7

1K 159 27
                                    

RAYUWA DA GIƁI 7


Batul Mamman💖

Sanarwa
In sha Allah post zai dinga zuwa ranakun Litinin zuwa Juma'a.



***

Ummi dai baje kolin rashin mutumcinta tayi akan Hamdi har ya kasance sauran ɗalibai suna samun sararawa. Kowanne aiki Hamdi, kowacce bola da shara ma ita ɗin dai take nema. Wanki harda na su pant ita take mata. Su ɗebo ruwa da kwafar note dama tuni ta daina saka wasu. Kuma ko da wasa Hamdi bata taɓa faɗin wata kalmar neman sauƙi ba. Komai Ummi ta ce 'to' ce amsar. Ita dai burinta ta bar makarantar ba tare da kowa ya san ko waye mahaifinta ba.

Da yake a cikin hutun da su ka aka yi jarabawar JAMB, yanzu ƴan kwanaki su ka rage kafin a fara WAEC. Kowa ya duƙufa da karatu ba ji ba gani. Waɗanda basu ɗauki karatun a bakin komai ba irinsu Ummi kuwa shagalinsu suke yi.

Ranar wata laraba da safe aka tashi makarantar babu ruwa. Abin ka da lokacin zafi. Tsakanin April da May a garin Kano dama ba a cewa komai. Rijiyar makarantar mai dama dama ba a samun komai sai wani ruwan dauɗa wanda zai iya sati bai kwanta ba. Kowa ya shiga damuwa don ko darussan aji ba a shiga ba. Ga ɗan karen zafi ana ta zufa. Principal tun safe ta fice sai wajajen shabiyu ta dawo da tankokin ruwa har bakwai a bayanta. Yara sai murna. Aka umarci malamai da su kula da ɗaliban wajen bin layi ta yadda kowa zai samu. Sannan an ja musu kunne babu mai ƙarɓar ruwa sau biyu. Kuma bokiti biyu kaɗai za a cika wa kowa saboda kada wasu su rasa.

Layi layi aka jera ɗaliban na ajujuwansu. A sammakon Hamdi ita ce ta talatin da huɗu a layinsu. Kafin a zo kanta rana ta gama dafa ta. Ana zuba mata taji wani sanyi ya ratsata. Ta ɗauki bokatan hagu da dama ta wuce ɗaki. Tun kafin ta isa bakin matattakalar hostel ɗin ta hango Ummi da ƙawayenta a zaune kan dandamalin wurin suna ta hayaniya ana dariya. Fuska a haɗe Ummin ta tarbeta da ta ƙarasa.

"Kin daɗe a layi gaskiya. Ke ko irin turereniyar nan baki iya bane?"

Take takenta Hamdi ta gane sai dai ta riga ta yiwa kanta alƙawarin ko me zai faru ba za ta bata ruwan da ta wahala wurin samu ba. Jikinta gabaɗaya ƙaiƙayi yake yi mata. Ga ƙishi ga yunwa.

"Ban iya ba."

"Mtswww, wuce ki kai min ruwan in samu nayi wanka kafin a gama abinci."

Wata zaƙaƙura ta ce "Ummi kin ce fa nima za ki sa ta ɗebo min."

"Ki bari ta juye min mana." Ta cewa wadda tayi maganar a wulaƙance.

Juyawa Ummi tayi taga Hamdi ta ajiye bokatan ta sarƙe hannu a ƙirji.

Rai a ɓace ta ce mata "Ɗauki mu tafi mana."

"Ki je ki bi layi don babu wanda za a zubawa sau biyu. Har ticking suna ake yi."

"To sai ki san yadda za ki yi. Ni ki wuce ki zuba min zafi nake ji."

Hamdi ta rasa daga ina take jin wani ƙwarin gwiwa kawai ta ce "naga kamar baki gane ba. Wannan ruwana ne. Ki je ki ɗebo naki."

Wata uwar shewa Ummi tayi tana dafa ƙirji "dani kike? Har kin manta abin da zan iya yi miki idan ki ka ɓata min rai?"

Tunawa da alamun mutumcin su Iyaa tayi sai take ganin kamar duk haukan Ummi ba za ta fitar da bidiyo ɗin ba.

"Kin daɗe baki nunawa duk makarantar nan waye ubana ba."

"Kanbu, dani kike?" Ummi ta faɗi cike da mamaki. Sai kuma ta fasa faɗan ta ce ƙawayenta su ɗauko bokitin.

Suna kai hannu Hamdi ta tare kayanta ta hanyar durƙusawa a gaban bokatan ta tarosu da hannuwanta.

"Wallahi ba zan baki ruwan nan ba."

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now