33

1.1K 120 13
                                    

RAYUWA DA GIƁI  33



Batul Mamman💖




This page is sponsored by spicesbyMrsghaleetk....yep, MRS GHALEE TK. Nace ba, wai kina cikin masu cewa girki da spices baya daɗi? Ko kuwa kin saba saya kina bari ya siƙe a kitchen saboda baki gane ɗanɗanon da yake bayarwa ba?

Albishirinki, Mrs Ghalee TK dai za ta yi Ramadan promo. Dama ce ta samu gareki wajen sayen ingantattun kayan girki masu tallafawa cefane musamman a wannan marra ta tsadar kayan abinci. Ke dai ƴar uwa, harma da ɗan uwan da ya saba taimakawa iyayensa ko matarsa, ko kuma mai son burge iyali, ku yi tanadi don Mrs Ghalee TK ta zo da rangwame domin gyara tukwanenku. Ku sai ku garzaya ku nemeta akan wannan layin ta manhajar whatsapp ko kiran waya 08032834178.

Taku ce Batul Mamman, ganau akan kayayyakin da nake tallata muku.


***

A cikin yanayin ciwo da gajiyar jiki Kamal ya buɗe idanu ya miƙa hannu zai ɗauki wayarsa. A gadon asibiti yake inda yake samun kulawa ta musamman. Da yake dokar asibitin ba a zaman jinya, shi kaɗai ne a ɗakin. Alhaji da su Ahmad suna hotel kusa da asibitin. Tafiyar just ƙafa ke kawo su. Tare dashi su ke wuni sai takwas na dare idan an buƙaci duka baƙi da masu ziyara su fita sannan su ke tafiya. Kwanaki goma aka bashi ya gama shan magani da allurai kafin a fara dialysis.

"Happy lafiya dai ko?" Ya ce cikin bacci da firgici domin kuwa ukun dare harda kwata lokacin.

Kamar an tsunkuli Taj ya ɗaga kai ya kalli kyakkyawan agogon bangon falon. Baki ya buɗe gami da girgiza kai.

"Don Allah Happiness kayi haƙuri. Kasan Allah ban duba time ba. Ashe past one. A nan uku ta wuce ko?"

Kamal ya gyara zama ya ce "Eh...mene ne ya faru? Haka kawai ba za ka manta lokaci ba."

"Gobe sai muyi magana in sha Allah. Am very sorry." Taj ya ce har zuciyarsa.

"Taj" Kamal ya kira shi da ɗan ƙarfi "me ya faru?"

Roƙonsa Taj ya fara yi akan ya jira safiya don har ya katse kiran amma ya sake kiransa. Su ka ɗan yi ja'inja ɗinsu sannan Taj ya faɗa masa abin da yake faruwa dashi game da ɗaukewar ɗanɗano da jin ƙamshi ko wari wasu lokutan.

"Zuciyata tana bani Covid ce. Nayi browsing naga ɗaukewar sense of smell da taste suna cikin symptoms ɗinta. Ni bana mura amma bayan magrib ina ƙirgawa sau bakwai Hamdi tayi atishawa."

Kamal yayi ƴar dariya "sannu Doctor."

Taj ya ɓata rai "Happiness its not funny."

"Na sani. Shi yasa nake mamaki da kana zaune a gida ka yankewa kanka cutar dake damunka."

Murmushi ne ya kama shi. Tabbas asibiti ya kamata yaje amma fargaba ta hana. Ba kuma kansa yake jiyewa tsoro ba. Idan ta tabbata yana da corona shikenan Hamdi ma ta samu. Daga tarewa ya haɗata da ciwo.

"Gobe zan je in sha Allah. Thank you and sorry."

Sai da safe suka yiwa juna. Kamal ya ce yana jiran jin sakamakon idan ya dawo daga asibitin. Da ya koma ɗakin  a dunƙule waje guda ya sami Hamdi. Ta dawo tsakiyar gadon tana baccinta hankali kwance. Sama ya kalla ya sake yin addu'ar da ya wuni yana yi. Allah Yasa ba covid bace. Idan kuma ita ce yana fatan Hamdi bata samu ba. Sai dai abin da kamar wuya. Yadda su ke manne da juna ana amarci ai taimakon Allah ne kawai zai hanata kamuwa. Kwanciya yayi a can gefe. Ko minti biyu bai yi ba yaji Hamdi a jikinsa ta ɗora rabin kanta a ƙirjinsa. Wani ɗan murmushi yayi ya sake shige mata har yayi bacci.

***

Yawan kallon wayar da Kamal yake yi ne yasa Alhaji tambayarsa kira ko saƙon wa yake jira. Shi kuwa ya faɗa masa yadda suka yi da Taj a waya.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now