4

1.1K 132 8
                                    

RAYUWA DA GIƁI 4

Batul Mamman💖

***

Manyan gidan a wannan rana basu ga bambancin dare da wuni ba. Kusan babu wanda ya runtsa tsakanin maigidan da matansa. Abin da yake faruwa baƙo ne a wurinsu. Basu saba da rigima ba sai gashi dare ɗaya ana gab da samun gagarumar ɓaraka.

Ita dai Inna daga sallar asuba ta fake da ɗora kunun karin kumallo ta sauko. Bata zame ko ina ba sai ɗakin Mama. Akan sallaya ta sameta idanu sun kumbure. Jikinta a mace ta fita ta kira Umma da Hajiya su ka dawo ɗakin tare. Kai a ƙasa ta labarta musu ainihin yadda su ka yi da Alhaji jiya.

"Ni wallahi ba da wata manufa nayi maganar ba. Na tashi gidanmu babu ƴan uba amma tsakanin yayyena sai babba ya kau ta hanyar aure ko barin gari sannan mai bi masa yake ɗaukar ragamar gidan. Ban san gudun kada a gaba yaran nan su sami raunin zumunci a dalilin haka ni zai jawowa matsala ba."

Umma ta kalleta babu wannan fara'ar ta kodayaushe
"To amma me ki ka gani a gidan nan da yasa ki tunkarar Alhaji da zancen? Cikinmu wata ta canja miki ne kuma ta nuna saboda kusancin Alhaji da Taj tayi haka?"

"Ko kusa. Nayi masa magana ne kawai akan ya dinga nuna sauran ƴaƴan musamman Ahmad da Kamal da su ke manya kamar yadda ya nuna shi."

"Maganar girkin fa?" Umma ta sake tambaya don ita so take a warware komai.

"Yadda ba ku ɗauke shi laifi ba nima ban ɗauka ba. Wallahi ko kusa ni ban yi masa zancen da ya shafi haka ba. Ba gashi a ranar girkina ya yi miyar ba?"

Wata tambayar Umma ta so yi Mama ta katseta.

"Ni ban sakawa raina komai ba. Jiya Hajiya ta ƙara min nasiha akan idan muka bari wannan maganar ta girmi haka to zaman gidan nan zai daina yiwa kowaccenmu daɗi. Saboda haka zance ya wuce."

Inna sai godiya da farinciki. Bata fita daga ɗakin ba sai da su ka koma wata hirar ana ta dariya. Da rana su ka kira Taj cikin lumana su ka rarrashe shi akan ya yar da wannan buri don ba mai yiwuwa bane. Mama tayi masa nasiha sosai akan yiwa iyaye biyayya.

"Ka cigaba da bin Alhaji kasuwa ranakun da babu makaranta amma daga yanzu tsakaninka da kitchen sai hange. Don Allah kada ka bari zancen nan ya koma tasowa a gidan nan."

Nuna musu ya yi kamar maganar ta mutu, ashe suma tayi.

Shi da Kamal sun kammala sakandire suna da shekara goma sha shida da sakamako mai kyau. Alhaji kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha ranar da su ka kawo takardunsu. Dama tuni ya tura Ahmad ƙasar India inda yake haɗa degree ɗinsa a fannin Computer Science. Zaɓi ya basu tsakanin Dubai, India ko China. Burinsa su zaɓa cikin ƙasashen da su ke cibiyar kasuwanci.

"Alhaji mun fi son zuwa wurin Yaya." Cewar Taj.

Kamal ya yi Taj wani irin kallo sannan ya ce "ni dai Dubai."

Kallonsu ya yi a tsanake. Da wuya zaɓinsu yake bambanta. Bai kuma saka ran samun haka ba ta ɓangaren karatun da zai rabasu na ƴan shekaru.

"Anya kuwa Happy da Happiness za su iya rabuwa na shekara huɗu? Ku dai sake shawara ku zaɓi waje ɗaya."

Kamal ya kalli Taj da sanyin jiki. Ya ɗauka sun gama magana akan za su zaɓi Dubai. Burinsa ya koyo larabci banda karatun da za su yi. Sannan idan da faraga ya sami wani balaraben malamin ya danɗaƙi haddarsa da kyau ta ƙara zama. Kuma lafiya ƙalau Taj ɗin ya amince har da cewa shi ma zai yi. To me ya kawo wannan sauyi?

Alhaji bai ce musu komai ba amma ya fahimci akwai matsala tsakanin yaran. Sai bayan kwana biyu ya kira kowannensu gefe don jin me yake faruwa. A yadda ya fahimta zaɓinsu bai zo ɗaya ba. Kuma kowanne yana so ɗan uwansa ya bi ra'ayinsa. Kamal sai daɗa kwaɗaitawa Taj koyon larabci yake. Shi kuma duk da yana so amma haka kawai zuciyarsa tafi kwantawa da India. Sulhu ya yi musu da alƙawarin kowa zai sami inda yake so.

RAYUWA DA GIƁITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang