8

1K 156 37
                                    

RAYUWA DA GIƁI  8


Batul Mamman💖


***

Zazzaɓin gaske ne ya kama Ummi tun bayan ta saurari wayar Vice principal da mahaifinta. Aikin gama ya riga ya gama. Bayan ya ajiye wayar wani irin kallo ya yi mata ya jinjina ƙarfin halinta. Sannan ya ƙara tabbatarwa mace abar tsoro ce komai ƙanƙantarta.

"Wannan mutumin shi ne mahaifinki Ummi?"

Kai a ƙasa ta ce "eh."

"Wanda yake zuwa kuma ya kuke da shi? Kuma me yasa ki ka zaɓi faɗin gaskiya yanzu?"

Shiru tayi babu amsa tunda Hamdi ma taƙi magana me zai sa ta fara?

Rai a ɓace ya ce "To kuwa ki kwana da sanin cewa yau ce ranarki ta ƙarshe a makarantar nan. Don ban ga wani dalili da zai hana a kore ki gobe ba ko da kece mai gaskiya. Sannan dole zan kira shi domin a warware komai gaban mahaifin naki."

Yanzu ma kasa cewa komai tayi sai faman saƙe-saƙen neman mafita. Sannan a gefe guda babu irin ashar ɗin da bata saukewa Hamdi ba. Da farko ta san kawai jindaɗin samun mai yi mata bauta a makaranta tayi da sanin sirrin Hamdi. Yanzu kuwa wata irin tsana ce da za ka ji komai ma za ka iya yiwa mutum take ji akanta. Har lokacin bata saduda ba don tana jin da Hamdi tayi mata biyayya ta bata ruwan nan da bata ga wannan lokacin ba. Haɗuwarta da Baba Maje gobe ba ƙaramar tarzoma zai tayar ba.

"Ki tashi ki fice min daga office nace."

Tsawar VP ta dawo da tunaninta inda take. Ta miƙe za ta fita sai kawai wani tunani ya zo mata. Guntun murmushi ta saki wanda har ga Allah sai da ya VP ɗin tsoro da shakku akanta.

Wurin ƙawarta konace babbar ƴar korarta Widad taje da saurinta. Sun gama nasu punishment ɗin na yau sai kuma washegari da ake sa ran samun ruwa. Za su wanke banɗakunan makarantar kaf har na malamai. Ga kuma sharar harabar makaranta da cire ciyayi.

Widad na ganinta ta tashi zaune daga kwanciyar gajiyar da tayi. Ummi ko kallon arziƙi bata yiwa  ciwon dake babban yatsan Widad na ƙafa wanda taji a wurin faɗan ɗazu ba. Kuma ta gan shi sarai amma ba shi ne a gabanta ba.

"Bani wayarki in kira Uncle B"

"Kuna can aka zo inspection ɗin bazata tun bayan an nuna wayarki a wajen principal. Yau wayar da aka fitar daga ɗakin nan tafi ashirin."

Muguwar harara Ummi ta jefeta da ita sannan ta yatsina fuska ta ce mata "banza, me yasa ko a pant baki ɓoye ba?"

"Korarmu aka yi waje bamu san dalili ba. Sannan aka yi searching ɗinmu da ɗai-ɗai." Widad ta amsa tana mai ɓoye zafin zagin da halin ko in kula da Ummin ta saba nuna mata.

Plan ɗinta na farko ya faɗi tun kafin ta aiwatar. Dama niyarta ta faɗawa sugar daddy ɗin nata da take kira Uncle B idan an nemi numbarsa kada ya yarda ya zo. Shawara ta biyu kawai za ta ɗauka. Idan an zauna gobe kawai ta tada aljanu kuma duk yadda za ayi da ita kar ta yadda ta dawo daidai sai an koma gida. In ya so ko kasheta za ayi gara ayi a can.

***

A hanyarsa ta zuwa tasha cikin adaidaita sahu Abba ya kira ƙaninsa a waya. Hankalinsa ne sam bai kwanta da zuwa makarantarsu Hamdi ba. Yana son kare martabar ƴaƴansa daga dukkan abin da zai iya janyo musu raini daga mutane. Ya tuna wani lokaci da Yaya Hayatu kamar yadda yake kiran Alhaji yayi masa wata magana a baya.

"Habibu gaba nake jiye maka. Lokacin da za ka ji kunyar nuna kanka a wasu wuraren saboda kana ganin kamar darajarka bata kai ba. A lokacin ilimi ko rashinsa, talauci ko arziƙi ba su ne za su zame maka shamaki ba. Wannan mazantakar da kake gudu da Allah Ya karramaka da ita ce za ka so a baka aro ko na awa guda ne."

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now