14

1.3K 167 41
                                    

RAYUWA DA GIƁI  14


Batul Mamman💖




***

Rashin wuta da ake fama dashi ya hana Hamdi sayen naman yin meatpie da ake sayarwa a shagon Abba kullum. Har ta haƙura da cinikin ranar saboda da ta saya a daren ko ta soya zafin da ake zai iya canja mata ɗanɗanonsa idan ta haɗa. Sai Abban ya kira ya ce ko da yamma ne idan tayi Halifa ya kawo saboda ana so. Sai aka yi rashin sa'a Haiifan bai dawo daga makaranta da wuri ba. Ita kuma tana tsoron yin kwantai.

"Yaya zan kai masa da kaina."

Izinin tafiyar tayi mata sannan tayi mata kwatance yadda za ta gane.  s
Sau ɗaya ta taɓa zuwa tun dawowarta. Adaidata ta samu har can. Shagon a bakin titi yake a gefen wata plaza. Tana sauka ta matsar da kayanta gefe sosai ta kira Abba kamar yadda Yaya ta ce tayi idan ta iso. Kira huɗu, wayar tana ta ringing babu amsa. Gashi taƙi jinin a dinga kallonta. Madaidaiciyar cooler ɗin da ta sako meatpie ɗin mai hannu biyu ta kinkima ta ƙarasa.

Wurin a cike yake Masha Allah. Mutane suna ta kai kawo ana ta sayen abinci. A bakin ƙofa ta kuma tsayawa ta kira Abba. Wayar ko shiga bata yi ba wani ya fito ya ganta.

"Ahhh, wannan dai duk yadda aka yi ɗiyarmu ce don ga kama nan. Ƴan mata shigo daga ciki. Aunty Simagade yau ana ta fama da baƙi."

Gaban Hamdi ya yanke ya faɗi. Da ganin mutumin Abba zai girme shi. Duk da dai bleaching ya caɓalɓala masa fuska fiye da ta Abban. Ya wani sha jallabiya da ɗaurin ƙirji. Kansa kuma ya yi ɗaurin ture ka ga tsiya da ɗankwali irin zanin.

'Me ya kawo ɗan daudu wajen nan?' Ta yi wa kanta tambayar cikin yanayin ƙuncin rai.

Ashe kallo yana ciki. Tana sanya ƙafafunta wani irin baƙinciki ya turnuƙeta. Akwai kwastomomi da yawa a ciki. Amma fa a yau dandazon ƴan daudu sama da huɗu ne su ke ta karakaina wajen ɗaukar odarsu da kawo musu abinci. Muryoyinsu da taƙi jini sun cika ko ina. Sai shewa ake ana yiwa juna shaƙiyanci. Ita kuwa waige ta kama yi tana son hango mahaifinta.

*

Ubangidan Abba a birnin Jedda lokacin da yake ganiyar daudancinsa ne ya zo Kano. Ƴar Ficika ake kiransa saboda ƙanƙanta da ƙwarewa a iya shege. Duk wani mai ji da hayaƙinsa idan ya gamu da Ƴar Ficika a Saudiyya dai sai ya sauke kai. Clicks da connections na fitina babu irin wanda baya haɗawa. A lokacin da suke tare da Abba ya so ƙwarai ya sanya shi a hanyar da kowa yake bi ya yi kuɗi. Sai ya fahimci Habibu ba komai ne a gabansa ba illa girki. Shi dai a tura shi gaban murhu ya haɗa abinci. Ƙaryar mutum ya ce ya taɓa ganinsa a wani waje sama da wurin girki ko cin abinci. Ƴar Ficika sai ya tsaya masa. Ko a bayan idonsa wani ya nemi yiwa Abba wayo ya sanya shi a gurguwar turba sai ya ci mutumcin mutum. Lokacin da Baba ma yaje wurinsa, da Abba zai dawo Ƴar Ficika ne ya biya masa rabin kuɗin jirgi.

Bayan dawowarsa gida babu abin da ya sake haɗa shi da kowa cikinsu. Ya tattare wannan shafin rayuwar tasa ya watsa a shara. Yaran da suke aiki a ƙarƙashinsa kaf babu ɗan daudu. Maza ne kawai masu ra'ayin girki a dalilin rashin wata sana'ar. To yau kwana uku kenan da Ƴar Ficika ya nemo Abba. A kamen takari aka watso su gida shi da wasu yaransa. Gashi girma ya kama shi amma zuciyar nema bata mutu ba. A nan gida Najeriya kuma bashi da ido da ƙafa kamar Saudiyya. Yana neman abin yi ne ya haɗu da wanda ya san inda Abba Habibu yake. Shi ne aka kawo shi har gidan abincinsa.

Abba bai ɓoye masa sabuwar rayuwar da yake yi ba. Ƴar Ficika yaji ya kwaɗaitu da samun darajar da ya rasa a wajen danginsa. Shi da yaransa babu wanda baya fuskantar ƙyama daga ahalinsa. Godiya ya yiwa Abba ya ce kuma zai buɗe gidan abinci. Yana fata zai taimaka masa.

"Ɗan halak baya manta alkhairi. In sha Allahu zan maka iya ƙoƙarina."

"Idan babu damuwa zan so ganin yadda salon kasuwar take a nan. In zai yiwu ma kawai lokacin tafiyarka sabon restoran ɗin sai na karɓi wurin nan."

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now