal ya faɗawa Yaya Kubra cewa Alhaji da Ahmad sun san da ciwonsa ta kasa samun kwanciyar hankali. Gani take kowane lokaci Alhaji zai iya kiranta. Abin da zai biyo baya kuwa sai Allah. Ilai kuwa wajajen goma na dare sai ga text ɗinsa. Bangajiyar biki ya fara yi mata sannan ya rubuta

(Ki nemi izinin mijinki. Ina son ganinki gobe da safe.)

Bacci ɓarawo da tarin gajiya ne su ka yi awon gaba da ita ba don ta so ba. Maigidan nata ta faɗawa komai a hali na tashin hankali.

"Wallahi ba ya son ɓoye ɓoye. Goben nan ban san me zai yi min ba."

"Baki kyauta masa bane kema kin sani. Ba don ya neme ki ba da nima zan nuna miki kuskurenki na biyewa Kamal. A wautarsa gata yayi muku na yin shiru. Amma a zahiri cutar kansa ya yi. Ance a problem shared is a problem solved. Bamu san ta inda za a dace ba da ya faɗa da wuri."

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now