24

1.6K 174 103
                                    

RAYUWA DA GIƁI  24


Batul Mamman💖





Lallai Alh. Mukhtar ɗinnan ya gamu da sharrin Mami shi ne abin da Alhaji ya fara rayawa a ransa bayan sun gama waya. Yadda ya dinga koro bayani akan irin son da ƴarsa take yiwa Taj da fatan amincewar Alhajin don ayi aurensu  kai ka san kan ba ƙalau ba. Shi dai yana son ƴaƴansa, amma fa yana ganin babu ƴar da ta isa ta saka shi zubar da mutumci haka a gaban tsohon mijin matarsa. Irin waɗannan abubuwan ya fara gani da burinta na fin kowacce mace matsayi ta kowacce hanya yasa shi sakinta. Yana da labarin yadda matan Alh. Mukhtar biyu su ka fita bayan an aurota. Kuma duk wadda ya ƙaro bata jimawa za ta yi waje ita ma.

Zama ya gyara da ya tuna yadda ya  ce masa ya amince kai tsaye. Fakewa zai yi da guzuma ya harbi karsana. Ya san a taurin kai irin na Taj akan ya auri Salwa ya faranta  masa gara ya saki Hamdi. Ana yin sakin da kansa zai ce masa ya janye batun auren. Duk da a iya saninsa Salwa yarinya ce mai saukin hali. Babu mamaki sirrin zuciyarta ta sanar da Mamin ita kuma tayi amfani da raunin ƴar ta ɗorata akan hanya mara ɓullewa irin wannan. Tsigar jikinsa har wanu tashi tayi da ya yi addu'ar Allah Ya tsare shi surukuta da Mami da lusarin mijinta kamar yadda ya laƙaba masa suna.

Bai ga alamun Habibu Simagade zai iya wani kataɓus wurin raba yaran ba. Yanzu da ya sami dama shine zai yi amfani da ita. Ɗansa yake muradi ya dawo gida. Amma ba tare da iri ko jinin ɗan daudu a tare dashi ba. Saboda rashin son ganin Hamdi ranar da aka ce za ta zo gidan zamansa ya yi a kasuwa har ƙarfe tara. Shi ba abin ya ce kada ta zo ba matan gidan su soma tijara. Ya fahimci yanzu kamar ma jira suke ya ce kule su ce masa cass.

Ahmad ya nema da yazo gida yana son ganinsa da daddare. Bayan ya taso daga office kai tsaye can ya wuce. Alhaji ya keɓe dashi yana tambayarsa alaƙar Taj da Salwa tunda duka a gidansa su ke.

Tsoro ne ya bayyana a fuskar Ahmad.
"Alhaji wata maganar ka ji?"

"Ya zan yi maka tambaya ka amsa min da tambaya?"

Da sauri ya bashi haƙuri tare da amsa tambayar da ya yi masa.
"Babu komai a tsakaninsu amma kuma ba faɗa su ke yi ba. Shi Taj ma bai fiye zaman gida ba ai saboda kullum su ke buɗewa."

"Babanta, Alh. Mukhtar sunansa ko?" Alhaji ya faɗi da irin rashin damuwar nan.

Ahmad baya jindaɗin yadda ake magana akan Salwa yanzu. Rannan ƴan uwansa ne su ka yi ana ta dariya. Yau kuma Alhaji ke tambayar sunan babanta kamar wani abin gudu.

"Sunansa kenan."

"Ya kirani yana roƙon na amince Taj ya aureta."

Maganar ta dake shi sosai "Roƙo kuma Alhaji?"

"Roƙo mana. Ya tabbatar min ita take son sa. Kaima yanzu ka ce babu komai tsakaninsu. To me zai sa ita babar taku ta amince harma mijinta ya kirani?"

"Zan yi mata magana Alhaji." Ya girgiza kai "Gobe in sha Allah zan mayar da ita Bauchin. Idan ma mijin ne su sama mata a can." Tashi ya yi zai tafi. Alhaji ya ce ya dawo.

"Babu daɗi mutum ya nemeka akan wata alfarma ka nuna masa baka so. Saboda haka na faɗa masa na amince. Saƙon da nake son baka shi ne ka sanar dasu cewa bana so komai ya wuce wata ɗaya indai da gaske su ke."

Yana magana ne yana kallon yanayin Ahmad. A ransa kuma yana addu'ar Allah Yasa ɗan nasa ya yafe masa. Da gangan yake maganar a haka saboda yana so idan Ahmad ya tashi kai saƙon ya nuna musu shi fa bai ɗauki maganar da mahimmanci ba. Sannan baya ɗokin haɗa zuri'a da ƴarsu. Ya sami wannan canjin ra'ayin ne bayan wani nazari da ya yi. A matsayinsa na uba sai hankalinsa bai kwanta da ya yi amfani da ƴar wani domin biyan buƙatarsa ba. Idan komai ya tafi yadda yake so ya dawo ya ce da Taj kada ya auri Salwa me kenan ya yi? Shi mai ƴaƴa da jikoki mata ya dace ya tozarta ƴar wani haka? Gashi saboda sanin halin babarta ya tabbatar idan ya yi sake ta auri Taj sai sun mayar masa ɗa abin wasan yara.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now