25

1.6K 181 103
                                    

RAYUWA DA GIƁI  25



Batul Mamman💖




Taurin zuciya ya hana Hamdi kukan da sauti. Sai hawaye kawai da ajiyar zuciya. Ji take kamar ta buɗe ido ta ganta a gaban Yaya. Auren za ta ce ta fasa da gaske. Gashi dai zuciyarta tana ƙaunarsa. Ƙauna da son da har yanzu bata taɓa faɗa masa ba saboda kunya da jan aji na mata. Sai dai tayi abin da zai gane shi ɗin mai matsayi ne babba. Tana tanadin kalmominta masu tsada zuwa lokacin da za su kasance a muhalli guda. Abin da ya gagareta fahimta bai wuce yadda ta rufe ido ta iya kiran shi munafuki ba. Haƙiƙa duk wanda ya santa zai yi mata shaidar tsiwa. Amma rashin kunya irin wannan kuma ga mijin aure, abu ne da ita kanta bata taɓa kawowa zata yi ba. Kuma har yanzu yadda take jin son nasa haka kuma wani irin haushinsa yake cin zuciyarta. So take kawai ya sake yin wani abin ita kuma ta cigaba da faɗa masa abin da zai ji haushi.

Shi kuwa Taj ya ma rasa me yake yi masa daɗi a duniya. Juya mata baya ya yi ya runtse idanunsa. Sai ya yi yunƙurin juyawa yaga halin da take ciki, sai yaji zuciyarsa tana tuna masa kalamanta a gare shi. Ransa ya ƙara ɓaci har wani tafasa zuciyarsa take yi. Muddin za ta cigaba da yi masa rashin kunya yana kyautata zaton zai iya yi mata dukan da sai an ɗagata....Duka??? Ai ko ƙannensa mata ba za su yi masa wannan shaidar ba yayi saurin kwaɓar kansa. Me ya kai shi marinta?

A hankali ya juya su ka fuskanci juna. Kumatunta ya yi shatin yatsunsa raɗau. Gabansa ya faɗi da ganin aika aikar da ya yi a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Wayarsa ya ɗauko ya kira Sajida don tabbas ba zai iya kai Hamdi gidan a haka ba.

Hamdi na cikin yanayin ɓacin ran nan taji yana cewa ba zai sami damar kaita ba. Da haka ta gane da wa yake wayar. Bata san me Sajidan ta ce ba ya bata wannan amsar.

"Lafiyarta ƙalau, kawai dai tana cikin yanayin da bai kamata taje ko ina ba. So please ki min alfarma kada ki faɗa a gida cewa bata zo ba."

Kallon mamaki Hamdi ta fara yi masa. Kafin kuma cikin fushi ta fara neman karɓe wayar. Za ta soma ɗaga murya ya danne wayar da kafaɗarsa ita kuma ya sanya hannu guda ya rufe mata baki. Ɗayan kuma matseta ya yi a jikinsa da shi. Ya yi ɗan murmushi da Sajidan ta soma cewa ta gane duk da muryarta ta bada ita.

"Ba fa abin da kike tunani bane wallahi. Fitowar ce dai kawai ba zan iya ba."

"Ko dai bata da lafiya ne?"

"She is fine. Bari tayi miki magana."

Kallon gargaɗi ya yi mata kafin ya cire hannunsa daga bakinta a hankali ya kara mata wayar a kunne. Ta ɗaga jajayen idanuwanta ta dube shi. Kalmar 'please' ta karanta a laɓɓansa. Ranta sosai yake ƙuna.

"Ya Sajida."

"Alhamdulillah" hankali kwance tunda taji muryarta ta ƙara da cewa "asha soyayya lafiya."

Da sauri Hamdi ta yanke shawarar fađa mata me ya faru.
"Mar..."

Bai bari ta ƙarasa ba ya cire wayar. Ta buɗe baki za ta yi magana da ƙarfi yadda zata ji ya zauna tare da ita a jikinsa ya turata ƙuryar kujera yana girgiza kai. Dolenta tayi shiru kawai sai harare harare bayan ta tattare ƙafafunta ta cure jiki waje guda.

Sam ba zai yarda a ganta da shatin nan har a fara tambayoyi ba. Muryarsa ya gyara ya ce
"Don Allah Sajida. I realy need this favour from you. Kin san dai ba zan cutar da ita ba. Duk da tana ta rigimar sai na kawota."

"Subhanallahi. Ya Taj me ya kawo wannan maganar? In sha Allah babu mai ji. Ita kuma kada ma ka biye mata."

"To nagode."

Akan centre table ɗin wurin cushion chairs ɗin mai kyau na gilas ya ajiye wayar ya fuskanceta. Zuciyarsa tana ta kai komo wurin faɗa masa ƙarya da gaskiya. Ya rasa tudun dafawa guda ɗaya. Hannunsa ya kai kumatunta zai taɓa tayi saurin karewa da nata,tana mai sadda kai ƙasa. Bai kulata ba ya riƙe hannun nata ya kai ya taɓa inda ya yi marin. Baya jin za ta kai shi jin ciwon wannan abu.

RAYUWA DA GIƁIOn viuen les histories. Descobreix ara