2

1.5K 154 15
                                    

RAYUWA DA GIƁI 2

Batul Mamman💖


Banda hotuna har sautin muryarsa Ummi ta ɗauka daidai inda yake kiran Hamdi ta kawo salad. Tana jin kiran ba amma saboda tsoron yanayin da za ta tarar da fuskar Ummi na farincikin samun lagonta sai ta kasa amsawa.

"Abba bari na kira ta." Zee ta miƙe tsaye.

"Matso mu su da plates bari naje."

Tashi ya yi ya tattare gefen jallabiyarsa ya riƙe da hannu ɗaya ya fita. Ya samu ta gama haɗa komai ta lulluɓe da clig (farar leda ta rufe abinci) kamar yadda ya koya mu su. Haɗin ya yi kyau gwanin ban sha'awa. Ya murmusa cikin jindaɗi yana ɗaukan tray ɗin. Ko ƙanƙani bai san wani abu girman kai ba musamman a tare da iyalinsa.

"Allah Ya yi albarka Hamdi. Mu je a ci abinci."

Jingina tayi da sink ta juya masa baya kamar wani abu za ta wanke ta gyaɗa kai. Amsawa da baki zai iya ankarar dashi kukan dake barazanar ɓalle mata.

Shi kuwa kamar ya sani ya ajiye tray ɗin ya juyo da kafaɗunta.
"Hamdi?"

Ai suna haɗa ido sai kawai ta fashe da kuka. Zuciyarta tamkar ta fashe saboda baƙincikin da take ji. Wani abu mai masifar ɗaci ya dinga kai komo a cikin ƙirjinta. Duk gidan tana da yaƙinin tafi kowa takaicin fita tsatson bawan Allahn nan. Ranta yana ƙyamarsa. Albarkacin karatun addini yasa ta daina danganta shi da munanan kalmomi da fata a zuci kamar yadda take yi a baya. Asalin da mutane ke tutiya dashi Yaya ta janyo sun rasa ta da haifesu tare da tubabben Ɗandaudu. Mutumin da har yau idan aka yi rashin sa'ar gamuwa da tsofaffin abokansa sai kaji ana kiransa Simagade.

Hankalinsa tashi yayi da ganin hawayenta ya dinga tambayarta damuwarta. Da bata ce komai ba ya yi yunƙurin rungumeta domin rarrashi amma sai ta banƙare jiki ta ja baya. Dama can ta saba yi masa haka don shi tarairayar yara sai dai wani ya koya a wurinsa. Na yau ne da ya sanya masa shakku tunda ya san ta kan bari sai dai ta zare jiki da wuri. Kallon tuhuma ya bita da shi sai ta wayance ta ɗago hannun da ta yanke ta nuna masa.

"Ya Salam" ya ce da ƙaramar muryarsa "Sannu. Jeki falo ki jira ni."

Tray ɗin salad ɗin ya ajiye ya fita cikin ruwan nan mai ƙarfi ya shiga ɗakinsa. Haƙƙin iyaye da a kullum shi ne jigon dake hanata fito masa da zahirin abin da take ji game da shi yasa ta ɗauki tray ɗin. Idonta da na Ummi su ka haɗu taga abin da take gudu muraran a tare da ita.   Jikinta ya sake yin sanyi.

Sallamar Abba ta dawo da ita duniyar mutane. Ya zauna akan hannun kujera ya ce ta kawo hannunta. Ɗan akwati gare shi irin na gidan ƴan boko da ya adana magunguna da kayan taimakon gaggawa. Ya umarci Zee da zubawa kowa abinci shi kuma ya zauna bawa ƴarsa kulawa. Spirit ya dangwala a jikin auduga ya goge ciwon. Ga azabar zafi saboda ba ƙaramar yanka bace amma ko uhumm ta kasa cewa. Allah Ya sani zafin da take ji a zuciyarta yafi raɗaɗin ciwon. Saboda yadda ta ƙyamaci rayuwar mahaifinta bata ƙaunar gabaɗaya abokan sana'arsa. A son ranta namiji ko ruwan zafi aka ce ya dafa ya dawo ya ce ya ƙone saboda rashin iyawa. Namiji mai shiga kitchen ba zai taɓa yi mata kwarjini ba balle har taga ƙimarsa.

Dressing sosai ya yi mata ya kawo auduga ya ɗora ya manne ta da plaster. Gwani ne sosai ta wannan fannin wurin son ganin komai ya tafi daidai kamar wani bature. Ire iren abubuwan nan harda Abban da yasa su ke kiransa kamar ba talakawa ba duk bata so. Cikakken namiji bahaushe a wajenta ai Baba ake kiransa ba wani iyayin Abba ko Daddy ba.

Kowa sannu yake mata tana amsawa da ka. Da kuma wannan damar ta samu ta gudu ɗaki ta kwanta. Ba ita ta sake fitowa ba har sai da baƙin su ka tafi bayan Iyaa da su Ummi sun leƙo sun mata sallama.

***

"This is crazy Taj. Waye yake tattara duka ƙwansa ya sanya a kwando guda?"

Wata kamilalliyar dattijuwa sanye da doguwar rigar bacci da ƴar hula ta furta da takaici. Huci take cikin ɓacin rai tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune yana murmushi kamar abin da take faɗi da wani take a talabijin ba shi ba.

RAYUWA DA GIƁITahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon