11

1.1K 172 28
                                    

RAYUWA DA GIƁI  11


Batul Mamman💖



Yadda ya gaisa da kowa da zai wuce haka ya tsaya su ka yi musabaha da wanda ya rako su. Sannan ya ɗagawa Taj da Kamal hannu yana ɗan ranƙwafawa kamar yadda ya gaisa da sauran mutanen da su ka gani.

"Ƴan samari barkanku dai. Ya sanyi sanyi? Ya ayyuka? To Allah Ya yi jagora." Ya dubi mutumin da da ya yi mu su rakiyar ya ce "na barku lafiya."

"Dakata Mal. Habibu. Waɗannan fa kai su ke nema."

Tsayuwa ya yi ya sake kallonsu sai dai bai tuna taɓa haɗuwa dasu ba.

"To Allah dai Yasa lafiya" ya ce muryarsa na raguwa saboda rashin sanin ko ba da alkhairi su ka zo ba.

Kamal ne ya amsa masa "lafiya ƙalau." Sannan ya gabatar da kansa da Taj.

Jin cewa Taj chef ne kuma a yanzu haka ginin restaurant yake sai Abba ya sami kansa da daina saurin zuwa uzurin da ya fito dashi. Zancen bai wuce fita nema ba dama.

"Dama nayi tunanin maganar ba za ta wuce ta ɗaukarka aiki ba. Shi yasa na rako su. Bari na wuce."

Abba ya yi masa godiya sosai sannan ya nunawa su Taj gidansa. "Ko mu ƙarasa daga soro mu zauna?"

A duk lokacin da ya yi magana sai Kamal yaji zuciyarsa ta karye. Allah Ya sani a yau ya daina ganin baƙin Alhajinsu. Tabbas da wannan rayuwar Taj ya faɗawa da shi ma sai ya yi kuka ba iyayensu ba. Ta yaya zuciya za ta jidaɗin ganin namijin da ya cika a halitta yana irin wannan muryar? Don ma bai san lanƙwasar jikin da sauƙi yanzu ba.

Gidan su ka bi shi. Daga soron ya ɗaga murya yana ta kiran sunan Zee amma sai da ya yi kamar sau biyar su ka ga ƴar budurwa ta fito a guje. Don shi Kamal ji ya yi kamar ya taya shi kiran saboda muryar ba ta tashi yadda ya dace.

"Abba yi haƙuri ban ji ba ne."

Mutanen da ta gani tare dashi ne yasa ta saurin komawa da baya don bata fito da lulluɓi ba. Ta bayan ƙofa ta gaishe su. Su duka biyun yadda tayi ɗin ya burge su sosai.

"Tabarma za ki kawo da ruwa."

Bata jima ba ta dawo da hijabi a jikinta ta shimfiɗa tabarmar. Abba ya sake gaisawa dasu sannan ya buƙaci jin neman da su ke yi masa.

"Kamar yadda ɗan uwana ya faɗa maka gidan abinci nake ginawa. To sai na sami labarinka a wajen mutane. Duk da ba haka ake so ba ance ka rasa wurin sana'arka."

"Eh. Amma yanzu ma haka wani waje zan je dubawa. Idan mun daidaita sai na kama haya."

Babu wani dogon tunani ko shawara Taj ya ce "hayar kafi so ko za ka iya aiki tare dani?"

"Kai da baka gama gini ba Happy? Zai yi ta jira ne har lokacin?" Kamal  ya yi saurin katse shi.

"Me ya kawo ku wurina tsakani da Allah?" Abba ya tambaya da sakin fuska.

"Aiki nake so mu yi tare amma wurin nawa da saura kamar yadda ya faɗa maka. Ina so nayi recruiting ma'aikata da wuri kafin na gama ginin."

Kamal da ya yi zaton ganinsa kawai su ka zo yi sai yaji hankalinsa bai kwanta ba. Me yasa Taj yake neman abin da zai ƙara nesanta shi da Alhaji? Ina shi ina aiki da wannan mutumin daga jin ance baya aiki?

Abba ya ƙare musu kallo sai ya yi murmushi. Da alama shawararsu bata zo ɗaya ba don yaga irin kallon da Kamal yake yiwa Taj.

"Samari nagode amma ina mai baku haƙuri. Ina da mata da ƴaƴa huɗu. Zama haka a yanzu ma yana damuna balle kuma na wasu watanni. Sannan ina da ma'aikata biyar da har yanzu dani su ka dogara."

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now