22

1.5K 208 89
                                    

RAYUWA DA GIƁI  22



Batul Mamman💖



This page is sponsored by Scentmania by Sana. A Kano take, amma ƙamshi babu ruwansa da gari ko ƙasa. Wuyarta ciniki ya faɗa. Za ku sami undiluted oil perfumes ɗinku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haɗa kwalabe daban daban ki gigita waɗanda ya halatta su ji ƙamshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeta a wannan layin 07065525409.

Ko sakan 30 ba ayi ba tsakanin fitar Salwa da shigarsu ciki Taj ya turo gate ɗin. Kamal ya yi mamakin ganinsa tsaye daga waje. Shi kuwa yafito shi kawai yake da hannu. Cewa Hamdi ya yi ta ɗan jira shi. Ko kallon Taj ɗin bata yi ba domin ranta a ɓace yake. Bata son yanayin da take jin zuciyarta a ciki. So take ko dai taga dawowar Salwa ciki ko kuma ita tayi hanyar gidansu.

Kafin Kamal ya ƙarasa gate ɗin sai ga Firdaus. Ƴar wajen Yaya Hajiyayye wadda su ka gama FGC tare da Hamdi.

"Anti Hamdiyya Habib Umar" ta kirata da ƙarfi cikin murna.

Tana rufe baki sauran jikokin su ka firfito suna yi mata oyoyo. Abin ya bata mamaki don gaskiya idan ta ce ta sa rai da tarba mai kyau daga zuwanta tayi ƙarya. Ƙaruwa mamakin nata ya yi da Firdaus ta rungumeta.

"Wai ashe matar Uncle Taj ce ke ban sani ba duk zamanmu a school. Ai da ko ruwa wallahi ba za ki ɗebo ba. Uncle Taj is my favourite."

Hamdi tayi murmushi kawai tana mai jin kunya. Firdaus ta ja hannunta su ka shiga ciki. Anti Zahra ta taso da sauri.

"Ke matsa min. Ƙanwata ce. Ni zan kaiwa su Hajiya ita."

"To duk gidan nan dai idan aka cire Happiness kowa ya san nice ta gaban goshin Happy. So please allow me..." wata ƙanwarsu ta janyeta "sannu da zuwa Sis"

"Meye haka jama'a? Ba babba babu yaro?" Umma tayi magana daga ƙofar ɗakinta. Kowa sai ya sami nutsuwa "Za ku barta ta zauna ne ko kuwa sai kun gama tsorata ta da wannan hayaniyar?"

Sai a lokacin wata mai yawan murmushi ta zaunar da Hamdi akan kujera. Sai dai tana zaman ta zame jikinta ta koma ƙasa. Akayi akayi sam taƙi komawa kujerar. Ga mayafi ta sa ta rufe fiye da rabin fuskarta. A haka ta gaishesu. Umma da su Hajiya su ka fito su ma. Cike da kunya da ladabi ta gaishesu tamkar iyayenta. Aka tambayeta mutanen gida ta ce suna gaishesu. Bakin Inna kasa rufuwa yayi. Surukar tata tayi mata ta ko ina. Fargabarta ma ta ganin wata halayya da za ta nuna nakasun tarbiyya a tattare da zuri'ar Abba Habibu ta ɓace ɓat.

Filin gabatarwa aka shiga inda Bishir ya nuna mata iyayensu da sunayensu. Sannan yabi ƴan uwansa ɗaya bayan ɗaya su ma. Haddacewar dai sai a hankali. A wajen ya nuna mata mata goma sha biyar. Sauran sun yi nisa. Ga jikoki gari guda. Su kaɗai sun ishi juna gayya.

"Za a saka ki a family group. A hankali duk za ki gane mu." Yaya Kubra ta faɗi.

Tana cikin waɗanda Hamdi ta riƙe sunansu saboda kana kallonta kaga ƴar gayu ajin ƙarshe. Gashi ance likita ce. Ta lura dai duka gidan akwai wata kamanceceniya da ko baka san su ba za ka iya danganta su da juna.

Kai ta gyaɗa har lokacin ta kasa buɗe fuskarta da kyau. Hira ce ta ɓarke kowa da irin tambayar da yake yi mata.

"A kawo abinci kafin ku cika mata kunne don Allah."

"Hajiya ai so muke ta buɗe bakinta."

"Baki zai buɗe ne babu abinci?" Mama ta fatattaki jikokin ta ce su tashi su fara ɗauko kwanuka.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now