12

1.1K 145 24
                                    

RAYUWA DA GIƁI  12

Batul Mamman 💖

Wannan shafin yana ɗauke da tallan LUCIOUSBITES gidan  kashe ƙwalama. Mazauna garin Abuja ga taku ta fito da kanta ba saƙo.

Taron biki, suna, conference, seminar ko reunion ne? Ko kuwa sha'awar kashe kwaɗayi ce ta tashi? To ku sha kuruminku. Hauwa aka luciousbites.ng ta fito domin fitar daku kunya a ko ina.
Domin ƙarin bayani kuna iya tuntuɓarta a kan wannan layi 08174821831.


***

Da gaske ciwon kai ke damun Taj saboda bai iya sanya abu a rai ba. Ya so ƙwarai ya ja Abban Hamdi a jiki. Ba don neman soyayyarta ba, wannan da kansa zai yi ba ya buƙatar taimakon kowa sai Allah. Mahaifinsa yake son nunawa a rayuwa kowa da ƙaddararsa. Kuma  a kowacce sana'a indai ba addini ne ya haramta ta ba, akwai mutumin banza da nagari. Don al'ada ta ƙyamaci wani abu ba shi yake nufin yinsa laifi bane. Sannan uwa uba akwai uzuri ga ƴan Adam domin ba kowa ke dawwama cikin saɓo ba.

A ganinsa rashin aikin Abban Hamdi wata hanya ce ya samu da zai iya sako shi cikin tasa sana'ar. Idan Allah Ya sanya musu albarka kasuwa ta buɗe Alhaji zai iya fahimtar kowanne bawa akwai hanyar arziƙinsa. Sannan ko iyaye ba sa so indai Allah bai haramta ba sannan ɗan bai kasance mai saɓawa kowa ba, albarka za ta iya binsa duk inda yake.

Ƙarar wayarsa ce ta tashe shi daga kwanciyar da ya jima yana yi. Sunan Salwa da ya gani ya sanya shi yin tsaki. Ita bata san gudunta yake yi ba? Har yau yana mamaki da bata yi tunanin kamar yadda mata ke killace kayansu na ciki haka kowanne namiji da ya san mutumcin kansa yake yiwa nasa ba. A iya saninsa ƙiwa da rashin son aikin namiji ba zai sa ya bawa ƙanwarsa shaƙiƙiya wankin ƙananan kaya ba. Ballantana kuma  wadda babu wani abu da ya haɗasu.

Bari ya yi kiran ya katse sannan ya kirata.

"Don Allah ka buɗe min ƙofa na manta muƙullina a ciki."

Falo ya fito sanye da dogon wando na sanyi ruwan toka da farar shirt. Ya buɗe mata jamlock ɗin ya juya zai koma ɗaki sai ta kira sunansa.

Tun ranar da ta gyara masa ɗaki da faɗan da Ahmad ya yi mata ta rage kuzari da karsashi a komai. Fargabarta ita ce ɓacin ran da ta gani tare da Taj da kuma shawarar da Ahmad ɗin ya bata akan ta cire shi daga ranta. Da za ta iya da tun kafin ta zubar da ajinta ta cire shi ta ƙarfin tsiya tunda ta fahimci bata gabansa ta fuskar da take so.

Sake kiransa tayi da bai juyo sosai ba.

"Ya Taj don Allah ka yi haƙuri akan abin da ya faru rannan. Na fahimci kuskurena."

"Ya wuce, kada ki damu."

Fasa tafiya ya yi da ya tuna ƙanwar Ahmad ai ƙanwarsa ce shi ma. A matsayi guda duk su biyun su ke zaune a gidan. Shi yasa yaga dacewar ya bata shawara.

"Ko don gaba ki kiyaye irin wannan. Ba ni ba, ko Yaya ki ka wankewa undies bana jin za ki burge shi." Kai ta sunkuyar sai ya yi murmushi "ku mata ba kwa son a taɓa koda jakarku. So just imagine ace ni nayi miki wannan karambanin. Will you realy be happy that I helped?"

Kunya maganar tashi ta bata. Ta rufe ido ta shige ciki da sauri tana mayar da numfashi. Da tunanin yadda ya yi maganar a tausashe ta ƙarasa ɗaki. Sai da cire kaya za ta shiga wanka ta kuma tariyo zancen sai taji faɗuwar gaba. Shin magana ya yaɓa mata ko kuwa ya sauko ne?

Domin tabbatar da matsayin maganar da sai ta tura masa SMS da yamma da ya fito falo suna hira da Ahmad. Daga kitchen ta leƙo bayan ta tura tana kallonsa ya duba saƙon, ya kuma rubuta reply. Da wani irin sauri ta koma ciki ta buɗe. Nata ta fara bi inda ta rubuta masa saƙo kamar haka.

(Ya Taj nagode kuma ina mai sake baka haƙuri. If I am forgiven please give me a chance to be your friend.)

Shi kuma ya rubuta wannan amsar.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now