17

1.2K 180 63
                                    

RAYUWA DA GIƁI  17

Batul Mamman💖


***
"Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshi a ƙasa a miƙa godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ƴan matanki a sa'a guda. Wannan farar juma'a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ƴan dugwi dugwi iyalan Baba."

Ba kowa bane da wannan aiki sai Ƴar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka amshe guɗar su na yi. Yaya fitowa tayi daga ɗakinta inda ta fake da shiryawa ta zauna rarrashin Sajida da Zee. Hamdi na gefe ita ma tana basu baki tare da taya su kuka.

Anti Zinatu ce kaɗai ta san zaman me su ke a ɗakin. Ita ce ma ta tura musu Yayan domin wani ciwon uwa kaɗai ke iya maganinsa.

Hamdi na jin muryarsa ta haɗe rai bayan fitar Yaya daga ɗakin.
"Wai namiji kenan. Mtsewww."

Lulluɓi Yaya tayi ta fita soron. Ƴar Ficika ya wangale baki.

"Sai muka ji abin arziƙi ko Jinjin? Allah Yasa abokan zamansu ne."

Ita ma takaicin ɗaga muryar tasa take yi. Ga zaƙin murya gashi bai iya tausasa harshe. Ta tabbata kowa na jinsu a ciki.

"Da ka ɗan rage maganar saboda ƴan biki ba su san auren Zee aka ɗaura ba maimakon Sajida. Sannan kana cewa amare uku sai ayi zaton..."

"Ba zato bane Jinjin. Ƴaƴan Simagade sun zama farinwata sha kallo. An so tozarta shi sai gashi Allah Ya aurar dasu lokaci ɗaya."

Yaya dai bata fahimci inda ya dosa ba. Gani take wani zancen yake haɗawa da wani. Sai kawai ta koma ciki. Aka yi ta tambayarta me yake nufi kuwa don duk sun ji.

"Shirmen Ƴar Ficika ne. Shi da ko wurin ɗaurin auren basu je ba?"

Rufe bakinta ke da wuya Halifa ya shigo gidan kamar an jeho shi daga sama. Haki yake da ƙarfinsa saboda gudun da ya sha ba na wasa bane. Tun daga masallacin juma'ar unguwarsu har gida. Tafiyar kimanin minti talatin. Ƙafafunsa sun yi buɗu buɗu.

"Yaya! Yaya!!" Ya dinga ƙwala kira kamar makaho na neman ɗan jagoransa.

"Kai Halifa lafiyarka kuwa?" Wata  maƙociyarsu ta tambaye shi.

"Ina Yaya?" Ya faɗi yana dariya.

Banda Yaya, duk matan da su ke gidan fitowa su ka yi. Yana ganinta ya taho da sauri, sai kuma ya tsallaketa ya rungume Sajida.

"Wai mene ne Halifa? Ka sanya mu a duhu" cewar Inna Luba.

Murmushi ya yi yana duban ƴan uwansa.

"Yaya an ɗaura. Duka su ukun an ɗaura musu aure."

Dafa shi Inna Luba tayi zuciyarta na bugawa.
"Nutsu ka yi min bayani. Su waye su ka yi auren?"

"Ya Sajida da Yaya Safwan."

Sajida ta bar jikin bangon da ta jingina tayi da sauri, ta rufe bakinta da hannu. Wasu zafafan hawaye suna sauko mata. Hamdi ta rungumeta tana cewa "Alhamdulillah."

Anti Zinatu ta ce "Mata biyu aka aura masa kenan? Naji ka ci mutum uku."

Ya murmusa da farincikinsa "a'a, sai Ya Hamdi da Happy."

Inna Luba ta ware idanu a tsorace "Hafi? Mutum ne?"

Yadda yake murna kai ka ce shi ne angon mata uku. Gyarawa ya yi yadda za ta gane da kyau.
"Ya Taj. Shugaban inda Abba yake aiki yanzu."

Cikin Hamdi wata irin ƙullewa ya yi. Taji ya saki lokaci guda yana neman tsinkata a gaban mutane. Duk da haka danne shi tayi da hannu biyu.

"Kai ka san bana son wasa irin wannan. Wace Hamdin kake nufi?"

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now