9

1.2K 163 49
                                    

RAYUWA DA GIƁI  9


Batul Mamman💖


***

Irin kukan da Iyaa tayi bayan jin tsiyar da Ummi take shukawa dole ya bawa mutum tausayi. Bayan an kai ruwa rana a station ɗin da su ka je Baba Maje ya gane duk inda yake tunanin Ummi ta wuce nan. Fitina da gagara ta ƴan matanci kam tana bugawa a bayan idonsa. Ya sake yarda ba a shaidar ɗan yau. Ba don da bakinta ta amsa laifukanta ba da ya yi rantsuwar sharri ake yi mata. Ummin da ya sani daban. Wadda ya dawo da ita gida daban.

Abin baƙinciki shaiɗanin tsohon najadun da yafi kowa hure mata kunne Uncle B ashe makanike ne. Matansa biyu da ƴaƴa goma sha uku. Sau ɗaya ake ɗora tukunya a gidansa. Irinsu Ummi ke cinye ɗan abin da yake samu. Ita da yake tunanin raba hanya da ita saboda rashin bashi haɗin kai tuntuni ashe silarta asirinsa zai tono. Sai da ya yi sati guda a ƙulle kafin a yarda a bada belinsa. Shi ma kuma an haɗa masa da muguwar tarar da zai ji jiki wajen biya.

Hantara da kyara su suka marabceta daga dawowarta gida. Ta zama mujiyar da bahaushe yake kira mai baƙin jini. Iyayenta ba su dake ta ba don ciwon abin da tayi ya kai maƙura. Yayanta Baballe ne dai ya kasa zama bayan yaji kukan Iyaa yayi yawa a waya da tana labarta masa. Ya niƙi gari ya taho Kano ya sakar mata ƙarfinsa. Zaneta ya yi ciki da bai babu wanda ya hana shi. Sai ma dare da jikinta ya yi mugun tsami ne Iyaa ta tada ta zaune.

"Sau nawa ki ka zubar da ciki Ummi?"

Duk soyewar zuciyarta da ya hanata kukan dukan da ta sha wannan tambaya sai da tayi sanadin zubar hawayenta. Hannu ta ɗora akan bakinta tana danne kukan.

"Iyaa? Ciki kuma?"

"To Ummi meye abin mamaki a ciki? Samarin da su ke kashe miki kuɗi ƙannen uwa ne ko na uba da za a ce zumunci suke yiwa?"

Hawaye take ita ma ga tsoron kada  Ummin ta amsa zargin da su ke yi mata ita da Baba Maje.

"Wallahi Iyaa ban taɓa yarda na bada kaina ba."

"To me ki ke basu ko me su ke samu a madadin kuɗinsu? Don dai bana jin shaiɗancin naki ya yi tsamarin da za ki asircesu su dinga bin umarninki."

Shiru Ummi tayi. Hankalin Iyaa ya sake tashi ta dinga kai mata duka da hannu ta ko ina.

"Ki faɗa min gaskiya kafin zuciyata ta buga."

"Iyakarsu tattaɓani amma bana yarda da..."

Da sauri Iyaa ta tashi don bata son kuma jin ƙarshen zancen.
"Ya isa. Kin yiwa kanki."

Fita tayi ta bar Ummi tana kuka. Kuma duk wannan abu bai zama ishara ya tuna mata yadda ta dinga cin zarafin mutane dole rana irin ta yau ta zo ba. Sunan Hamdi kawai ke yawo a zuciyarta. Ko harararta aka yi laifinta take ƙara gani. Musguna mata da ta dinga yi a makaranta ai bai shafi komai na karatunta ko rayuwarta ba a tunaninta. She was just having fun. Ba ita kaɗai bace senior mai yi wa na ƙasa da ita hawan karkatacciyar kuka, saboda haka bata ga dalilin da zai sa ita kaɗai ce rayuwarta ta kife irin haka ba. Da me ake so ta ji? Sanin waye Uncle B ko fitowar sirrinta? Ko kuwa rabata da makaranta a matakin ƙarshe da iyayenta su ka yi don ta ɗauki bidiyon ɗan daudu?

"Wallahi sai na rama Hamdiyya. Babu wanda ya isa ya saka ni kuka ban saka shi ba."

Da wannan kalaman ta goge hawayenta a fusace ta kwanta tana shure Siyama da ƙafa don ta ɗan matso ɓangarenta cikin bacci.

***

Kwanaki sun ja inda a farko farkon watan August ɗaliban sakandire su ka kammala jarabawar fita. An yi WAEC har ta fito kafin a gama NECO. Da taimakon Allah da kuma dagewar karatu Hamdi ta sami kyakkyawan sakamako.

RAYUWA DA GIƁIOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz